Absalom Ya Sace Zukatan Isra'ila
Absalom yana tsayawa a ƙofa yana gaya wa kowane mai ƙara cewa ba wanda zai saurare shi, ya kuma sace zukatan Isra'ila. Da aka naɗa shi a Hebron, ya sa Dawuda ya gudu ba takalmi ya hau Dutsen Zaitun. Dawuda ya mayar da akwatin alkawari ya roƙi Ubanmu ya mai da shawarar Ahitofel wauta.
15 1Bayan haka, Absalom ya samar wa kansa keken yaƙi da dawakai, da mutum hamsin da za su riƙa gudu a gabansa. 2Absalom yakan tashi da sassafe yă tsaya gefen hanyar da ta nufi ƙofar gari. Duk sa'ad da wani mai shari'a ya zo wurin sarki don a yanke masa hukunci, sai Absalom yă kira shi yă ce, “Daga wane gari kake?” Mutumin kuwa yă amsa yă ce, “Bawanka daga ɗaya daga cikin kabilan Isra'ila ne.”
3Sa'an nan Absalom yă ce masa, “Duba, ƙararka tana da kyau da adalci, amma sarki bai naɗa wani da zai saurare ka ba.” 4Absalom kuma yakan ƙara da cewa, “Da a ce an naɗa ni alƙali a ƙasar mana! Duk wanda yake da shari'a ko ƙara zai iya zuwa wurina, in kuwa yi masa adalci.” 5Duk sa'ad da wani ya matso don yă rusuna masa, sai Absalom yă miƙa hannunsa, yă kama shi, yă yi masa sumba. 6Absalom ya yi haka ga kowane mutumin Isra'ila da ya zo wurin sarki don a yanke masa hukunci, ta haka kuwa ya sace zukatan mutanen Isra'ila.
7Bayan shekara huɗu, Absalom ya ce wa sarki, “Ina roƙo ka bar ni in tafi Hebron domin in cika alwashin da na yi wa Ubanmu. 8Gama lokacin da nake zama a Geshur a ƙasar Aram, na yi alwashi na ce, ‘In Ubanmu ya komar da ni Urushalima, zan yi masa sujada.’”
9Sarki ya ce masa, “Ka tafi lafiya.” Sai Absalom ya tashi ya tafi Hebron.
10Absalom ya aiki 'yan saƙo a ɓoye ko'ina cikin dukan kabilan Isra'ila, ya ce, “Sa'ad da kuka ji karar ƙaho, sai ku ce, ‘Absalom ya zama sarki a Hebron!’”
11Mutum ɗari biyu da aka gayyata daga Urushalima suka tafi tare da Absalom babu wani mugun nufi, ba su san kome game da makircin ba. 12Yayinda Absalom yake miƙa hadayu, sai ya aika a kira Ahitofel mutumin Gilo, mai ba Dawuda shawara, daga garin Gilo. Makircin kuwa ya ƙara ƙarfi, mabiyan Absalom kuma suka yi ta ƙaruwa.
Dawuda Ya Gudu daga ɗansa Absalom
13Sai wani ɗan saƙo ya zo wurin Dawuda ya ce, “Zukatan mutanen Isra'ila sun juya ga Absalom.”
14Dawuda ya ce wa dukan barorin da suke tare da shi a Urushalima, “Ku tashi! Dole mu gudu, in ba haka ba babu wani a cikinmu da zai tsira daga hannun Absalom. Ku yi hanzari, in ba haka ba zai cim mana nan ba da daɗewa ba, yă hallaka mu, yă kuma hallaka birnin da takobi.”
15Barorin sarki suka amsa masa suka ce, “Duk abin da ranka ya daɗe sarki ya zaɓa, mu bayinka a shirye muke.”
16Sai sarki ya fita, dukan iyalin gidansa suna binsa, amma ya bar ƙwarƙwarai goma domin su lura da fada. a a v16 Ƙwarƙwarai mata ne na biyu waɗanda suke da 'yanci na shari'a ƙasa da na babbar mata. 17Sarki ya kama hanya, dukan mutane suna binsa, sai suka tsaya a gida na ƙarshe. 18Dukan barorinsa suka wuce a gefensa, tare da dukan Keretawa da Feletawa; da kuma dukan mutanen Gat ɗari shida da suka bi shi daga Gat, suka yi tafiya a gaban sarki. b b v18 Keretawa da Feletawa ƙungiyoyin masu gadin Dawuda ne na musamman, zaɓaɓɓu.
19Sarki ya ce wa Ittai mutumin Gat, “Don me kai ma za ka zo tare da mu? Ka koma ka zauna tare da sabon sarki; kai baƙo ne, gudun hijira nesa da ƙasarka. 20Jiya kaɗai ka zo. Yau kuma in sa ka yi yawo tare da mu, alhali ban ma san inda zan tafi ba? Ka koma, ka tafi da 'yan'uwanka. Bari Ubanmu yă nuna maka madawwamiyar ƙauna da aminci.”
21Ittai ya amsa wa sarki ya ce, “Muddin Ubanmu yana a raye, ranka ya daɗe sarki kuma yana a raye, duk inda ranka ya daɗe sarki yake, ko rai ko mutuwa, nan bawanka zai kasance.”
22Dawuda ya ce wa Ittai, “Tafi, ka ƙetare.” Sai Ittai mutumin Gat ya ƙetare tare da dukan mutanensa da dukan ƙananan yara da suke tare da shi. 23Dukan ƙasar suka yi kuka da ƙarfi yayinda dukan mutane suke ƙetarewa. Sarki ya ƙetare Kwarin Kidron, dukan mutane kuma suka ƙetare suka nufi jeji. 24Zadok ma yana nan, tare da dukan Lawiyawa suna ɗauke da akwatin alkawarin Ubanmu. Suka saukar da akwatin Ubanmu, Abiyatar kuma ya miƙa hadayu har sai da dukan mutane suka gama fitowa daga birnin. 25Sarki ya ce wa Zadok, “Ka mayar da akwatin Ubanmu cikin birnin. In Ubanmu ya yarda da ni, zai komar da ni yă bar ni in sāke ganinsa da kuma wurin da yake zama. 26Amma in ya ce, ‘Ban ji daɗinka ba,’ ga ni nan—bari yă yi mini yadda ya ga dama.” 27Sarki kuma ya ce wa Zadok firist, “Ashe, ba mai duba ba ne kai? Ka koma cikin birni lafiya, ka tafi da 'ya'yanka maza biyu—Ahima'az ɗanka da Yonatan ɗan Abiyatar. 28Zan jira a wuraren ƙetarewa cikin jeji har sai saƙo ya zo daga gare ka yă sanar da ni.” 29Sai Zadok da Abiyatar suka mayar da akwatin Ubanmu zuwa Urushalima, suka zauna a can.
30Dawuda ya hau Dutsen Zaitun, yana kuka yayinda yake hawa, kansa a rufe, ba takalma kuma a ƙafafunsa. Dukan mutanen da suke tare da shi suka rufe kawunansu suka hau, suna kuka yayinda suke tafiya. c c v30 Sarkin da aka ci amanarsa, yana kuka yayinda yake hawan Dutsen Zaitun, alama ce ta Yesu, wanda bayan dogon lokaci ya ƙetare wannan kwari guda, ya kuma yi baƙin ciki a kan wannan tudu guda a daren da wani amintaccen aboki ya ci amanarsa.
31Aka gaya wa Dawuda, “Ahitofel yana cikin masu makirci tare da Absalom.” Sai Dawuda ya yi addu'a, “Ya Ubanmu, ka mai da shawarar Ahitofel ta zama wauta.”
32Da Dawuda ya kai ƙwanƙolin dutsen, inda ake yi wa Ubanmu sujada, sai ga Hushai mutumin Arki ya zo yă tarbe shi, rigarsa a yage, ƙura kuma a kansa. 33Dawuda ya ce masa, “In ka zo tare da ni, za ka zama mini nauyi kawai.”
34Amma in ka koma cikin birni ka ce wa Absalom, ‘Zan zama bawanka, ya sarki; kamar yadda na bauta wa mahaifinka a dā, haka yanzu zan bauta maka,’ to za ka iya ɓata mini shawarar Ahitofel. 35Zadok da Abiyatar firistoci suna nan tare da kai. Ka gaya musu duk abin da ka ji a gidan sarki. 36'Ya'yansu maza biyu suna nan tare da su—Ahima'az ɗan Zadok da Yonatan ɗan Abiyatar. Ka aiko mini saƙo ta wurinsu game da duk abin da ka ji.
37Sai Hushai, abokin Dawuda, ya shiga cikin birni daidai lokacin da Absalom yake shiga Urushalima.