Yanzu a bugun takarda

Karin Magana 23 FHB Father's Heart Bible™

UbaYesuRuhu
Rangwamen 15% a odarku ta farko →
Littafi

Ɗana, Ka Ba Ni Zuciyarka

Ladabin cin abinci da wani abu mafi tsanani a ƙarƙashinsa. Ka kiyaye kanka a gaban abinci mai daɗi na mai mulki, kada kuma ka gajiyar da kanka kana bin dukiya wadda take tsiro fikafikai ta tashi. Ya ƙare da hoton mashayi, an buge shi bai ji ba, yana farkawa sai don neman wani abin sha.

Babi na 23.

Sa'ad da ka zauna ka ci abinci tare da mai mulki, ka lura sosai da abin da yake gabanka, ka kuma sa wuƙa a maƙogwaronka in kai mai haɗama ne. Kada ka yi kwaɗayin kyawawan abincinsa, gama abinci ne mai ruɗi.

Kada ka gajiyar da kanka don neman arziki; ka kasance da hikimar ƙame kanka. Da zarar ka kalli dukiya, sai ta ɓace, gama farat ɗaya takan fid da fikafikai ta tashi sama kamar gaggafa.

Kada ka ci abincin mai rowa, kada kuma ka yi kwaɗayin kyawawan abincinsa, gama irin mutumin da yake ta ƙididdigar kuɗi ne. Yana ce maka, “Ka ci, ka sha!” amma zuciyarsa ba ta tare da kai ba. Za ka yi amai da ɗan abin da ka ci, ka kuma ɓata kalmominka masu daɗi a banza.

Kada ka yi magana a kunnen wawa, gama zai rena hikimar maganarka.

Kada ka matsar da dutsen iyaka na dā, kada kuma ka yi ƙwace a gonakin marayu, gama Mai Fansarsu mai ƙarfi ne; Ubanmu zai ɗauki ƙararsu a kanka. a a v11 Sa'ad da wani ya yi wa maraya wanda ba shi da mai kāre shi laifi, Ubanmu da kansa yakan zama mai kāre shi, yă ɗauki ƙararsa kamar tasa.

Ka sa zuciyarka ga koyarwa, ka kuma kasa kunne ga kalmomin sani.

Kada ka hana wa yaro horo; in ka doke shi da sanda, ba zai mutu ba. Ka doke shi da sanda, za ka kuwa ceci ransa daga kabari.

Ɗana, in zuciyarka tana da hikima, zuciyata ma za ta yi murna. Zuciyata ta ciki za ta yi farin ciki sa'ad da leɓunanka suka faɗi abin da yake daidai.

Kada ka bar zuciyarka ta yi hassadar masu zunubi, amma ka ci gaba da tsoron Ubanmu dukan yini. Lalle akwai sa'ar gaba, begenka kuma ba za a yanke shi ba.

Ka saurara, ɗana, ka kuma zama mai hikima, ka kuma kiyaye zuciyarka a kan hanya madaidaiciya. Kada ka kasance cikin mashaya ruwan inabi, ko masu cin nama fiye da kima, gama mashayi da mai haɗamar ci za su koma talauci, gyangyaɗi kuma zai yafa musu tsummoki.

Ka saurari mahaifinka, wanda ya ba ka rai, kada kuma ka rena mahaifiyarka sa'ad da ta tsufa. Ka sayi gaskiya kada kuma ka sayar da ita; ka sayi hikima, da koyarwa, da ganewa. Mahaifin yaro mai adalci zai yi matuƙar murna; duk wanda ya haifi ɗa mai hikima zai ji daɗinsa. Bari mahaifinka da mahaifiyarka su yi murna; bari wadda ta haife ka ta yi farin ciki.

Ɗana, ka ba ni zuciyarka, bari kuma idanunka su ji daɗin hanyoyina. Gama karuwa rami ne mai zurfi, mazinaciya kuma kunkuntar rijiya ce. Takan kwanta tana fako kamar ɓarawo, ta kuma jawo maza da yawa ga rashin aminci.

Wa yake cikin azaba? Wa yake cikin baƙin ciki? Wa yake cikin faɗa? Wa yake cikin gunaguni? Wa yake da raunuka ba dalili? Wa yake da jajayen idanu? Waɗanda suke daɗe a kan ruwan inabi, waɗanda suke zuwa don ɗanɗanar kwanonin ruwan inabi gauraye. Kada ka zura wa ruwan inabi ido sa'ad da yake ja, sa'ad da yake ƙyalƙyali a cikin kwaf yana kuma gangarawa sumul. A ƙarshe yakan sare kamar maciji, ya kuma harbi kamar gamsheƙa. Idanunka za su ga abubuwa baƙon abu, zuciyarka kuma za ta furta karkatattun abubuwa. Za ka zama kamar wanda yake kwance a tsakiyar teku, kamar wanda yake kwance a kan turken jirgin ruwa. “Sun buge ni, amma ban ji zafi ba; sun doke ni, amma ban sani ba. Yaushe ne zan farka? Zan sāke neman abin sha.”