Shaida Gabagaɗi a Ikoniyum
A Listira wani gurgu ya yi tsalle ya tashi, taron kuwa suka ce Barnaba da Bulus su ne Zafsa da Hamisa da suka sauko. Suka kece tufafinsu suka nuna wa mutane Uba mai rai maimakon haka. Bayan 'yan kwanaki, wannan taro ya jejjefi Bulus da duwatsu ya bar shi a zaton ya mutu. Ya tashi ya ci gaba da tafiya.
14 1A Ikoniyum suka shiga majami'ar Yahudawa tare, suka yi magana har Yahudawa da Hellenawa masu yawa suka gaskata. 2Amma Yahudawan da suka ƙi gaskatawa suka zuga Al'ummai suka kuma ɓata musu zukata gāba da 'yan'uwa. 3Suka daɗe a can, suna magana gabagaɗi saboda Ubangiji, wanda ya tabbatar da saƙon alherinsa, yana yin alamu da al'ajabai ta hannuwansu. 4Amma birnin ya rabu kashi biyu: waɗansu suka goyi bayan Yahudawa, waɗansu kuma suka goyi bayan manzanni. 5Sa'ad da Al'ummai da Yahudawa, tare da shugabanninsu, suka yunƙura su wulaƙanta su kuma jajjefe su da duwatsu, 6da suka gane haka, sai suka gudu zuwa biranen Likawoniya, Listira da Darbe, da kuma yankunan da suke kewaye, 7A can kuwa suka ci gaba da yin wa'azin bishara.
Uba Ya Warkar a Listira
8A Listira kuwa wani mutum yana zaune, ƙafafunsa sun naƙasa, gurgu tun haihuwa, wanda bai taɓa tafiya ba. 9Yana sauraron Bulus yana magana. Bulus ya zura masa ido, ya ga yana da bangaskiyar da za a warkar da shi, 10sai ya ce da babbar murya, “Ka miƙe tsaye a kan ƙafafunka.” Sai mutumin ya yi tsalle ya tashi, ya fara tafiya. 11Da taron suka ga abin da Bulus ya yi, sai suka ɗaga murya a harshen Likawoniya suka ce, “Alloli sun sauko mana da siffar mutane!” 12Suka kira Barnaba Zafsa, suka kuma kira Bulus Harmisa, domin shi ne babban mai magana. 13Firist na Zafsa, wanda haikalinsa yake a gaban birnin, ya kawo bijimai da kambun furanni zuwa ƙofofin birni, yana so yă yi hadaya tare da taron.
14Amma da manzanni Barnaba da Bulus suka ji haka, sai suka yage tufafinsu, suka ruga cikin taron, suna ihu, 15suna cewa, “Ya mutane, don me kuke yin haka? Mu ma mutane ne kamarku, da irin halin da kuke da shi. Muna kawo muku bishara: ku juyo daga waɗannan abubuwa banza zuwa ga Uba mai rai, wanda ya yi sama, da ƙasa, da teku, da kome da yake cikinsu. 16A zamanan baya ya bar dukan al'ummai su bi tafarkunsu, 17duk da haka bai bar kansa babu shaida ba: yana yin alheri, yana ba ku ruwan sama daga sama da lokutan amfani, yana cika zukatanku da abinci da farin ciki.”
18Ko da waɗannan kalmomi ma, da ƙyar suka hana taron yin musu hadaya. 19Amma waɗansu Yahudawa daga Antakiya da Ikoniyum suka zo, suka rinjayi taron, suka jajjefi Bulus da duwatsu, suka kuma jã shi zuwa bayan birni, suna tsammani ya mutu. 20Da almajirai suka kewaye shi, sai ya tashi ya shiga birnin. Kashegari ya tafi Darbe tare da Barnaba.
Ƙarfafa Almajirai
21Bayan sun yi wa'azin bishara a wannan birni, suka kuma mai da mutane da yawa almajirai, sai suka koma Listira, da Ikoniyum, da Antakiya, 22suna ƙarfafa rayukan almajirai, suna gargaɗinsu su tsaya cikin bangaskiya: dole ne mu shiga Mulkin Ubanmu ta wahaloli masu yawa. 23Bayan sun naɗa musu dattawa a kowace ikkilisiya, suka yi addu'a tare da azumi, sai suka miƙa su ga Ubangiji wanda suka gaskata da shi.
24Sa'an nan suka ratsa Bisidiya suka zo Bamfiliya. 25Da suka yi magana a Berga, sai suka gangara zuwa Attaliya, 26daga can suka shiga jirgin ruwa zuwa Antakiya, inda aka miƙa su ga alherin Ubanmu domin aikin da suka gama. 27Da suka iso, sai suka tara ikkilisiya, suka ba da labarin dukan abin da Ubanmu ya yi tare da su, da yadda ya buɗe wa Al'ummai ƙofar bangaskiya. 28Suka kuwa daɗe a can tare da almajirai.