Abin da Mai Haƙar Ma'adinai Ba Ya Iya Tonowa
Masu haƙar ma'adinai sukan haƙa rami cikin dutse don azurfa da saffir, suna zuwa inda shaho bai taɓa gani ba. Amma hikima ba a haƙo ta ko a saye ta; zurfi da teku sun ce ba ta nan. Allah kaɗai ya san wurinta, ya kuwa faɗa wa 'yan adam: ku ji tsoron Allah, ku rabu da mugunta.
28 1“Hakika akwai ramin haƙar azurfa, akwai kuma wurin da ake tace zinariya. 2Ana ɗebo baƙin ƙarfe daga ƙasa, ana kuma narkar da tagulla daga dutse. 3Mutum yakan sa iyaka ga duhu; yakan nema har iyakar ƙarshe domin ma'adinai cikin duffai da inuwa mai yawa. 4Yakan haƙa rami nesa da wurin da mutane suke zama, a wuraren da ƙafa ba ta taɓa taƙawa ba; a can suke rataye suna lilo, nesa da kowa. 5Ƙasa—daga gare ta ake samun abinci, duk da haka a ƙarƙashinta an juya ta kamar da wuta. 6Duwatsunta suna ɗauke da saffaya, ƙurarta kuma tana ɗauke da zinariya. 7Hanya ce da babu tsuntsu mai farauta da ya sani, wadda idon shaho bai taɓa gani ba. 8Namun daji masu girman kai ba su taƙa ta ba, zaki kuma bai yi yawo a kanta ba. 9Mutum yakan sa hannunsa a kan dutse mai wuya, yakan kuma tumɓuke duwatsu daga saiwoyinsu. 10Yakan yanka magudanai cikin duwatsu, idonsa kuma yakan ga kowane abu mai daraja. 11Yakan hana ɗigon ruwan rafuffuka, yakan kuma fito da abubuwan da suke ɓoye zuwa haske.
12“Amma hikima—ina za a same ta? Ina kuma wurin fahimta yake? 13Mutum bai san darajarta ba, ba a kuma same ta a ƙasar masu rai ba. 14Zurfi ya ce, ‘Ba ta cikina ba,’ teku kuma ya ce, ‘Ba ta tare da ni ba.’ 15Ba za a iya sayenta da zinariya mafi kyau ba, ba kuwa za a iya auna kuɗinta da azurfa ba. 16Ba za a iya ƙididdige darajarta da zinariyar Ofir ba, ko da onis mai daraja ko saffaya. 17Zinariya da kristal ba za su kai ta ba, ba kuwa za a iya musaya ta da kayan zinariya zalla ba. 18Murjani da kristal ba su cancanci a ambata ba; darajar hikima ta fi ta yaƙutu. 19Tufaz na Kush ba zai kai ta ba, ba kuwa za a iya ƙididdige darajarta da zinariya zalla ba.
20“To, daga ina hikima take zuwa? Ina kuma wurin fahimta yake? 21An ɓoye ta daga idanun dukan masu rai, an kuma rufe ta har daga tsuntsayen sama. 22Hallaka da Mutuwa suna cewa, ‘Da kunnuwanmu mun ji jita-jitarta.’
23“Allah ya fahimci hanya zuwa gare ta, ya kuma san wurinta. 24Gama yakan dubi iyakokin duniya yakan kuma ga kome a ƙarƙashin sammai. 25Sa'ad da ya ba iska nauyinta ya kuma auna ruwaye, 26sa'ad da ya kafa doka domin ruwan sama da kuma hanya domin walƙiya, 27sai ya ga hikima ya kuma bayyana ta; ya kafa ta ya kuma bincike ta.
28Ya kuma ce wa 'yan adam, ‘Tsoron Allah—shi ne hikima, juyewa daga mugunta kuwa shi ne fahimta.’”