Yanzu a bugun takarda

Ayuba 29 FHB Father's Heart Bible™

UbaYesuRuhu
Rangwamen 15% a odarku ta farko →
Littafi

Ayuba Ya Sāke Magana

Ayuba ya tuna da abin da ya rasa: 'ya'yansa kewaye da shi, abokantakar Allah bisa alfarwarsa, girmamawar birni gaba ɗaya. Ya zama idanu ga makafi, uba kuma ga mabukata, yana kuma tsammanin zai mutu da tsufa cikin sheƙarsa, darajarsa sabuwa.

Babi na 29.

Ayuba ya sāke magana ya ce, “Kash, da a ce ina kamar yadda nake a watannin da suka wuce, kamar kwanakin da Allah yake lura da ni, sa'ad da fitilarsa take haskakawa bisa kaina, na kuma yi tafiya cikin duhu ta wurin haskensa; kamar yadda nake a kwanakin ƙarfina, sa'ad da zumuncin Allah na kud da kud ya kasance bisa tentina, a a v4 Ayuba yana marmarin kusancin da ya taɓa sani — zumuncin Allah na kud da kud bisa gidansa. Bai riga ya sani ba cewa Allah da yake marmarinsa shi ne Uba wanda zuciyarsa ba ta taɓa rabuwa da shi ba; cewa zai gani da kansa kafin littafin yă ƙare. sa'ad da Maɗaukaki yake tare da ni har yanzu, sa'ad da 'ya'yana suke kewaye da ni; sa'ad da ake wanke sawuna da madara, dutse kuma yakan zubo mini rafukan mai. Sa'ad da nake fita zuwa ƙofar birni, na kuma ɗauki wurin zamana a dandalin jama'a, samari sukan gan ni su kauce, dattawa kuma sukan tashi tsaye; sarakuna sukan daina magana, su kuma sa hannu a bakunansu; muryar manya ta yi shiru, harsunansu kuma suka manne a samfar bakunansu. Sa'ad da kunne ya ji, sai ya kira ni mai albarka, sa'ad da ido ya gani kuma, sai ya ba da shaida domina, gama na ceci matalauci da ya yi kuka don taimako, da maraya wanda ba shi da mai taimako. Albarkar wanda yake bakin halaka ta sauko mini, na kuma sa zuciyar gwauruwa ta rera waƙa domin farin ciki. Na yafa adalci kamar riga, shi kuma ya suturta ni; adalcina ya zama kamar taguwa da rawani. Na zama idanu ga makaho, ƙafafu kuma ga guragu. Na zama uba ga masu bukata, na kuma binciki ƙarar wanda ban sani ba. Na karya haƙoran mugu, na ƙwace ganima daga haƙoransa. Saboda haka na yi tunani, ‘Zan mutu a cikin sheƙata, in riɓanya kwanakina kamar yashi.’ Saiwoyina sun kai ga ruwaye, raɓa kuma ta kwana a kan rassana. Ɗaukakata ta kasance sabuwa a cikina, bakana kuma kullum sabo ne a hannuna. Mutane sukan saurare ni su jira; sukan yi shiru domin shawarata. Bayan na yi magana, ba sa ƙara cewa kome; maganata takan zuba a kansu a hankali. Sukan jira ni kamar yadda ake jiran ruwan sama, su buɗe bakunansu kamar yadda ake jiran ruwan bazara. Sa'ad da na yi musu murmushi, da ƙyar su gaskata hakan, sukan kuma riƙe hasken fuskata. Na zaɓi hanyarsu, na zauna a matsayin shugabansu; na yi zama kamar sarki a cikin rundunarsa, kamar mai ta'aziyya ga masu makoki.”