Yanzu a bugun takarda

Ayuba 27 FHB Father's Heart Bible™

UbaYesuRuhu
Rangwamen 15% a odarku ta farko →
Littafi

Ayuba Ya Sāke Ɗaga Muryarsa

Yana rantsuwa da Allah wanda ya ɗauke masa adalcinsa, Ayuba ya ƙi yarda cewa abokansa suna da gaskiya; zai riƙe mutuncinsa har mutuwa. Sa'an nan shi da kansa ya kwatanta rabon mugun mutum: tarin azurfa da adalai za su sa, guguwa da dare, gida na yanar gizo.

Babi na 27.

Ayuba ya sāke ɗaukar jawabinsa ya ce, “Na rantse da Allah mai rai, wanda ya hana mini adalci, da kuma Maɗaukaki, wanda ya sa raina ya ɗaci, muddin numfashina yana cikina, Ruhun Ubanmu kuma yana cikin hancina, leɓunana ba za su faɗi ƙarya ba, harshena kuma ba zai yi magana ta ruɗu ba. Ba zan taɓa yarda cewa kuna da gaskiya ba; har in mutu ba zan watsar da mutuncina ba. Na riƙe adalcina ƙam, ba kuwa zan saki shi ba; zuciyata ba ta zargina a kan ko ɗaya daga cikin kwanakina.

“Bari abokin gābana yă zama kamar mugu, wanda kuma yake tasowa gāba da ni yă zama kamar marar adalci. Gama wane bege ne marar tsoron Allah yake da shi sa'ad da aka datse shi, sa'ad da Allah ya ƙwace ransa? Allah zai ji kukansa sa'ad da wahala ta auko masa? Zai ji daɗi a cikin Maɗaukaki? Zai yi kira ga Allah a kowane lokaci? Zan koya muku game da hannun Allah; ba zan ɓoye abin da yake wurin Maɗaukaki ba. Ga shi, dukanku kun ga wannan da idanunku; to don me fa kuke faɗin irin wannan maganar banza? Wannan ne rabon mugun mutum daga Allah, gādon da masu zalunci suke samu daga Maɗaukaki: In 'ya'yansa sun yi yawa, za su mutu ta takobi, zuriyarsa kuma ba za su sami isashen abinci ba. Waɗanda suka tsira daga gare shi, annoba za ta binne su, gwaurayensu kuma ba za su yi kuka ba. Ko da ya tara azurfa kamar ƙura ya kuma tara tufafi kamar laka, zai iya tara shi, amma mai adalci zai sa shi, marar laifi kuma zai raba azurfar. Ya gina gidansa kamar gidan asu, kamar bukkar da mai gadi yake yi. Yakan kwanta mai arziki, amma ba zai ƙara yin haka ba; yă buɗe idanunsa, sai ga shi kome ya tafi. Razana sun kama shi kamar ambaliya; da dare guguwa ta kwashe shi. Iskar gabas ta ɗaga shi sai ya tafi; ta share shi daga wurinsa. Ta auko masa babu tausayi; ya sheƙa a guje daga ikonta. Ta tafa masa hannuwanta ta kuma yi masa tsaki ya rabu da wurinsa.”