Dawuda Ya Yi Ƙidayar Mutane
Dawuda ya ƙidaya mayaƙansa, daga baya kuma zuciyarsa ta buge shi. Da aka ba shi zaɓin hukunci uku, ya zaɓi ya faɗa a hannun Ubanmu maimakon na mutum, domin jinƙansa da yawa yake. Annobar ta tsaya a masussukar Arauna, wadda Dawuda ya nace sai ya saye ta maimakon ya karɓe ta kyauta.
24 1Har wa yau fushin Ubanmu ya sāke ƙuna a kan Isra'ila, sai ya zuga Dawuda a kansu, yana cewa, “Ka tafi, ka yi ƙidayar Isra'ila da Yahuda.”
2Sai sarki ya ce wa Yowab, shugaban mayaƙan da yake tare da shi, “Ka zaga dukan kabilan Isra'ila yanzu, daga Dan har zuwa Beyersheba, ka ƙidaya mutane, domin in san yawan mutanen.”
3Amma Yowab ya ce wa sarki, “Bari Ubanka yă ƙara wa mutane har sau ɗari bisa yawansu, idanun ranka yă daɗe sarki kuma su gan shi. Amma don me ranka yă daɗe sarki yake so yă yi wannan abu?”
4Amma umarnin sarki ya rinjayi Yowab da shugabannin mayaƙa. Sai Yowab da shugabannin mayaƙa suka tashi daga gaban sarki domin su ƙidaya mutanen Isra'ila. 5Suka haye Urdun suka yi sansani kusa da Arower, a kudu da birnin da yake tsakiyar kwari, wajen Gad har zuwa Yazer. 6Sa'an nan suka iso Gileyad da yankin Tatim-hodshi, suka kuma iso Dan-ya'an suka kewaya zuwa Sidon, 7suka iso kagarar Taya da dukan biranen Hiwiyawa da Kan'aniyawa, suka fita zuwa Negeb ta Yahuda a Beyersheba. 8Da suka zaga dukan ƙasar, sai suka iso Urushalima bayan wata tara da kwana ashirin. 9Yowab ya kawo wa sarki jimillar ƙidayar mutanen. A Isra'ila akwai jarumawa dubu ɗari takwas da suka iya zare takobi, Yahuda kuwa tana da dubu ɗari biyar.
10Amma zuciyar Dawuda ta yi masa tsiwa bayan ya ƙidaya mutane. Sai Dawuda ya ce wa Ubanmu, “Na yi zunubi ƙwarai a cikin abin da na yi. Yanzu, ya Ubana, ina roƙonka ka ɗauke laifin bawanka, gama na yi wauta ƙwarai.”
11Da Dawuda ya tashi da safe, sai maganar Ubanmu ta zo wa annabi Gad, mai duban Dawuda,
12“Ka tafi ka ce wa Dawuda, ‘Ga abin da Ubanmu yake cewa: Ina riƙe da abubuwa uku a kanka. Ka zaɓi ɗaya daga cikinsu, ni kuwa in aikata shi a kanka.’”
13Sai Gad ya zo wurin Dawuda ya gaya masa, yana tambaya, “Shekara uku na yunwa za su auko wa ƙasarka? Ko za ka gudu wata uku a gaban abokan gābanka yayin da suke korarka? Ko kuwa a yi kwana uku na annoba a ƙasarka? Yanzu ka yi tunani sosai ka tsai da shawara, wace amsa zan kai wa wanda ya aiko ni.”
14Sai Dawuda ya ce wa Gad, “Ina cikin matsananciyar wahala. Bari mu fāɗa a hannun Ubanmu, gama jinƙansa yana da girma ƙwarai; amma kada ya bari in fāɗa a hannun mutum.”
15Sai Ubanmu ya aiko da annoba a kan Isra'ila daga safe har zuwa ƙayyadadden lokaci, mutum dubu saba'in kuwa daga Dan har zuwa Beyersheba suka mutu. a a v15 “Ƙayyadadden lokaci” mai yiwuwa yana nufin ƙayyadadden sa'ar hadaya ta yamma ne.
16Amma da mala'ikan ya miƙa hannunsa wajen Urushalima domin yă hallaka ta, sai Ubanmu ya canja shawararsa game da masifar, ya ce wa mala'ikan da yake hallaka mutane, “Ya isa! Yanzu ka janye hannunka.” A lokacin mala'ikan Ubanmu yana nan kusa da masussukar Arauna mutumin Yebus.
17Da Dawuda ya ga mala'ikan da yake bugun mutane, sai ya yi magana da Ubanmu ya ce, “Ga shi, ni ne wanda ya yi zunubi; ni ne wanda ya aikata mugunta. Amma waɗannan tumaki, me suka yi? Ina roƙo, bari hannunka ya sauka a kaina da kan gidan mahaifina.”
Dawuda Ya Gina Bagade
18A ranar nan Gad ya zo wurin Dawuda ya ce masa, “Ka haura ka gina bagade ga Ubanmu a masussukar Arauna mutumin Yebus.” 19Sai Dawuda ya haura, bisa ga maganar Gad, yadda Ubanmu ya umarta. 20Da Arauna ya duba ƙasa ya ga sarki da bayinsa suna zuwa wurinsa, sai ya fito ya rusuna a gaban sarki har fuskarsa ta kai ƙasa. 21Sai Arauna ya ce, “Me ya kawo ranka yă daɗe sarki wurin bawansa?” Dawuda ya amsa ya ce, “Domin in sayi masussuka a wurinka, in gina bagade ga Ubanmu, domin a dakatar da annoba daga mutane.”
22Arauna ya ce wa Dawuda, “Bari ranka yă daɗe sarki yă ɗauka yă miƙa duk abin da ya ga dama. Ga shi, ga shanu domin hadaya ta ƙonawa, ga allunan sussuka da karkiyar shanu domin itace. 23Dukan wannan, ya sarki, Arauna yana ba wa sarki.” Arauna kuma ya ce wa sarki, “Bari Ubangiji Allahnka yă karɓe ka.”
24Amma sarki ya ce wa Arauna, “A'a, dole in saye shi a wurinka a kan kuɗi. Ba zan miƙa wa Ubana hadayu na ƙonawa waɗanda ban biya kome a kansu ba.” Sai Dawuda ya sayi masussuka da shanun a kan kimanin fam 1.2 na azurfa. 25Sai Dawuda ya gina bagade a can ga Ubanmu, ya miƙa hadayu na ƙonawa da hadayu na salama. Sai Ubanmu ya karɓi roƙo saboda ƙasar, aka kuma dakatar da annoba daga Isra'ila.