Waƙar Ƙarshe ta Dawuda
Kalmomin Dawuda na ƙarshe: Ubanmu ya yi madawwamin alkawari da gidansa, mai mulki cikin adalci kuwa kamar hasken safiya ne bayan ruwan sama. Sa'an nan jerin jarumawansa — mutum ukun nan da suka keta layin Filistiyawa domin su ɗebo ruwan Baitalami, wanda Dawuda ya zubar maimakon ya sha.
23 1To, waɗannan su ne kalmomin ƙarshe na Dawuda. Saƙon Dawuda ɗan Yesse, saƙon mutumin da aka ɗaukaka, wanda Allah na Yaƙubu, Ubanmu, ya shafe shi, ƙaunataccen mawaƙin Isra'ila: a a v1 Saƙo wata kalma ce ta annabci da aka hure; a nan Dawuda yana magana kamar wanda Ruhun Allah ya motsa. 2Ruhun Ubanmu ya yi magana ta wurina; maganarsa tana kan harshena.
3Ubanmu, Allah na Isra'ila, ya yi magana; Dutsen Isra'ila ya ce mini, “Sa'ad da mutum yake mulkin mutane da adalci, yana mulki cikin tsoron Allah,
4yana kama da hasken safiya sa'ad da rana ta fito a wayewar gari marar gizagizai, kamar haske bayan ruwan sama da yake fito da ciyawa daga ƙasa.
5Ashe, gidana ba haka yake a wurin Ubanmu ba? Gama ya yi alkawari madawwami da ni, wanda aka tsara shi a kowane abu kuma yake tabbatacce. Ashe, ba zai cika dukan cetona da dukan sha'awata ba? 6Amma dukan mutanen banza kamar ƙayayuwan da aka watsar suke, gama ba a iya ɗaukarsu da hannu ba. 7Wanda zai taɓa su yakan ɗauki ƙarfe da sandan māshi, a kuma ƙone su da wuta nan take.”
Jarumawan Dawuda
8Waɗannan su ne sunayen jarumawan Dawuda. Yosheb-basshebet Batakemoni, shugaban ukun nan, ya ɗaga māshinsa a kan mutum 800, ya kashe su gaba ɗaya. 9Na biye da shi shi ne Ele'azar ɗan Dodo Ba'ahohe, ɗaya daga cikin jarumai ukun nan da suke tare da Dawuda sa'ad da suka ƙalubalanci Filistiyawan da suka taru don yaƙi a can, mutanen Isra'ila kuwa suka ja da baya. 10Ya tashi ya kakkashe Filistiyawa har hannunsa ya gaji ya manne wa takobi. Ubanmu ya ba da babban nasara a ranar, mayaƙan kuwa suka komo bayansa don kawai su washe gawawwaki. 11Na biye da shi shi ne Shamma ɗan Age Baharare. Filistiyawa suka taru a Lehi, a cikin gona cike da waken barewa, mayaƙa kuwa suka gudu daga gabansu. 12Amma Shamma ya tsaya a tsakiyar gonar, ya kāre ta, ya kuma kashe Filistiyawa. Ubanmu kuwa ya ba da babban nasara.
13A lokacin girbi, uku daga cikin manyan mutane talatin ɗin suka gangara wurin Dawuda a kogon Adullam, yayinda ƙungiyar Filistiyawa suka yi sansani a Kwarin Refayim. 14A lokacin Dawuda yana cikin kagara, rundunar Filistiyawa kuwa tana a Baitlahami. 15Dawuda ya yi marmarin ruwa ya ce, “Kash, da a ce wani zai ba ni ruwan sha daga rijiyar da take kusa da ƙofar Baitlahami!”
16Sai jarumai ukun nan suka ratsa sansanin Filistiyawa, suka debo ruwa daga rijiyar Baitlahami da take kusa da ƙofa, suka kawo wa Dawuda. Amma ya ƙi shan shi; ya zubar da shi ga Ubanmu. 17Ya ce, “Ya Ubana, Allah kiyaye in yi wannan! Ashe, wannan ba jinin mutanen da suka yi kasada da ransu ba ne?” Saboda haka ya ƙi shan shi. Haka jarumai ukun nan suka yi.
18Abishai, ɗan'uwan Yowab, ɗan Zeruya, shi ne shugaban talatin ɗin. Ya ɗaga māshinsa a kan mutum 300, ya kashe su, ya kuma yi suna a cikin ukun nan. 19Ashe, ba shi ne ya fi kowa daraja cikin talatin ɗin ba? Ya zama shugabansu, ko da yake ba ɗaya daga cikin ukun nan ba ne.
20Benaya ɗan Yehoyada mutum ne jarumi daga Kabzeyel, mai manyan ayyuka. Ya kashe jarumawa biyu na Mowab. Ya gangara cikin rami a ranar da aka yi ƙanƙara ya kashe zaki a can. 21Ya kuma kashe wani gagarumin Bamasare. Bamasaren yana riƙe da māshi, amma Benaya ya nufe shi da sanda kaɗai, ya ƙwace māshin daga hannunsa, ya kashe shi da māshinsa. 22Waɗannan su ne ayyukan Benaya ɗan Yehoyada, wanda ya yi suna a cikin jarumai ukun nan. 23Ya fi talatin ɗin daraja, amma ba ya cikin ukun nan. Dawuda ya sa shi shugaban masu gadinsa.
24Cikin talatin ɗin akwai, Asahel ɗan'uwan Yowab; Elhanan ɗan Dodo na Baitlahami; 25Shamma Baharode; Elika Baharode; 26Helez Bafalti; Ira ɗan Ikkesh Batekowa; 27Abiyezer Ba'anatot; Mebunnai Bahushat; 28Zalmon Ba'ahohe; Maharai Banetofa; 29Heleb ɗan Ba'ana Banetofa; Ittai ɗan Ribai daga Gibeya ta Biliyaminawa; 30Benaya Bafiraton; Hiddai daga kwarurrukan Ga'ash; 31Abi-albon Ba'arbat; Azmawet Baharume; 32Eliyahba Basha'albon; 'ya'yan Yashen; Yonatan; 33Shamma Baharare; Ahiyam ɗan Sharar Baharare; 34Elifelet ɗan Ahasbai Bama'aka; Eliyam ɗan Ahitofel Bagilon; 35Hezro Bakarmel; Pa'arai Ba'arbi; 36Igal ɗan Natan na Zoba; Bani Bagad; 37Zelek Ba'ammon; Naharai Babe'erot, mai riƙe da makamin Yowab ɗan Zeruya; 38Ira Bayitra; Gareb Bayitra; 39da Uriya Bahitte—talatin da bakwai ne duka.