Waƙar Ceto ta Dawuda
Dogon waƙar Dawuda, wadda ya rera bayan kowace kuɓuta: igiyoyin mutuwa sun naɗe shi ya yi kira, Ubansa kuwa ya sauko ta cikin hayaƙi da hadari ya fitar da shi daga zurfafan ruwaye. An cece shi domin Ubansa yana jin daɗinsa, Ubansa kuma fitila ne a cikin duhunsa.
22 1Dawuda ya yi wa Ubanmu maganar wannan waƙa sa'ad da Ubanmu ya cece shi daga hannun dukan abokan gābansa da kuma daga hannun Shawulu. 2Ya ce, Ubana shi ne dutsena, kagarata, mai cetona. 3Ubana, dutsena, wanda nake neman mafaka a wurinsa, garkuwata da ƙarfin cetona, mafakata da madogarata, mai cetona—kai kake cetona daga tashin hankali. 4Ina kiran Ubana, wanda ya cancanci yabo, an kuwa cece ni daga abokan gābana. 5Gama raƙuman ruwan mutuwa sun kewaye ni; ambaliyar hallaka ta razana ni. 6Igiyoyin kabari sun daure ni; tarkunan mutuwa sun fuskance ni. 7Cikin wahalata na kira ga Ubana; na yi kuka ga Allahna don taimako. Daga haikalinsa ya ji muryata, kukata kuwa ta kai kunnuwansa. 8Sai ƙasa ta girgiza ta kuma jijjigu; harsashan sammai sun yi rawar jiki suka kuma jijjigu, domin ya yi fushi. 9Hayaƙi ya taso daga hancinsa, wuta mai cinyewa kuwa ta fito daga bakinsa; garwashin wuta mai ci ya rika fitowa daga gare shi. 10Ya buɗe sammai ya sauko, da gizagizai masu duhu a ƙarƙashin ƙafafunsa. 11Ya hau kerubi ya tashi sama; ya yi shawagi a kan fikafikan iska. 12Ya mai da duhu rumfarsa kewaye da shi—gizagizai masu duhu na sararin sama. 13Daga cikin hasken da yake gabansa garwashin wuta ya yi ci. 14Ubana ya yi tsawa daga sama; Maɗaukaki ya tā da muryarsa. 15Ya harbe kibiyoyinsa ya watsar da abokan gābansa, ya aika walƙiya ya fatattake su. 16Magudanan teku suka bayyana, an tono harsashan duniya saboda tsawatawar Ubana, saboda hararar numfashin hancinsa. 17Ya miƙo hannu daga sama ya kama ni; ya jawo ni daga zurfin ruwaye. 18Ya cece ni daga maƙiyina mai ƙarfi, daga abokan gābana waɗanda suka fi ni ƙarfi. 19Sun fuskance ni a ranar masifata, amma Ubana shi ne mai goyon bayana. 20Ya fitar da ni zuwa wuri mai faɗi; ya cece ni domin yana farin ciki da ni. 21Ubana ya yi mini gwargwadon adalcina; gwargwadon tsabtar hannuwana ya sāka mini. 22Gama na kiyaye hanyoyin Ubana; ban kuwa juya daga Allahna da mugunta ba. 23Dukan hukunce-hukuncensa suna a gabana; ban kauce wa ƙa'idojinsa ba. 24Na kasance marar aibu a gabansa, na kuma kiyaye kaina daga laifina. 25Saboda haka Ubana ya sāka mini gwargwadon adalcina, gwargwadon tsabtata a gabansa. 26Ga mai aminci kana nuna kanka mai aminci; ga marar aibu kana nuna kanka marar aibu. 27Ga mai tsabta kana nuna kanka mai tsabta, amma ga mai karkata kana nuna kanka mai wayo. 28Kana ceton mutane masu shan wahala, amma idanunka suna a kan masu girman kai, domin ka ƙasƙantar da su. 29Gama kai ne fitilata, Ya Ubana; yana mai da duhuna haske. 30Tare da kai zan iya kai wa mayaƙa hari; tare da Ubana zan iya tsalle bango. 31Game da Ubana kuwa, hanyarsa cikakkiya ce; maganar Ubana babu aibu. Shi garkuwa ne ga duk wanda yake neman mafaka a wurinsa. 32Gama wane ne Allah sai Ubanmu? Wane ne kuma dutse in ba Ubanmu ba? 33Ubana shi ne mafakata mai ƙarfi; yana sa hanyata ta zama marar aibu. 34Yana sa ƙafafuna su zama kamar ƙafafun barewa yana kuma kafa ni lafiya a kan tuddai. 35Yana koya wa hannuwana yaƙi, domin hannuwana su iya tanƙware bakan tagulla. 36Ka ba ni garkuwar cetonka, tawali'unka kuma ya mai da ni babba. 37Ka faɗaɗa hanya a ƙarƙashina, domin kada idon ƙafafuna su yi santsi. 38Na bi abokan gābana na kuma hallaka su; ban kuwa juya baya ba sai da suka ƙare. 39Na cinye su na kuma ragargaza su har ba za su iya tashi ba; suka fāɗi a ƙarƙashin ƙafafuna. 40Ka ɗamara mini ƙarfi don yaƙi; ka sa abokan gābana su rusuna a ƙarƙashina. 41Ka sa abokan gābana suka juya bayansu suka gudu, waɗanda kuma suka ƙi ni na hallaka su. 42Suka duba, amma babu wanda zai cece su—har ga Ubana ma, amma bai amsa ba. 43Na niƙe su har suka yi laushi kamar ƙurar ƙasa; na murƙushe su na tattake su kamar laka a tituna. 44Ka cece ni daga faɗace-faɗacen mutanena; ka kiyaye ni in zama shugaban al'ummai; mutanen da ban sani ba yanzu suna bauta mini. 45Baƙi suna rusuna a gabana; da jin labari kawai, sukan yi mini biyayya. 46Baƙi sun karaya; suna fitowa suna rawar jiki daga kagarorinsu. 47Ubana yana a raye! Albarka ta tabbata ga Dutsena! A ɗaukaka Ubana, Dutsen cetona! 48Ubana ne yake yi mini adalci, yake kuma ƙasƙantar da al'ummai a ƙarƙashina. 49Yana fitar da ni daga abokan gābana. Ka ɗaukaka ni bisa maƙiyana; ka cece ni daga mutum mai tashin hankali. 50Saboda haka zan yabe ka a cikin al'ummai, Ya Ubana; zan rera yabo ga sunanka. 51Yana ba sarkinsa manyan nasarori yana kuma nuna madawwamiyar ƙauna ga shafaffensa, ga Dawuda da zuriyarsa har abada.