Babu Kome Sai Almasihu Gicciyayye
Bulus da gangan ya zo ba tare da iya magana mai burgewa ba, sai dai Almasihu gicciyeyye, domin bangaskiyarsu ta dogara ga ikon Ubanmu ba ga gwanintar mai magana ba. Hikimar da yake koyarwa a ɓoye take, an shirya ta tun kafin farkon zamani, kuma ana saninta ne kawai yadda Ruhun Ubanmu ya bayyana ta.
2 1'Yan'uwa, sa'ad da na zo wurinku, ban yi muku shelar shaidar Ubanmu da kalmomi masu kayatarwa ko hikima ba. 2Gama na ƙuduri niyyar ba zan san kome a cikinku ba sai Yesu Almasihu, shi kuwa wanda aka gicciye. 3Na kuwa zo wurinku cikin rauni, da tsoro, da rawar jiki mai yawa. 4Saƙona da wa'azina ba su dogara ga kalmomin hikima masu rinjayarwa ba, sai dai ga tabbacin Ruhu Mai Tsarki da na iko, 5domin kada bangaskiyarku ta dangana ga hikimar mutane, sai dai ga ikon Ubanmu.
6Duk da haka muna faɗar hikima a cikin waɗanda suka balaga—ba hikimar wannan zamani ba, ba kuma ta masu mulkin wannan zamani ba, waɗanda suke shuɗewa. 7A'a, muna faɗar hikimar Ubanmu, asirin da yake a ɓoye, wanda Ubanmu ya ƙaddara tun kafin lokaci ya fara, domin ɗaukakarmu. 8Ba wani daga cikin masu mulkin wannan zamani da ya san ta; da sun sani, da ba su gicciye Ubangiji mai ɗaukaka ba. 9Kamar yadda yake a rubuce, “Abin da ido bai taɓa gani ba, kunne bai ji ba, zuciyar mutum kuma ba ta taɓa tunani ba—waɗannan abubuwa ne Ubanmu ya shirya wa masu ƙaunarsa.”
10Amma Ubanmu ya bayyana mana su ta wurin Ruhu; gama Ruhu yana binciken dukan abubuwa, har ma da zurfafan abubuwan Ubanmu. 11Wane ne ya san tunanin mutum sai ruhun mutumin da yake cikinsa? Haka ma, ba wanda ya san tunanin Ubanmu sai Ruhun Ubanmu. 12Ba ruhun duniya muka karɓa ba, sai dai Ruhun da yake daga wurin Ubanmu, domin mu san abubuwan da Ubanmu ya ba mu kyauta. 13Wannan ne muke faɗa, ba da kalmomin da hikimar mutane take koyarwa ba, sai dai da waɗanda Ruhu yake koyarwa, muna bayyana gaskiyar ruhaniya ga mutane masu ruhaniya. 14Mutumin da ba shi da Ruhu ba ya karɓar abin da yake zuwa daga Ruhun Ubanmu; wauta ce a gare shi, kuma ba ya iya fahimtarsa, domin sai ta wurin fahimtar ruhaniya ake iya gane shi. 15Mutum mai ruhaniya yana gane dukan abubuwa, amma shi kansa babu wanda yake yin masa hukunci. 16Gama, “Wane ne ya taɓa sanin tunanin Ubanmu, har da zai koya masa?” Amma mu, muna da tunanin Almasihu.