Madawwamiyar Ƙaunarsa Tana Dawwama Har Abada
Tarihi ɗaya ne daga ɗaya gefen, a matsayin furta zunubi. Sun manta a bakin teku, sun yi kwaɗayi a jeji, sun yi ɗan maraƙi, sun miƙa 'ya'yansu hadaya. Sau da sau Ubanmu ya bashe su, ya ji kukansu, duk da haka ya tuna da alkawarinsa.
106 1Halleluya! Ku gode wa Ubanmu, gama shi nagari ne; ƙaunarsa ta alkawari tana dawwama har abada.
2Wa zai iya ba da labarin manyan ayyukan Ubanmu, ko yă yi shelar dukan yabonsa? 3Masu albarka ne waɗanda suke kiyaye adalci, waɗanda kullum suke aikata abin da yake daidai.
4Ka tuna da ni, ya Ubanmu, da alherin da kake nunawa mutanenka; ka zo wurina da cetonka, 5domin in ga wadatar zaɓaɓɓunka, in yi murna tare da farin cikin al'ummarka, in kuma yi fahariya tare da gādonka.
6Mun yi zunubi, kamar yadda kakanninmu suka yi; mun yi laifi, mun aikata mugunta. 7Sa'ad da kakanninmu suke a Masar, ba su lura da al'ajiban nan naka ba; ba su tuna da yawan ƙaunarka ta alkawari ba, amma suka yi tawaye a bakin teku, a Jar Teku. a a v7 Ibraniyanci: Yam Suf, “Tekun Kyauro.” 8Duk da haka ya cece su saboda sunansa, domin yă sanar da ikonsa mai girma. 9Ya tsawata wa Jar Teku, sai ta kafe; ya bi da su ta cikin zurfafan ruwaye kamar ta cikin hamada. 10Ya cece su daga hannun wanda yake ƙin su, ya kuma fanshe su daga hannun abokin gāba. 11Ruwaye suka rufe maƙiyansu; babu ko ɗaya a cikinsu da ya ragu. 12Sa'an nan suka gaskata maganarsa; suka rera yabonsa.
13Amma nan da nan suka manta da ayyukansa; ba su jira shawararsa ba. 14A jeji suka kamu da ƙyashi, a cikin hamada kuma suka gwada Ubanmu. 15Saboda haka ya ba su abin da suka roƙa, amma ya aiko da cuta mai ɓarnatarwa a cikinsu. 16A sansani suka ji kishin Musa, da kuma na Haruna, mai tsarki na Ubanmu. 17Ƙasa ta buɗe ta haɗiye Datan, ta kuma rufe ƙungiyar Abiram. 18Wuta ta ƙuna a kan ƙungiyarsu; harshen wuta ya ƙone mugaye.
19A Horeb suka yi ɗan maraƙi suka kuma rusuna wa gunkin ƙarfe narkakke. 20Suka musanya ɗaukakarsu da siffar bijimi mai cin ciyawa. 21Suka manta da Ubanmu, Mai cetonsu, wanda ya yi manyan abubuwa a Masar, 22al'ajibai a ƙasar Ham, ayyuka masu ban tsoro a bakin Jar Teku. b b v22 “Ƙasar Ham” wani tsohon sunan waƙa ne na Masar. 23Saboda haka ya ce zai hallaka su—da ba don Musa, zaɓaɓɓensa, ya tsaya a gurbin da ya tsage a gabansa, domin yă kau da hasalarsa daga hallaka su ba.
24Sa'an nan suka rena ƙasa mai daɗi; ba su gaskata alkawarinsa ba. 25Suka yi gunaguni a cikin tentunansu ba su kuwa saurari muryar Ubanmu ba. 26Saboda haka ya ɗaga hannunsa ya rantse cewa zai sa su fāɗi a jeji, 27zai sa zuriyarsu su fāɗi a cikin al'ummai yă kuma watsar da su cikin ƙasashe.
28Suka haɗa kai da Ba'al Feyor suka ci hadayun da aka miƙa wa gumaka marasa rai. 29Suka tsokane shi ya yi fushi da ayyukansu, sai annoba ta ɓarke a cikinsu. 30Amma Finehas ya tashi ya shiga tsakani, sai aka dakatar da annobar. 31Aka kuma lissafta masa wannan adalci ne, wa dukan tsararraki har abada. 32A ruwayen Meriba suka ba shi haushi, al'amura kuwa suka lalace wa Musa saboda su, 33gama sun sa ruhunsa yă ɗaci, sai ya yi magana babu tunani.
34Ba su hallaka mutanen ba, yadda Ubanmu ya umarce su, 35amma suka gauraya da al'ummai suka kuma koyi hanyoyinsu. 36Suka bauta wa gumakansu, waɗanda suka zama tarko gare su. 37Suka miƙa 'ya'yansu maza da 'ya'yansu mata hadaya ga aljanu. 38Suka zub da jini marar laifi, jinin 'ya'yansu maza da mata, waɗanda suka miƙa wa gumakan Kan'ana, ƙasa kuwa ta ƙazantu da jini. 39Suka ƙazantu ta wurin ayyukansu suka kuma yi karuwanci ta wurin halayensu.
40Saboda haka fushin Ubanmu ya ƙuna a kan mutanensa, ya kuwa ƙyamaci gādonsa. 41Ya ba da su ga al'ummai, masu ƙin su kuwa suka yi mulki a kansu. 42Abokan gābansu suka danne su, aka kuwa sa su a ƙarƙashin ikonsu. 43Sau da yawa ya cece su, amma a cikin dukan shirye-shiryensu sun nace ga tawaye, sai suka nutse ƙasa cikin zunubinsu. 44Duk da haka ya dubi wahalarsu sa'ad da ya ji kukansu. 45Saboda su ya tuna da alkawarinsa, ya kuma janye bisa ga yawan ƙaunarsa ta aminci. 46Ya sa dukan waɗanda suka kame su su ji tausayinsu.
47Ka cece mu, ya Ubanmu, ka tattara mu daga cikin al'ummai, domin mu gode wa sunanka mai tsarki mu kuma yi fahariya cikin yabonka.
48Albarka ta tabbata ga Uban Isra'ila, daga madawwami zuwa madawwami! Bari dukan mutane su ce, “Amin!” Halleluya!