Mutuwa da Rai suna cikin Harshe
Magana da keɓewa. Kalmomi ruwa ne mai zurfi da suke ɗauke da mutuwa ko rai, bakin wawa tarkonsa ne, amsawa kafin a saurara kuma kunya ce. Ya lura cewa wanda ya fara faɗar ƙararsa yana kama da mai gaskiya har sai an yi masa tambaya, kuma ɗan'uwan da aka ɓata wa rai yana da wuyar komowa.
18 1Wanda yake ware kansa yana bin sha'awar kansa; yakan yi faɗa da dukan hikima mai kyau. 2Wawa ba ya jin daɗin ganewa, sai dai kawai cikin bayyana ra'ayin kansa. 3Sa'ad da mugunta ta zo, sai reni ya biyo, kuma tare da wulaƙanci kan zo abin kunya. 4Kalmomin bakin mutum ruwa ne mai zurfi; maɓulɓular hikima rafi ne mai gudu. 5Ba shi da kyau a nuna sonkai ga mugu, a kuma hana wa adali adalci. 6Leɓunan wawa suna kawo faɗa, kuma bakinsa yana jawo dūka. 7Bakin wawa shi ne lalacewarsa, kuma leɓunansa tarko ne ga ransa. 8Kalmomin mai gulma suna kama da zaɓaɓɓun loma; suna gangarawa har cikin zuciya. 9Wanda yake ragwanci a aikinsa ɗan'uwan mai hallakarwa ne. 10Sunan Ubanmu hasumiya ce mai ƙarfi; adali yakan ruga cikinta ya kuma tsira. 11Dukiyar mai arziki birninsa mai katanga ne; a tunaninsa tana kama da bango mai tsawo. 12Kafin hallaka zuciyar mutum takan yi girman kai, amma tawali'u na zuwa kafin girmamawa. 13Idan mutum ya amsa kafin yă saurara, wauta ce da kuma abin kunya a gare shi. 14Ruhun mutum yana iya riƙe shi cikin rashin lafiya, amma ruhu da ya ragargaje—wa zai iya jurewa? 15Zuciya mai basira takan sami sani, kuma kunnen mai hikima yakan neme shi. 16Kyautar mutum takan buɗe masa hanya, ta kuma kai shi gaban manyan mutane. 17Wanda ya fara gabatar da ƙararsa yakan zama kamar mai gaskiya, sai wani ya zo ya bincike shi. 18Jefa ƙuri'a yakan daidaita husuma, ya kuma raba masu faɗa masu ƙarfi. 19Ɗan'uwan da aka ɓata wa rai ya fi birni mai katanga wuyar lallashi, kuma husuma tana kama da ƙyamaren kagara. 20Daga 'ya'yan bakin mutum cikinsa kan ƙoshi; da amfanin leɓunansa yakan cika. 21Mutuwa da rai suna cikin ikon harshe, kuma masu son sa za su ci 'ya'yansa. 22Wanda ya sami mata ya sami abu mai kyau, ya kuma sami tagomashi daga wurin Ubanmu. 23Matalauci yakan yi roƙon jinƙai, amma mai arziki yakan amsa da kakkausar murya. 24Mutum mai abokai da yawa yana iya lalacewa, amma akwai aboki da yake manne fiye da ɗan'uwa.