Yanzu a bugun takarda

Markus 8 FHB Father's Heart Bible™

UbaYesuRuhu
Rangwamen 15% a odarku ta farko →
Littafi

Yesu Ya Ciyar da Mutum Dubu Huɗu

Yesu ya ciyar da mutum dubu huɗu, ya ƙi ba da wata alama, ya kuma yi gargaɗi game da yisti na Farisiyawa. Wani makaho ya sami ganin gari a mataki biyu. Bitrus ya kira shi Almasihu, sa'an nan ya tsawata masa don ya ce dole ne ya mutu, aka kira shi Shaiɗan, mai tunanin al'amuran mutane ba na Ubanmu ba.

Babi na 8.

A kwanakin nan, sai babban taro ya sāke taruwa, ba su kuma da abin da za su ci. Yesu ya kira almajiransa ya ce,

“Ina jin tausayin taron nan, domin ga shi kwana uku ke nan suna tare da ni, ba su kuma da abin da za su ci. In na sallame su gida da yunwa, za su suma a hanya, domin waɗansunsu daga nesa suka zo.”

Almajiransa suka amsa masa suka ce, “A ina wani zai sami burodin da zai ƙosar da mutanen nan a nan jeji?”

Sai ya tambaye su ya ce, “Burodi guda nawa kuke da shi?” Suka ce, “Guda bakwai.”

Sai ya umarci taron su zauna a ƙasa, ya ɗauki burodin nan guda bakwai, ya yi godiya, ya kakkarya su, ya ba wa almajiransa su rarraba wa mutane, suka kuwa rarraba wa taron. Suna kuma da 'yan ƙananan kifaye; bayan ya sa musu albarka, sai ya umarci almajiran su rarraba waɗannan ma wa mutane. Suka ci suka ƙoshi. Suka kuma tattara gutsattsarin da suka rage, kwando bakwai cike. Mutane wajen dubu huɗu ne suke a wurin. Sai ya sallame su.

Nan da nan sai ya shiga jirgin ruwa tare da almajiransa, suka tafi yankin Dalmanuta.

Zamani Mai Neman Alamu

Sai Farisiyawa suka zo suka fara yin gardama da shi, suna gwada shi ta wurin neman masa alama daga Sama.

Ya yi ajiyar zuciya mai zurfi a ruhunsa, ya ce, “Me ya sa zamanin nan yake neman alama? Lalle hakika, ina gaya muku, ba za a ba wa zamanin nan wata alama ba.”

Sai ya bar su, ya sāke shiga jirgin ruwa, ya tafi ɗaya gefen.

Ku Yi Hankali da Yistin Farisiyawa

Almajiran kuwa sun manta su kawo burodi, sai dai burodi guda ɗaya suke da shi a jirgin ruwa.

Sai ya gargaɗe su ya ce, “Ku yi hankali, ku yi lura da yistin Farisiyawa da kuma yistin Hirudus.”

Suka fara tattaunawa da juna cewa ba su da burodi.

Da Yesu ya san haka, sai ya ce, “Me ya sa kuke tattaunawa cewa ba ku da burodi? Har yanzu ba ku gane ba, ba ku kuma fahimta ba? Zukatanku sun taurare ne? Kuna da idanu, ashe, ba kwa gani? Kuna da kunnuwa, ashe, ba kwa ji? Ba ku kuma tunawa? Sa'ad da na kakkarya burodi guda biyar don mutum dubu biyar, kwando nawa cike da gutsattsari kuka tattara?” Suka ce, “Goma sha biyu.”

“Sa'ad da kuma na kakkarya guda bakwai don mutum dubu huɗu, kwando nawa cike da gutsattsari kuka tattara?” Suka ce, “Bakwai.”

Sai ya ce musu, “Har yanzu ba ku fahimta ba?”

Wani Makaho Ya Sami Ganin Gari

Suka iso Betsaida, inda mutane suka kawo masa wani makaho, suka roƙi Yesu ya taɓa mutumin.

Sai ya kama hannun makahon, ya fitar da shi bayan ƙauyen, ya tofa yau a idanunsa, ya ɗibiya hannuwansa a kansa, ya tambaye shi, “Kana ganin wani abu?”

Ya ɗaga kai ya ce, “Ina ganin mutane, amma suna kama da itatuwa suna tafiya.”

Sai Yesu ya sāke ɗibiya hannuwansa a idanun mutumin; sai ya zura ido sosai, ya warke, ya ga kome a fili.

Sai ya sallame shi gida, yana cewa, “Kada ma ka shiga ƙauyen.”

Wane Ne Ni a Cewarku?

Yesu da almajiransa suka tafi ƙauyukan Kaisariya Filibi. A hanya sai ya tambaye su, “Wane ne ni a cewar mutane?”

Suka ce masa, “Yohanna Mai Baftisma; waɗansu kuwa suna cewa Iliya; waɗansu kuma, ɗaya daga cikin annabawa.”

Sai ya tambaye su, “Amma ku, wane ne ni a cewarku?” Bitrus ya amsa ya ce, “Kai ne Almasihu.”

Sai ya tsananta musu gargaɗi kada su gaya wa kowa game da shi.

Dole Ɗan Mutum Ya Sha Wahala

Sai ya fara koya musu cewa dole Ɗan Mutum ya sha wahala mai yawa, dattawa da manyan firistoci da malaman Attaura kuma su ƙi shi, a kashe shi, bayan kwana uku kuma ya tashi. A fili ya faɗi wannan. Sai Bitrus ya ja shi gefe ya fara tsawata masa.

Amma ya juya, ya dubi almajiransa, ya tsawata wa Bitrus ya ce, “Ka koma bayana, Shaiɗan! Gama ba ka kafa tunaninka a kan abubuwan Ubanmu ba, sai dai a kan abubuwan mutum.”

Sai ya kira taron da almajiransa ya ce musu, “Duk mai son bina, sai ya ƙi kansa, ya ɗauki gicciyensa, ya kuma bi ni. Gama duk mai son ceton ransa, zai rasa shi; amma duk wanda ya rasa ransa saboda ni da kuma bishara, zai cece shi. Wace riba ce mutum zai samu in ya ci riba ta dukan duniya, amma ya rasa ransa? Ko kuwa me mutum zai iya bayarwa a madadin ransa? Gama duk wanda ya ji kunyata da kuma kalmomina a cikin zamanin nan na mazinata da masu zunubi, Ɗan Mutum ma zai ji kunyarsa, sa'ad da ya zo cikin ɗaukakar Ubansa tare da mala'iku masu tsarki.”