Sa'ad da Babu Sarki a Isra'ila
Wani Balawe da ke kan hanyarsa zuwa gidan Ubanmu ya ɗauko ƙwarƙwararsa da ta gudu, bai kuwa sami kowa da ya yarda ya sauke shi ba sai wani tsoho baƙo. Mutanen garin suka kewaye gidan; Balawen ya tura ta waje. Da gari ya waye tana kwance a bakin ƙofa. Ya yanyanka ta gunduwa goma sha biyu.
19 1A kwanakin nan Isra'ila ba ta da sarki. Wani Balawe da yake zama a cikin ƙasar tuddai mai nisa ta Ifraimu ya auro wata ƙwarƙwara daga Baitlaham ta Yahuda. 2Ƙwarƙwararsa kuwa ta yi masa rashin aminci, ta bar shi ta koma gidan mahaifinta a Baitlaham ta Yahuda, ta kuma zauna a can wata huɗu. 3Sai mijinta ya kama hanya ya bi ta, domin yă lallashe ta yă dawo da ita, tare da bawansa da jakai biyu. Ita kuwa ta kai shi gidan mahaifinta, mahaifin yarinyar kuwa ya yi murna da ya gan shi. 4Surukinsa, wato mahaifin yarinyar, ya rinjaye shi yă dakata, sai ya zauna tare da shi kwana uku; suka ci, suka sha, suka kuma kwana a can.
5A rana ta huɗu suka tashi da sassafe, shi kuwa ya tashi zai tafi. Amma mahaifin yarinyar ya ce wa surukinsa, “Ka ɗan ci abinci kaɗan, sa'an nan ka tafi.” 6Sai su biyu suka zauna, suka ci, suka kuma sha tare. Mahaifin yarinyar ya ce wa mutumin, “Ina roƙonka, ka kwana a nan yau, bari zuciyarka ta yi farin ciki.” 7Mutumin ya tashi zai tafi, amma surukinsa ya matsa masa, sai ya sāke kwana a can. 8A rana ta biyar ya tashi da sassafe zai tafi; sai mahaifin yarinyar ya ce, “Ina roƙonka, ka ƙarfafa kanka, ka jira har yamma.” Sai su biyu suka ci abinci. 9Da mutumin ya tashi zai tafi, tare da ƙwarƙwararsa da bawansa, sai surukinsa, wato mahaifin yarinyar, ya ce, “Ga shi, rana ta kusa fāɗuwa; ka kwana. Duba, yini yana kusa ƙarewa; ka sauka a nan, ka ji daɗi. Gobe da sassafe ka tashi ka kama hanyarka, ka tafi gida.” 10Amma mutumin ya ƙi yă sāke kwana; ya tashi, ya tafi, ya kuma zo ɗaura da Yebus (wato Urushalima), tare da jakansa biyu masu sirdi da ƙwarƙwararsa. 11Da suka kai kusa da Yebus, rana kuwa ta kusa fāɗuwa, sai bawan ya ce wa maigidansa, “Ina roƙonka, zo mu ratsa cikin wannan birni na Yebusiyawa mu kwana a ciki.”
12Maigidansa ya amsa ya ce, “Ba za mu ratsa cikin birni na baƙi ba, wanda ba na Isra'ilawa ba ne; za mu ci gaba har Gibeya.” 13Ya ce wa bawansa, “Zo, mu kai ɗaya daga cikin waɗannan wurare, mu sauka a Gibeya ko kuwa a Rama.” 14Sai suka ci gaba da tafiyarsu, rana kuwa ta fāɗa musu kusa da Gibeya ta Benyamin. 15Suka juya don su sauka a Gibeya. Ya shiga ya zauna a dandalin birni, amma babu wanda ya karɓe su gidansa don su kwana.
16Sai ga wani tsoho yana dawowa daga aikin gona da yamma. Shi kuwa daga ƙasar tuddai ta Ifraimu ne, yana zama a Gibeya kamar baƙo; mutanen wurin kuwa Benyaminawa ne. 17Tsohon ya ɗaga kai, ya ga matafiyin a dandalin birni, sai ya ce, “Ina za ka? Daga ina ka fito?”
18Ya ce masa, “Muna tafiya ne daga Baitlaham ta Yahuda zuwa ƙasar tuddai mai nisa ta Ifraimu — a can ne gidana. Na je Baitlaham ta Yahuda, yanzu kuwa ina kan hanyata zuwa gidan Ubanmu, amma babu wanda ya karɓe ni gidansa. 19Muna da ciyawa da abinci domin jakanmu, muna kuma da abinci da ruwan inabi domina, da baiwarka, da kuma saurayin nan da yake tare da bayinka. Ba mu rasa kome ba.”
20Tsohon ya ce, “Salama a gare ka. Zan tanada maka duk abin da kake bukata; sai dai kada ka kwana a dandali.” 21Sai ya kai shi gida, ya ba wa jakai abinci, suka kuma wanke ƙafafunsu, suka ci, suka sha.
22Yayinda suke cikin jin daɗi, sai ga waɗansu mutanen banza na birnin suka kewaye gidan, suna ƙwanƙwasa ƙofa. Suka yi ihu ga tsohon mai gidan, suka ce, “Fito da mutumin da ya shiga gidanka, domin mu kwana da shi!”
23Mai gidan ya fito wurinsu ya ce, “A'a, 'yan'uwana, ina roƙonku kada ku aikata mugunta, da yake wannan mutum ya shiga gidana; kada ku yi wannan abin kunya. 24Ga 'yata budurwa da ƙwarƙwararsa — bari in fito da su. Ku ƙasƙantar da su, ku yi musu duk abin da kuka ga dama, amma kada ku yi wa wannan mutum wannan abin kunya.”
25Amma mutanen suka ƙi su saurara. Sai mutumin ya kama ƙwarƙwararsa ya tura ta waje gare su; suka yi mata fyaɗe suka wulaƙanta ta dukan dare har gari ya waye, sa'an nan suka sake ta. 26Da gari ya waye sai macen ta zo ta fāɗi a ƙofar gidan mutumin, inda maigidanta yake, har rana ta fito. 27Da safe maigidanta ya tashi, ya buɗe ƙofofin gidan, ya fito zai kama hanyarsa — sai ga ƙwarƙwararsa a kwance, ta fāɗi a mashigin gidan, hannuwanta kuwa a kan madogarar ƙofa. 28Ya ce mata, “Tashi, mu tafi.” Amma babu amsa. Sai ya ɗora ta a kan jaki, ya kama hanya zuwa gida.
29Da ya isa gida sai ya ɗauki wuƙa, ya kama ƙwarƙwararsa, ya yayyanka ta gaɓa-gaɓa gida goma sha biyu, ya kuma aika da ita ko'ina a cikin dukan ƙasar Isra'ila. 30Duk waɗanda suka gan shi suka ce, “Ba a taɓa yin ko ganin irin wannan abu ba tun ranar da Isra'ila ta fito daga ƙasar Masar har yă zuwa yau. Ku lura da shi, ku tattauna a kai, ku kuma faɗa.”