Makoki A Kan Taya
Makoki ga Taya kamar babban jirgin ruwa, da katakan fir, da ginshiƙin itacen al'ul, da filin lilin na Masar, wanda abokan cinikayya daga ko'ina da aka ambaci sunayensu suke tuƙawa suke cika masa kaya. Iskar gabas ta farfasa shi a tsakiyar teku, ma'aikatan jirgi a bakin gaci kuma suka zuba ƙura a kansu suka rera wannan waƙa.
27 1Maganar Ubanmu ta zo mini,
2“Yanzu kai, ɗan mutum, ka yi makoki a kan Taya, 3ka kuma ce wa Taya, wadda take zaune a ƙofofin teku, 'yar kasuwa ga mutane a bakin tekuna masu yawa, Ga abin da Uba Mai Iko Duka yake cewa, ‘Ke Taya, kin ce, “Ni cikakkiya ce a kyau.” 4Iyakokinki suna cikin zuciyar tekuna; maginanki sun kammala kyanki. 5Sun gina dukan katakanki da itatuwan fir daga Senir; sun ɗauko itacen al'ul daga Lebanon don su yi miki jigo. 6Sun yi filafilanki da itatuwan oak na Bashan; sun yi dakalin jirginki da hauren giwa a kafe cikin itacen saiparas daga bakin tekun Kubrus. 7Zanen jirginki lallausan lilin mai ado ne daga Masar, wanda ya zama tutarki; rumfarki kuwa shuɗi ce da shunayya daga bakin tekun Elisha. 8Mutanen Sidon da Arbad su ne matuƙanki; gwanayenki, Ya Taya, suna cikinki a matsayin masu jagorancin jirginki. 9Dattawan Gebal da gwanayenta suna cikinki, suna gyara miki wuraren da suka tsage; dukan jiragen ruwan teku tare da matuƙansu sun zo wurinki domin su yi ciniki da kayanki. 10Farisa da Lud da Fut suna cikin sojojinki, mayaƙanki. Sun rataya garkuwoyinsu da kwalkwalolinsu a katangarki, suka ba ki kwarjini. 11Mutanen Arbad da sojojinki suna kan katangarki kewaye da kewaye, akwai kuma Gammadim cikin hasumiyoyinki. Sun rataya garkuwoyinsu a kan katangarki kewaye da kewaye; sun kammala kyanki.
12“Tarshish ya yi ciniki da ke saboda yawan arzikinki na kowane iri, yana musaya da azurfa, da ƙarfe, da tin, da dalma domin kayanki.
13“Yaban, da Tubal, da Meshek sun yi ciniki da ke da rayukan mutane da kwanonin tagulla.
14“Daga Bet-togarma suka kawo dawakai, da dawakan yaƙi, da alfadarai domin kayanki.
15“Mutanen Dedan sun yi ciniki da ke; bakin tekuna masu yawa su ne kasuwanninki, suna biyanki da haurajen giwa da itacen ebony.
16“Aram ya yi ciniki da ke saboda yawan kayanki, yana musaya da duwatsun turkus, da shunayya, da aikin ɗinki, da lallausan lilin, da murjani, da yaƙutu domin kayanki.
17“Yahuda da Isra'ila sun yi ciniki da ke; alkamar Minnit, da gari, da zuma, da mai, da balsam.
18“Dimashƙu ya yi ciniki da ke saboda yawan kayanki, da yawan arzikinki na kowane iri, da ruwan inabi na Helbon, da ulu na Zahar. 19Bedan da Yaban daga Uzal sun yi ciniki domin kayanki; ƙarfen da aka ƙera, da kasiya, da kalamus suna cikin kayanki.
20“Dedan ya yi ciniki da ke da mayafan sirdi na hawa.
21“Larabawa da dukan sarakunan Kedar su ne abokan cinikinki, suna ciniki da 'yan raguna, da raguna, da awaki.
22“'Yan kasuwar Sheba da Rama sun yi ciniki da ke, suna biya da mafi kyau na dukan kayan ƙamshi, da kowane dutse mai daraja, da zinariya domin kayanki.
23“Haran, da Kanne, da Eden, 'yan kasuwar Sheba, da Asshur, da Kilmad sun yi ciniki da ke. 24Waɗannan sun yi ciniki da ke da tufafi masu kyau, da shuɗaɗɗen zane mai ɗinki, da darduma masu launuka dabam-dabam waɗanda aka ɗaura da igiyoyi aka kuma kintsa, a kasuwarki. 25Jiragen ruwan Tarshish sun ɗauki kayan cinikinki kamar ayari. Saboda haka kika cika kika kuma yi nauyi a cikin zuciyar tekuna. 26Matuƙanki sun fitar da ke zuwa manyan ruwaye; iskar gabas ta farfashe ki a cikin zuciyar tekuna. 27Arzikinki, da kayanki, da kayan cinikinki, da matuƙanki da masu jagorancin jirginki, da masu gyaran jirginki, da 'yan kasuwarki, da dukan mayaƙanki da suke cikinki, tare da dukan sauran da suke a jirgi, za su nutse cikin zuciyar tekuna a ranar faɗuwarki. 28Da jin karar kukan masu jagorancin jirginki, ƙasa mai faɗi takan girgiza. 29Dukan masu riƙe da fila, matuƙa da dukan masu jagorancin jiragen teku, sun sauka daga jiragensu; suna tsaye a ƙasa, 30suna ɗaga muryarsu a kanki suna kuka mai zafi. Suna zuba ƙura a kansu suna birgima cikin toka; 31suna aske kansu saboda ke suna kuma sa tufafin makoki, suna kuka a kanki da ɓacin rai, da makoki mai zafi. 32Cikin kukansu suna rera makoki dominki suna kuma yin makoki a kanki, “Wa ya taɓa zama kamar Taya, kamar wadda aka sa ta yi shiru a tsakiyar teku?” 33Sa'ad da kayanki suka fito daga tekuna, kika ƙosar da mutane masu yawa; da yawan arzikinki da kayan cinikinki kika azurta sarakunan duniya. 34Yanzu kuwa tekuna sun farfashe ki a cikin zurfin ruwaye; kayan cinikinki da dukan ma'aikatanki sun nutse tare da ke. 35Dukan mazaunan bakin tekuna sun firgita saboda ke, sarakunansu kuma suna rawar jiki don tsoro; fuskokinsu sun ɓaci. 36'Yan kasuwa a cikin mutane suna yi miki tsaki; kin zama abin razana, ba kuwa za ki ƙara kasancewa ba, har abada.’”