Fitilar Ubanmu
Babi na ma'aunai da manufofi: ruwan inabi mai ba'a, ma'aunai na gaskiya, mai saye wanda ya rage farashi sa'an nan ya yi taƙama da cinikinsa, gādon da aka ƙwace da wuri. Ya yarda cewa babu wanda zai iya cewa zuciyarsa tsabtatacciya ce, ya kuma kira ruhun mutum fitilar Ubanmu, mai bincika zurfafan ciki.
20 1Giya mai ba'a ce, barasa kuma mai hargitsi ce, duk wanda ya yi tangaɗi saboda ita ba mai hikima ba ne. 2Tsoron sarki yana kama da rurin zaki; duk wanda ya tsokane shi ya yi fushi, yana hasarar ransa. 3Abin daraja ne ga mutum yă nisanci jayayya, amma kowane wawa yana da saurin yin faɗa. 4Rago ba ya noma a lokacin noma; saboda haka a lokacin girbi yakan nemi amfani amma ba ya samun kome. 5Nufe-nufen zuciyar mutum ruwa ne mai zurfi, amma mai basira yakan jawo su fito. 6Mutane da yawa sukan yi shelar ƙaunarsu ta aminci, amma wa zai sami mai aminci? 7Masu adalci suna tafiya cikin kamalarsu; masu albarka ne 'ya'yansu a bayansu! 8Sarki da yake zaune a kursiyin shari'a yana shekar dukan mugunta da idanunsa. 9Wa zai iya cewa, “Na tsarkake zuciyata; na kuɓuta daga zunubina”? 10Ma'auni marar daidaito da mudu marar daidaito— Ubanmu yana ƙyamar dukansu. 11Ko yaro ma ana gane shi ta ayyukansa, ta ko halinsa mai tsabta ne da madaidaici. 12Kunnen da yake ji da idon da yake gani—Ubanmu ne ya yi dukansu. 13Kada ka so barci, don kada ka talauce; ka buɗe idanunka, za ka kuwa sami abinci a yalwace. 14“Ba shi da amfani, ba shi da amfani!” in ji mai saye—sa'an nan sai ya tafi yana taƙama da cinikinsa. 15Akwai zinariya da lu'ulu'u masu yawa, amma leɓɓan da suke magana da sani dukiya ce mai wuyar samu. 16Ka karɓi rigar wanda ya ɗauki lamunin baƙo; ka riƙe ta jingina sa'ad da ya yi haka saboda baƙi. 17Abincin da aka samu ta hanyar yaudara yana da zaƙi, amma daga baya bakin mutum zai cika da tsakuwa. 18Ana kafa shirye-shirye ta wurin shawara; saboda haka ka yi yaƙi sai da jagoranci mai hikima. 19Mai gulma yana tona asiri; saboda haka kada ka yi abota da mai yawan surutu. 20Duk wanda ya la'anci mahaifinsa ko mahaifiyarsa— za a kashe fitilarsa cikin matuƙar duhu. 21Gādon da aka samu da garaje da farko ba zai zama mai albarka a ƙarshe ba. 22Kada ka ce, “Zan rama mugunta da mugunta.” Ka jira Ubanmu, shi kuwa zai cece ka. 23Ubanmu yana ƙyamar ma'auni marar daidaito, sikelin zamba kuma ba shi da kyau. 24Ubanmu ne yake bi da takawar mutum; to yaya mutum zai iya fahimtar hanyarsa? 25Tarko ne mutum yă yi garaje yă keɓe wani abu, sa'an nan daga baya yă sāke tunani a kan alkawarin. 26Sarki mai hikima yana shekar mugaye yana kuma bi da keken sussuka a kansu. 27Ruhun mutum fitilar Ubanmu ne, yana bincika kowane sashe na ciki. 28Madawwamiyar ƙauna da aminci suna kiyaye sarki; ta wurin madawwamiyar ƙauna ake tabbatar da kursiyinsa. 29Ɗaukakar samari ita ce ƙarfinsu, amma darajar tsofaffi furfura ce. 30Dūkan da suke sa ciwo suna share mugunta, bugu kuma yana tsarkake sassan ciki.