Neman Alama Daga Sama
Bitrus ya kira shi Almasihu, Ɗan Uba Rayayye, bayan 'yan mintoci kuma aka kira shi Shaiɗan domin ya ƙi ya ji cewa dole a kashe wannan Almasihu. Bi, in ji Yesu, yana nufin ka ƙi kanka ka ɗauki gicciye, ba wai a kuɓutar da kai daga gare shi ba.
16 1Farisiyawa da Sadukiyawa suka zo wurinsa domin su gwada shi, suka roƙe shi yă nuna musu wata alama daga Sama.
2Ya amsa musu ya ce, “Sa'ad da yamma ta yi, kukan ce, ‘Yanayi zai yi kyau, gama sararin sama ya yi ja.’
3“Da safe kuma, ‘Yau za a yi hadari, gama sararin sama ya yi ja ya kuma yi duhu.’ Kun san yadda za ku karanta fuskar sararin sama, amma ba ku iya karanta alamun zamani ba.
4“Mugun zamani marar aminci yana neman alama; ba za a ba shi wata alama ba sai dai alamar Yunusa.” Sa'an nan ya rabu da su ya tafi.
Yistin Koyarwar Ƙarya
5Da almajiran suka haye zuwa ɗaya gefen tafkin, sun manta su kawo burodi.
6Yesu ya ce musu, “Ku yi hankali, ku kuma yi lura da yistin Farisiyawa da na Sadukiyawa.”
7Suka yi ta tattaunawa a tsakaninsu suna cewa, “Wannan ya faru ne domin ba mu kawo burodi ba.”
8Da Yesu ya gane haka, sai ya ce, “Me ya sa kuke tattaunawa a tsakaninku, ku masu ƙarancin bangaskiya, cewa ba ku da burodi? 9Har yanzu ba ku gane ba? Ba ku tuna burodi guda biyar na mutum dubu biyar ba, da yawan kwanduna da kuka tara?
10“Ko burodi guda bakwai na mutum dubu huɗu, da yawan kwanduna da kuka tara?
11“Yaya ba ku gane cewa ba a kan burodi nake magana da ku ba? Ku yi hankali da yistin Farisiyawa da na Sadukiyawa.”
12Sa'an nan suka gane cewa bai gaya musu su yi lura da yistin da ke cikin burodi ba ne, sai dai da koyarwar Farisiyawa da ta Sadukiyawa.
Bitrus Ya Shaida Ɗan Uba
13Da Yesu ya iso yankin Kaisariya Filibi, sai ya tambayi almajiransa, “Wa mutane suke cewa Ɗan Mutum yake?”
14Suka ce, “Waɗansu suna cewa Yahaya Mai Baftisma ne, waɗansu kuma Iliya, waɗansu kuwa Irmiya ko ɗaya daga cikin annabawa.”
15Ya ce musu, “Amma ku, wa kuke cewa ni nake?”
16Siman Bitrus ya amsa ya ce, “Kai ne Almasihu, Ɗan Uba mai rai.”
17Yesu ya amsa masa ya ce, “Siman ɗan Yunusa, mai albarka ne kai—ba nama da jini ne ya bayyana maka wannan ba, sai dai Ubana na Sama.
18“Ina kuma gaya maka, kai ne Bitrus, kuma a kan wannan dutse zan gina ikkilisiyata; ƙofofin kabari ba za su rinjaye ta ba.
19“Zan ba ka mabuɗan Mulkin Ubanmu; duk abin da ka ɗaure a duniya, za a kasance an ɗaure shi a Sama, kuma duk abin da ka kunce a duniya, za a kasance an kunce shi a Sama.”
20Sa'an nan ya yi wa almajiran gargaɗi mai tsanani kada su gaya wa kowa cewa shi ne Almasihu.
Dole Ɗa Yă Sha Wahala Yă Tashi
21Daga wannan lokaci, Yesu ya fara gaya wa almajiransa cewa dole yă tafi Urushalima, yă sha wahala mai yawa daga hannun dattawa, da manyan firistoci, da malaman Attaura, a kashe shi, a kuma tā da shi a rana ta uku.
22Bitrus ya jawo shi gefe ya tsawata masa, ya ce, “Ya Ubangiji, kada haka yă faru! Wannan ba zai taɓa faruwa da kai ba.”
23Amma ya juya ya ce wa Bitrus, “Ka koma bayana, Shaiɗan! Kai dutsen sa tuntuɓe ne a gare ni, domin ba kana tunanin abin da Ubanmu yake kula da shi ba, sai dai abin da mutane suke kula da shi.”
24Sa'an nan Yesu ya ce wa almajiransa, “Duk wanda yake so yă biyo ni, dole yă ƙi kansa, yă ɗauki gicciyensa, yă kuma bi ni.
25“Gama duk wanda yake so yă ceci ransa, zai rasa shi, amma duk wanda ya rasa ransa saboda ni, zai same shi.
26“Wace riba ce mutum zai samu in ya mallaki dukan duniya amma ya rasa ransa? Ko kuwa me mutum zai iya bayarwa a musayar ransa?
27“Gama Ɗan Mutum yana gab da zuwa cikin ɗaukakar Ubansa tare da mala'ikunsa, sa'an nan zai sāka wa kowane mutum bisa ga abin da ya aikata.
28“Lalle hakika, ina gaya muku, waɗansu da suke tsaye a nan ba za su ɗanɗana mutuwa ba, sai sun ga Ɗan Mutum yana zuwa cikin mulkinsa.”