Ka Tsage Sammai
Wannan addu'a ce cewa Ubanmu ya tsage sararin sama ya sauko. Ba ta kāre jama'a ba, tana kiran ayyukansu mafi kyau ƙazamin tufa, tana kuma yarda cewa ba wanda yake riƙe shi. An ƙone haikalin. Ta ƙare da tambayar da ba a amsa ba.
64 1Kash, da ma ka tsage sammai ka sauko, har duwatsu su girgiza a gabanka, 2kamar yadda wuta takan sa ciyawa ta ƙuna, takan kuma sa ruwa ya tafasa — domin ka sanar da sunanka ga magabtanka, har al'ummai su yi rawar jiki a gabanka! 3Sa'ad da ka yi abubuwa masu ban al'ajabi da ba mu zata ba, sai ka sauko, duwatsu kuma suka girgiza a gabanka. 4Tun fil azal, ba wanda ya taɓa ji ko ya gane da kunne, ba idon da ya taɓa ganin wani banda kai, wanda kake aiki domin wanda yake jiranka. 5Kana marabtar waɗanda suke yin abin da yake daidai da farin ciki, waɗanda suke tuna da kai sa'ad da suke tafiya a hanyoyinka. Amma ka yi fushi, mun kuwa yi zunubi; tun da daɗewa muna cikin zunubanmu — ko za a iya cece mu? 6Dukanmu mun zama kamar marar tsarki, dukan ayyukanmu na adalci kuma sun zama kamar ƙazamar tufa. Dukanmu mun yanƙwane kamar ganye, zunubanmu kuma, kamar iska, suna kwashe mu. 7Babu wanda yake kiran sunanka, wanda yake tāyar da kansa ya riƙe ka; gama ka ɓoye fuskarka daga gare mu, ka kuma bashe mu ga zunubanmu.
8Amma yanzu, kai ne Ubanmu; mu laka ne, kai kuwa mai yin tukwanenmu ne; dukanmu aikin hannunka ne. 9Kada ka yi fushi mai tsanani haka, ya Ubanmu, kada kuma ka riƙa tuna da zunubinmu har abada. Ka duba, muna roƙonka — dukanmu mutanenka ne. 10Birane masu tsarki naka sun zama jeji; Sihiyona ta zama jeji, Urushalima kuma ta zama kufai. 11Gidanmu mai tsarki, mai kyau, inda kakanninmu suka yabe ka, an ƙone shi da wuta, dukan abin da muka ƙaunata kuma ya zama kango. 12Bayan dukan wannan, za ka ƙame kanka ne, ya Ubanmu? Za ka yi shiru ka kuma wahalshe mu haka ƙwarai?