Yesu, Mai Iko na Ceto
Wani yana zuwa daga Edom da tufafi masu ɗigon jini, ya taka matsewar inabi shi kaɗai ba mai taimako. Sa'an nan tunawa ta zama mai taushi: Ubanmu ya sha wahala cikin wahalar mutanensa, yana ɗauke da su, har suka ɓata wa Ruhunsa rai. Ya ƙare da tambayar ina jinƙansa ya tafi.
63 1Wane ne wannan mai zuwa daga Edom, cikin tufafi masu jajayen tabo daga Bozra, wannan mai ɗaukaka cikin tufafinsa, yana taƙama da ikonsa mai girma? “Ni ne, mai shelar adalci, mai iko na ceto.” a a v1 Manzo Yohanna ya ga Yesu, sanye da riga wadda aka tsoma cikin jini, yana tattaka wurin matsin inabi na fushin Ubansa — Ru'ya ta Yohanna 19:11-15.
2Me ya sa tufafinka ja suke, tufafinka kuma kamar na mai tattaka a wurin matsin inabi?
3“Na tattaka wurin matsin inabi ni kaɗai, daga cikin mutane kuwa babu wanda yake tare da ni; na murƙushe su cikin fushina na kuma tattake su cikin hasalata; jininsu ya yayyafa a tufafina, na kuma ɓata dukan tufafina. 4Gama ranar sakayya tana a zuciyata, shekarar fansata kuwa ta zo. 5Na duba, amma babu mai taimako; na yi mamaki domin babu wanda ya goyi bayana; saboda haka hannuna da kansa ya kawo mini ceto, hasalata kuma ta goyi bayana. 6Na tattake mutane cikin fushina; na buge su da maye cikin hasalata, na kuma zubar da jininsu a ƙasa.”
Zan Faɗi Ƙaunar Ubanmu
7Zan faɗi madawwamiyar ƙaunar Ubanmu, yabonsa, bisa ga dukan abin da ya yi mana, da kyautatawa mai girma da ya nuna wa gidan Isra'ila, bisa ga jinƙansa, bisa ga yawan madawwamiyar ƙaunarsa.
8Gama ya ce, “Hakika su mutanena ne, 'ya'ya waɗanda ba za su yi ha'inci ba.” Sai ya zama Mai cetonsu.
9Cikin dukan wahalarsu shi ma ya sha wahala, mala'ikan fuskarsa kuwa ya cece su; cikin ƙaunarsa da jinƙansa ya fanshe su; ya ɗaga su sama ya kuma ɗauke su dukan kwanakin dā. 10Amma suka yi tawaye suka kuma ɓata wa Ruhunsa Mai Tsarki rai; saboda haka ya juya ya zama maƙiyinsu, shi kansa kuma ya yaƙe su. 11Sai ya tuna da kwanakin dā, na Musa da na mutanensa. Ina wanda ya fitar da su daga teku, tare da makiyayan garkensa? Ina wanda ya sa Ruhunsa Mai Tsarki a cikinsu, 12wanda ya miƙa hannunsa mai ɗaukaka a hannun daman Musa, wanda ya raba ruwaye a gabansu domin yă yi wa kansa suna madawwami, 13wanda ya bi da su ta cikin zurfafa? Kamar doki a jeji, ba su yi tuntuɓe ba. 14Kamar dabbobin da suke gangarawa zuwa kwari, Ruhun Ubanmu ya ba su hutawa. Haka ka bi da mutanenka, domin ka yi wa kanka suna mai ɗaukaka.
Ka Duba Daga Sama
15Ka duba daga sama ka gani, daga mazauninka mai tsarki da ɗaukaka. Ina himmarka da manyan ayyukanka? An hana ni motsin zuciyarka da jinƙanka. 16Gama kai ne Ubanmu, ko da yake Ibrahim bai san mu ba, Isra'ila kuma bai yarda da mu ba; kai ne Ubanmu; Mai Fansarmu tun zamanin dā shi ne sunanka. 17Me ya sa, ya Ubanmu, kake bar mu muna karkacewa daga hanyoyinka kake kuma taurare zuciyarmu, har ba ma tsoronka? Ka komo saboda bayinka, kabilan gādonka. 18Na ɗan lokaci kaɗan mutanenka masu tsarki suka mallaki wurin; maƙiyanmu sun tattake wurinka mai tsarki. 19Mun zama kamar waɗanda ba ka taɓa yin mulki a kansu ba, kamar waɗanda ba a kira su da sunanka ba.