Dokokin da Suke Kwace wa Matalauta
Assuriya sanda ce a hannun Ubanmu amma ba ta sani ba — gatari da yake fahariya a kan wanda yake sara da shi — saboda haka za a hukunta girmankan kayan aikin ma. An bi diddigin tafiyar mai kai harin gari bayan gari har ya kaɗa wa Urushalima dunƙulensa.
10 1Kaiton waɗanda suke kafa dokoki marasa adalci, ga marubutan da suke fitar da dokokin danniya, 2domin su hana matalauta adalci, su kuma kwace wa masu bukata a cikin mutanena hakkinsu, suna mai da gwauraye ganimarsu, marayu kuma abin farautarsu. 3Me za ku yi a ranar hisabi, sa'ad da hallaka ta zo daga nesa? Ga wa za ku gudu nemi taimako? A ina za ku bar dukiyarku? 4Babu abin da ya rage sai dai ku tsugunna a cikin kamammu, ko ku fāɗi a cikin waɗanda aka kashe. Duk da haka, fushinsa bai huce ba; hannunsa kuma har yanzu a miƙe yake.
Assuriya, Sandan da ke Hannunsa
5“Kaiton Assuriya, sandan fushina, wanda a hannunsa akwai kulkin hasalata! 6Ina aike shi gāba da al'ummar da ba ta bin Allah; a kan mutanen da na yi fushi da su na umarce shi, yă kwashe ganima yă kuma yi washe, yă tattake su kamar laka a kan tituna.”
7Amma ba haka yake nufi ba; ba haka zuciyarsa ta shirya ba. Nufinsa shi ne yă hallaka, yă hallaka al'umma bayan al'umma. 8Gama ya ce, “Ashe, dukan hafsoshina ba sarakuna ba ne? 9Ashe, Kalno ba kamar Karkemish ba ce? Hamat ba kamar Arfad ba ce? Samariya ba kamar Dimashƙu ba ce? 10Kamar yadda hannuna ya ƙwace mulkoki na gumaka, waɗanda sassaƙaƙƙun gumakansu suka fi na Urushalima da Samariya, 11ashe ba zan yi da Urushalima da siffofinta yadda na yi da Samariya da gumakanta ba?”
12Sa'ad da Ubangiji Uba ya gama dukan aikinsa a kan Dutsen Sihiyona da Urushalima, zan hukunta sakamakon girman kan sarkin Assuriya, da fariyar idanunsa masu girma.
13Gama ya ce, “Da ƙarfin hannuna na yi wannan, da kuma hikimata, gama ina da fahimi. Na kawar da iyakokin mutane, na kuma washe dukiyoyinsu; na saukar da waɗanda suke zaune a kan karaga kamar jarumi. 14Hannuna ya nemo dukiyar mutane kamar cikin sheƙa; kamar yadda mutum yake tattara ƙwai da aka yashe, na tattara dukan duniya. Babu ko ɗaya da ya motsa fiffike, ko ya buɗe baki yă yi cilla. 15Ashe, gatari zai ɗaukaka kansa a kan wanda yake kaɗa shi? Ashe, zarto zai yi fahariya a kan wanda yake amfani da shi? Kamar dai sanda zai iya kaɗa wanda ya ɗaga shi, kamar dai kulki zai iya ɗaga abin da ba itace ba ne!” 16Saboda haka Ubangiji Uba, Uban rundunonin Sama, zai aiko da cuta mai ɓata jiki a cikin jarumawansa masu ƙarfi, a ƙarƙashin ɗaukakarsa kuma wuta za ta ruruwa kamar harshen wuta mai cin wuta. 17Hasken Isra'ila zai zama wuta, Mai Tsarkinmu kuwa harshen wuta; a rana guda kuma za ta ƙone ta cinye ƙayayuwansa da sarƙaƙƙiyarsa. 18Ɗaukakar kurminsa da gonarsa mai albarka, Ubanmu zai hallaka, rai da jiki duka; zai zama kamar sa'ad da maras lafiya yake narkewa. 19Saurun itatuwan kurminsa za su yi kaɗan ƙwarai har yaro zai iya ƙirga su.
Sāke Dogara ga Ubanmu
20A wannan rana, raguwar Isra'ila da saurun gidan Yaƙubu ba za su ƙara dogara ga wanda ya buge su ba, sai dai za su dogara da gaskiya ga Ubanmu, Mai Tsarki na Isra'ila. 21Raguwa za ta dawo— raguwar Yaƙubu—ga Allah Maɗaukaki. 22Ko da yake mutanenka Isra'ila suna kamar yashin teku, raguwa kaɗai za ta dawo. An ƙaddara hallaka, wadda take cike da adalci. 23Gama Ubangiji Uba, Uban rundunonin Sama, zai aiwatar da hallakar da aka ƙaddara a cikin dukan ƙasar.
24Saboda haka Ubangiji Uba, Uban rundunonin Sama, ya ce, “Mutanena da suke zaune a Sihiyona, kada ku ji tsoron Assuriya, wadda take bugunku da sanda, take kuma ɗaga kulki a kanku yadda Masar ta yi. 25Gama cikin ɗan ƙanƙanin lokaci hasalata za ta ƙare, fushina kuma zai juya ga hallakarsu.” 26Uban rundunonin Sama zai daga bulala a kansu, kamar lokacin da ya bugi Midiyawa a dutsen Oreb; zai ɗaga sandansa a kan teku kamar yadda ya yi a Masar. a a v26 Dutsen Oreb shi ne inda mayaƙan Gidiyon suka kashe hafsoshin Midiyawa (Alƙalai 7:25). 27A wannan rana, za a ɗauke nauyinsu daga kafaɗarka, karkiyarsu kuma daga wuyanka; za a karya karkiyar.
28Ya zo gāba da Aiyat, ya ratsa ta Migron, ya ajiye kayansa a Mikmash. 29Sun ƙetare mashigin, suna cewa, “Za mu kafa sansani a Geba.” Rama tana rawar jiki; Gibeya ta Saul ta gudu. 30Ki yi kuka da ƙarfi, ya 'yar Gallim! Ki saurara, ya Laisha! Ya kaiton Anatot! 31Madmena tana gudu; mutanen Gebim suna neman mafaka. 32A wannan rana kuwa zai tsaya a Nob, yana girgiza hannunsa ga dutsen 'yar Sihiyona, tudun Urushalima. 33Ga shi, Ubangiji Uba, Uban rundunonin Sama, zai sare rassa da iko mai bantsoro; za a saukar da itatuwa mafi tsayi, a ƙasƙantar da masu ɗaukaka. 34Zai sassare kurmin daji da gatari, Lebanon kuma zai fāɗi a gaban Maɗaukaki.