Yanzu a bugun takarda

2 Sarakuna 8 FHB Father's Heart Bible™

UbaYesuRuhu
Rangwamen 15% a odarku ta farko →
Littafi

Uba Ya Mayar mata da Ƙasarta

Mutuniyar Shunem ta komo daga yunwar da Ubanmu ya kira, ta kuma sami gonarta a daidai lokacin da Gehazi yake ba sarki labarinta. A Dimashƙu, Elisha ya yi kuka yana gaya wa Hazayel abin da zai yi wa Isra'ila; kashegari Hazayel ya shaƙe ubangidansa ya hau gadon sarauta.

Babi na 8.

Elisha ya gaya wa macen da ya rayar da ɗanta, “Ki tashi, ki tafi, ke da gidanki, ki zauna duk inda za ki iya, gama Ubanmu ya kirawo yunwa, wadda za ta auka wa ƙasar har shekara bakwai.”

Macen ta tashi, ta yi yadda mutumin Ubanmu ya faɗa, ta tafi, ita da gidanta, don ta zauna a ƙasar Filistiyawa shekara bakwai. Bayan shekara bakwai, macen ta dawo daga ƙasar Filistiyawa, sai ta tafi don ta roƙi sarki game da gidanta da ƙasarta. Sarki yana magana da Gehazi, bawan mutumin Ubanmu, ya ce, “Ka gaya mini dukan manyan abubuwan da Elisha ya yi.” Yayinda Gehazi yake gaya wa sarki yadda Elisha ya rayar da mataccen, sai ga macen da ya rayar da ɗanta ta zo tana kuka ga sarki saboda gidanta da gonarta. Gehazi ya ce, “Ranka yă daɗe sarki, ga macen nan, kuma ga ɗanta da Elisha ya rayar.”

Sarki ya tambayi macen, ita kuwa ta ba da bayani. Sai ya sanya mata wani jami'i, ya ce, “Ka mayar mata da dukan abin da yake nata, har da dukan amfanin gonar tun ranar da ta bar ƙasar har yă zuwa yanzu.”

Uba Ya Bayyana Tasowar Hazayel kan Sarauta

Elisha ya zo Dimashƙu. Ana nan Ben-hadad sarkin Aram yana fama da ciwo, sai aka gaya masa, “Mutumin Allah ya zo nan.”

Sarki ya ce wa Hazayel, “Ka ɗauki kyauta, ka tafi ka taryi mutumin Allah, ka kuma tambayi Ubangiji ta wurinsa, Zan warke daga wannan ciwo?”

Hazayel ya tafi don ya tarye shi, ya ɗauki kyauta na dukan kyawawan kayan Dimashƙu, wato kayan ɗaukar raƙuma arba'in. Ya tsaya a gaban Elisha, ya ce, “Ɗanka Ben-hadad sarkin Aram ya aiko ni in tambaya, ‘Zan warke daga wannan ciwo?’”

Elisha ya ce, “Ka tafi ka gaya masa, ‘Lalle za ka warke,’ amma Ubanmu ya nuna mini cewa lalle zai mutu.” Ya zura masa ido har Hazayel ya ji kunya. Sa'an nan mutumin Ubanmu ya yi kuka.

Hazayel ya tambaya, “Me ya sa ranka yă daɗe yake kuka?” Ya amsa ya ce, “Domin na san irin lahanin da za ka yi wa Isra'ilawa: za ka ƙone kagarunsu, ka kashe samarinsu da takobi, ka fyaɗe ƙananansu a ƙasa, ka kuma tsage cikunan matansu masu juna biyu.”

Hazayel ya amsa ya ce, “Mene ne bawanka, kare kawai, da zai yi irin wannan babban abu?” Elisha ya amsa ya ce, “Ubanmu ya nuna mini cewa za ka zama sarki a kan Aram.”

Hazayel ya bar Elisha, ya koma wurin maigidansa, wanda ya tambaye shi, “Me Elisha ya faɗa?” Ya amsa ya ce, “Ya gaya mini cewa lalle za ka warke.”

Kashegari, Hazayel ya ɗauki kyalle mai kauri, ya tsoma shi cikin ruwa, ya shimfiɗa shi a fuskar sarki, sai ya mutu. Hazayel kuwa ya gāji sarautarsa.

Yehoram Ya Yi Sarauta a Yahuda

A shekara ta biyar ta sarautar Yoram ɗan Ahab, sarkin Isra'ila, sa'ad da Yehoshafat yake sarkin Yahuda, Yehoram ɗan Yehoshafat ya fara sarauta a matsayin sarkin Yahuda. Yana da shekara talatin da biyu sa'ad da ya zama sarki, ya kuma yi sarauta shekara takwas a Urushalima. Ya bi hanyoyin sarakunan Isra'ila, kamar yadda gidan Ahab ya yi, gama ya auri 'yar Ahab. Ya kuma aikata mugunta a gaban Ubanmu. Duk da haka Ubanmu bai yarda ya hallaka Yahuda ba, saboda Dawuda bawansa, yadda ya yi alkawari zai ba Dawuda da 'ya'yansa fitila har abada.

A zamaninsa Edom ya yi tawaye ga mulkin Yahuda, ya naɗa wa kansa sarki. Yoram ya ƙetare zuwa Za'ir tare da dukan karusansa, ya tashi da dare, ya bugi Edomawa da suka kewaye shi da kuma shugabannin karusai, amma rundunar ta gudu zuwa tentunansu. Har yă zuwa yau Edom yana cikin tawaye ga mulkin Yahuda. A lokaci guda Libna ma ta yi tawaye. Sauran ayyukan Yoram, da dukan abin da ya yi—ba a rubuce suke a cikin Littafin Tarihin Sarakunan Yahuda ba? Yoram ya mutu, aka binne shi tare da kakanninsa a Birnin Dawuda. Ahaziya ɗansa ya gāji sarautarsa.

Ahaziya Ya Yi Sarauta a Yahuda

A shekara ta goma sha biyu ta sarautar Yoram ɗan Ahab, sarkin Isra'ila, Ahaziya ɗan Yehoram, sarkin Yahuda, ya fara sarauta. Ahaziya ya zama sarki yana da shekara ashirin da biyu; ya yi sarauta shekara ɗaya a Urushalima. Mahaifiyarsa Ataliya jikanyar Omri sarkin Isra'ila ce. Ya bi hanyar gidan Ahab, ya aikata mugunta a gaban Ubanmu kamar gidan Ahab, don shi surukin gidan Ahab ne.

Ya tafi tare da Yoram ɗan Ahab don su yaƙi Hazayel sarkin Aram a Ramot-gileyad, inda Aramawa suka ji wa Yoram rauni. Sarki Yoram ya koma Yezre'el don yă warke daga raunukan da Aramawa suka yi masa a Rama, sa'ad da yake yaƙi da Hazayel sarkin Aram. Ahaziya ɗan Yehoram, sarkin Yahuda, ya gangara don yă ga Yoram ɗan Ahab da ya ji rauni a Yezre'el.