Waƙa don Keɓewa
Zabura. Waƙa don keɓe gidan. Ta Dawuda.
An rubuta shi domin keɓewa bayan warkarwa. Dawuda ya furta cewa sa'ad da al'amura suke tafiya da kyau ya ɗauka ba za a taɓa girgiza shi ba, sa'an nan aka ɓoye fuskar Ubansa. Ya yi hujja cewa ƙura ba ta iya yabo, ya kuma ƙare da tufafin makoki da aka musanya da farin ciki.
30 1Zan ɗaukaka ka, Ubana, gama ka ɗaga ni sama, ba ka kuwa bar maƙiyana su yi murna a kaina ba.
2Ubana, na yi kira gare ka don neman taimako, ka kuwa warkar da ni. 3Ubana, ka fito da raina daga kabari; ka kiyaye ni da rai, ba ka kuwa bar ni in gangara cikin rami ba.
4Ku rera waƙa ga Ubanmu, ku masu aminci gare shi, ku kuma gode wa sunansa mai tsarki. 5Gama fushinsa na ɗan lokaci ne kawai, amma tagomashinsa na dukan rayuwa ne; kuka yakan kwana da dare, amma farin ciki yakan zo da safe.
6Sa'ad da nake cikin kwanciyar hankali, na ce, “Ba zan taɓa girgizuwa ba.” 7Ubana, ta wurin tagomashinka ka sa dutsena ya tsaya daram; amma sa'ad da ka ɓoye fuskarka, sai na firgita.
8Gare ka, Ubana, na yi kira; ga Uba Mai Iko Duka na yi roƙon jinƙai, 9“Wane amfani ake samu in an sa ni yi shiru, in na gangara cikin rami? Ƙura za ta yabe ka ne? Za ta yi shelar amincinka ne? 10Ka ji ni, Ubana, ka kuma yi mini alheri; Ubana, ka zama mataimakina.”
11Ka mai da makokina ya zama rawa; ka cire mini tufafin makoki, ka kuma suturta ni da farin ciki, 12domin zuciyata ta rera yabonka, kada kuma ta yi shiru. Ubana, zan gode maka har abada.