Umarnan Uba, Rayuwar Ɗa
Shawara ga ɗa, galibi game da dogara: kada ka dogara ga fahimtarka, ka girmama Ubanmu da abin da kake samu, kada ka ji haushin horonsa. Sa'an nan hikima da ta fi azurfa daraja, da dokokin maƙwabtaka kai tsaye, har da biyan bashin da ake binka yau maimakon gobe.
3 1Ɗana, kada ka manta da koyarwata, amma bari zuciyarka ta kiyaye umarnaina, 2gama za su ƙara maka tsawon kwanaki da shekarun rai da salama. 3Kada ka bar madawwamiyar ƙauna da aminci su rabu da kai; ka ɗaura su kewaye da wuyanka, ka rubuta su a allon zuciyarka. 4Ta haka za ka sami tagomashi da kyakkyawan suna a gaban Ubanmu da kuma a gaban mutane.
5Ka dogara ga Ubanmu da dukan zuciyarka, kada kuma ka jingina ga ganewarka. 6A cikin dukan hanyoyinka ka san shi, shi kuwa zai miƙe maka hanyoyinka.
7Kada ka zama mai hikima a idonka; ka ji tsoron Ubanmu, ka kuma juya baya ga mugunta. 8Wannan zai kawo lafiya ga jikinka da kuma sabuntawa ga ƙasusuwanka.
9Ka girmama Ubanmu da dukiyarka da kuma nunan fari na dukan amfaninka, a a v9 Nunan fari shi ne sashi na farko kuma mafi kyau na girbi, da ake miƙa wa Ubanmu kafin a yi amfani da wani sashinsa. 10sa'an nan rumbunanka za su cika da yalwa, randunanka kuma za su yi ambaliya da sabon ruwan inabi.
11Ɗana, kada ka rena horon Ubanmu, kada kuma ka gaji da gyaransa, 12gama Ubanmu yakan hori wanda zuciyarsa take ƙauna, kamar yadda uba yakan hori ɗan da yake farin ciki da shi.
13Mai albarka ne wanda ya sami hikima, da kuma wanda ya sami ganewa, 14gama ribar da ake samu daga gare ta ta fi ta azurfa, ribarta kuma ta fi ta zinariya. 15Ta fi duwatsu masu daraja tamani, kuma babu wani abin da kake marmari da ya kai ta. 16Tsawon rai yana a hannunta na dama; a hannunta na hagu kuwa akwai dukiya da girma. 17Hanyoyinta masu daɗi ne, dukan hanyoyinta kuma salama ne. 18Ita itaciyar rai ce ga waɗanda suka riƙe ta; ana ce da waɗanda suka riƙe ta ƙwarai masu albarka.
19Ubanmu ta wurin hikima ya kafa duniya; ta wurin ganewa ya kafa sammai; 20ta wurin saninsa aka tsage zurfafan ruwaye, gizagizai kuma suna zubo da raɓa.
21Ɗana, kada ka rasa ganin waɗannan; ka riƙe ingantacciyar hikima da hankali, 22za su kuma zama rai ga ranka da kuma ado ga wuyanka. 23Sa'an nan za ka yi tafiya cikin aminci a hanyarka, ƙafarka kuma ba za ta yi tuntuɓe ba. 24In ka kwanta, ba za ka ji tsoro ba; sa'ad da ka kwanta, barcinka zai yi daɗi. 25Kada ka ji tsoron fargaba ba zato ba tsammani, ko na hallakar da mugaye sa'ad da ta zo, 26gama Ubanmu zai zama gabagaɗinka, zai kuma kiyaye ƙafarka daga fāɗawa tarko.
27Kada ka hana alheri ga waɗanda suka cancanci shi, sa'ad da yake cikin ikonka ka yi haka. 28Kada ka ce wa maƙwabcinka, “Je ka, ka komo, gobe kuwa zan ba ka”—alhali kana da shi a hannunka. 29Kada ka ƙulla wa maƙwabcinka mugunta, wanda yake zama kusa da kai cikin aminci. 30Kada ka yi gardama da wani ba dalili, sa'ad da bai yi maka wata illa ba.
31Kada ka yi kishin mutum mai tashin hankali, kada kuma ka zaɓi waɗansu hanyoyinsa, 32gama mai karkataccen hali abin ƙyama ne ga Ubanmu, amma yana ba masu adalci sirrinsa. 33La'anar Ubanmu tana a kan gidan mugaye, amma yana sa wa gidan masu adalci albarka. 34Ga masu ba'a yana reni, amma ga masu tawali'u yana ba da alheri. 35Masu hikima za su gāji girma, amma wawaye kunya kaɗai za su samu.