Ku Saurara, 'Ya'yana
Wani uba yana miƙa abin da nasa mahaifin ya faɗa masa, babin kuma ba ya mance da wannan sarƙa. Hotunansa game da hanya ne: hanyar da take ƙara haske har zuwa hantsi, gāba da wadda take da duhu ƙwarai har ba ka ganin abin da ya sa ka tuntuɓe. Ka tsare zuciyarka, ka duba gaba sosai.
4 1Ku saurari gargaɗin uba, 'ya'yana; ku kasa kunne, ku kuma sami fahimi. 2Ina ba ku kyakkyawar koyarwa, saboda haka kada ku yar da koyarwata. 3Gama ni ma na kasance ɗa ga mahaifina, yaro mai laushi, makaɗaici kuma ƙaunataccen mahaifiyata. 4Ya koya mini ya ce, “Bari zuciyarka ta riƙe kalmomina; ka kiyaye umarnaina, za ka kuwa rayu. 5Ka nemi hikima, ka nemi fahimi; kada ka manta, kada kuma ka juya baya daga kalmomin bakina. 6Kada ka yashe ta, za ta kuwa tsare ka; ka ƙaunace ta, za ta kuwa lura da kai. 7Farkon hikima shi ne wannan: ka nemi hikima; kuma da duk abin da ka samu, ka nemi fahimi. 8Ka darajanta ta, za ta kuwa ɗaukaka ka; ka rungume ta, za ta kuwa kawo maka girma. 9Za ta sa kambin alheri a kanka; za ta ba ka rawanin ɗaukaka.”
10Ka saurara, ɗana, ka kuma karɓi kalmomina, shekarun ranka kuwa za su yi yawa. 11Na koya maka hanyar hikima; na bishe ka a miƙaƙƙun hanyoyi. 12Sa'ad da kake tafiya, ba za a tsai da takawarka ba; sa'ad da kuma kake gudu, ba za ka yi tuntuɓe ba. 13Ka riƙe gargaɗi, kada ka saki; ka tsare ta, gama ita ce ranka.
14Kada ka taka hanyar mugaye, kada kuma ka bi hanyar masu aikata mugunta. 15Ka guje mata, kada ka bi ta; ka juya daga gare ta ka wuce. 16Gama ba sa iya barci sai sun aikata mugunta; an hana su hutu sai sun sa wani ya yi tuntuɓe. 17Suna cin burodin mugunta suna kuma shan ruwan inabin tashin hankali.
18Amma hanyar masu adalci kamar hasken safiya take, tana ƙara haskakawa har ya kai cikakken hasken yini. 19Hanyar mugaye kamar baƙin duhu take; ba su san abin da yake sa su tuntuɓe ba.
20Ɗana, ka kasa kunne ga kalmomina; ka saurari maganganuna sosai. 21Kada ka kau da ido daga gare su; ka kiyaye su cikin zuciyarka. 22Gama su rai ne ga waɗanda suka same su, su kuma warkarwa ne ga dukan jikinsu.
23Fiye da kome, ka kiyaye zuciyarka, gama daga gare ta ne dukan abin da kake yi yake fitowa. 24Ka kawar da karkataccen magana daga bakinka, ka kuma nisanta leɓunan ƙarya daga gare ka. 25Bari idanunka su dubi gaba kai tsaye; ka kafa kallonka daidai gabanka. 26Ka yi tunani sosai a kan hanyar ƙafafunka, dukan hanyoyinka kuwa za su zama tsayayyu. 27Kada ka karkata dama ko hagu; ka kiyaye ƙafarka daga mugunta.