Koyarwa a Garuruwansu
Yahaya, yana cikin kurkuku, ya aika a tambaya ko Yesu shi ne wanda ake jira da gaske. Amsar jerin abubuwan da ke faruwa ne, ba kwantar da hankali ba. Sa'an nan Yesu ya la'anci garuruwan da suka ga mu'ujizansa amma ba su canja ba, ya gode wa Ubansa, ya kuma ba da hutu ga duk wanda ya gaji tilis.
11 1Bayan Yesu ya gama koya wa almajiransa goma sha biyu, sai ya tashi daga wurin don yă koyar yă kuma yi wa'azi a garuruwansu.
Tambayar Yohanna daga Kurkuku
2Sa'ad da Yohanna yake kurkuku, ya ji labarin ayyukan Almasihu, sai ya aika saƙo ta wurin almajiransa, 3ya tambaye shi, “Kai ne wanda zai zo, ko kuwa mu jira wani dabam?”
4Yesu ya amsa musu ya ce, “Ku tafi ku ba Yohanna labarin abin da kuke ji kuke kuma gani,
5“Makafi suna ganin gani, guragu suna tafiya, ana tsarkake kutare, kurame suna ji, ana tā da matattu, ana kuma yi wa matalauta wa'azin bishara. 6Mai albarka kuwa shi ne wanda ba ya tuntuɓe saboda ni.”
7Yayin da suke tafiya, sai Yesu ya fara wa taron magana game da Yohanna, “Me kuka fita zuwa jeji domin ku gani? Kyauron da iska take girgiza shi? 8To, me kuka fita don ku gani—mutumin da yake saye da riguna masu laushi? Ga shi, masu sa riguna masu laushi suna cikin fadodin sarakuna. 9To, me kuka fita don ku gani? Annabi? I, ina gaya muku, ya fi annabi nesa. 10Wannan shi ne wanda aka rubuta a kansa cewa, ‘Ga shi, ina aiken manzona a gabanka, wanda zai shirya maka hanya a gabanka.’ 11Lalle hakika, ina gaya muku, cikin dukan waɗanda mata suka haifa, babu wanda ya taso da ya fi Yohanna Mai Baftisma girma; duk da haka, mafi ƙanƙanta a Mulkin Ubanmu ya fi shi girma. 12Tun daga kwanakin Yohanna Mai Baftisma har yă zuwa yanzu, ana ta tsananta wa Mulkin Ubanmu, masu tsanani kuwa suna ƙwace shi da ƙarfi. 13Gama dukan Annabawa da Shari'a sun yi annabci har zuwa lokacin Yohanna, 14In kuwa kuna niyyar karɓa, shi ne Iliya wanda zai zo. 15Duk mai kunnen ji, yă ji.
16Da me zan kwatanta mutanen zamanin nan? Suna kama da yara da suke zaune a kasuwanni, suna kiran waɗansu, 17‘Mun busa sarewa dominku, amma ba ku yi rawa ba; mun yi waƙar makoki, amma ba ku yi makoki ba.’ 18Gama Yohanna ya zo, ba ya ci ba ya sha, sai suka ce, ‘Yana da aljani.’ 19Ɗan Mutum ya zo yana ci yana sha, sai suka ce, ‘Ga mai haɗama da mashayi, abokin masu karɓar haraji da masu zunubi!’ Duk da haka, an tabbatar da adalcin hikima ta wurin ayyukanta.”
Kaiton Garuruwan da Ba su Tuba ba
20Sa'an nan ya fara tsawata wa garuruwan da ya yi yawancin mu'ujizansa a cikinsu, domin ba su tuba ba.
21“Kaitonki, Korazin! Kaitonki, Betsaida! Gama da a ce an yi mu'ujizan da aka yi a cikinki a Taya da Sidon ne, da tun da daɗewa sun tuba, sanye da tufafin makoki suna zaune cikin toka. 22Amma ina gaya muku, a ranar shari'a hukuncin Taya da Sidon zai fi na ku sauƙi. 23Ke kuwa, Kafarnahum—ko za a ɗaga ki zuwa sama ne? Za a saukar da ke har zuwa Lahira. Gama da a ce an yi mu'ujizan da aka yi a cikinki a Saduma ne, da har yau tana nan a tsaye. 24Amma ina gaya muku, a ranar shari'a ƙasar Saduma za ta fi ku sauƙi.”
Ɗa ya Bayyana Uba
25A lokacin nan Yesu ya ce, “Ina yabonka, ya Uba, Mai Mulkin sama da ƙasa, domin ka ɓoye waɗannan abubuwa daga masu hikima da masu basira, ka kuwa bayyana su ga jarirai. 26I, ya Uba, gama haka ya gamshe ka. 27Ubana ya danƙa mini dukkan kome. Ba wanda ya san Ɗa sai Uba, ba kuma wanda ya san Uba sai Ɗa, da kuma duk wanda Ɗa ya zaɓa yă bayyana masa Uba.
28“Ku zo wurina, dukanku masu gajiya da waɗanda aka nawaya wa kaya, ni kuwa zan ba ku hutawa. 29Ku ɗauki karkiyata a kanku, ku kuma yi koyo daga wurina, gama ni mai sauƙin hali ne, mai tawali'u kuma a zuciya, za ku kuwa sami hutawa ga rayukanku. 30Gama karkiyata mai sauƙi ce, kayana kuma marar nauyi ne.”