Elihu Ya Sāke Yin Magana
Elihu ya kafa hujja cewa zunubin ɗan adam da nagartarsa ba sa canja kome ga Allah, wanda ya fi gizagizai tsawo; a kan wasu mutane suke faɗawa. Waɗanda aka zalunta sukan yi kuka, amma ba wanda yake tambaya ina Mahaliccinsu yake, wanda yake ba da waƙoƙi da dare. Saboda haka Ayuba yana yawaita magana ba tare da sani ba.
35 1Sai Elihu ya ci gaba da magana, ya ce, 2“Kana zaton wannan daidai ne? Ka ce, ‘Adalcina ya fi na Allah.’ 3Gama kana tambaya, ‘Wane amfani yake yi maka? Me zan amfana in ban yi zunubi ba?’ 4Zan amsa maka, kai da abokanka tare da kai. 5Ka ɗaga ido ka dubi sammai, ka gani; ka zura ido ga gizagizai, waɗanda suka fi ka tsayi. 6In ka yi zunubi, me ka cim ma shi? In kuwa tawayenka sun yi yawa, me kake yi masa? 7In kai mai adalci ne, me ka ba shi? Ko me yake karɓa daga hannunka? 8Muguntarka takan shafi mutum kamarka kaɗai, adalcinka kuwa yakan shafi ɗan'adam kamarka kaɗai. 9Mutane suna kuka saboda nauyin danniya mai yawa; suna kira don a taimake su daga hannun masu iko. 10Amma babu wanda yake cewa, ‘Ina Allah Mahaliccina, wanda yake ba da waƙoƙi da dare, 11wanda yake koya mana fiye da dabbobin ƙasa, ya kuma sa mu fi tsuntsayen sama hikima?’ 12A can suna kuka, amma ba ya ba da amsa, saboda girman kan mugayen mutane. 13Lalle Allah ba ya sauraron kukan banza; Maɗaukaki ba ya kula da shi ko kaɗan. 14Balle fa yă amsa, sa'ad da kake cewa ba ka ganin shi—ko da yake ƙararka tana gabansa, dole ka jira shi. 15Yanzu kuwa, domin fushinsa bai hukunta ba tukuna, bai kuwa kula sosai da wauta ba. 16Ayuba ya buɗe bakinsa da surutun banza; yana yawaita kalmomi babu sani.”