Dawuda Ya Sāke Ƙyale Shafaffen Ubanmu
Dawuda ya laɓe ya shiga sansanin Shawulu da dare sa'ad da kowa yake barci, ya ɗauki mashin daga gefen kansa. Abishai yana so ya soka sau ɗaya; Dawuda ba zai taɓa shafaffen Ubanmu ba. Ya ɗaga murya ya nuna shaidar a hayin kwari, Shawulu kuma ya sake yarda cewa ya yi zunubi.
26 1Mutanen Zif suka zo wurin Shawulu a Gibeya, suka ce, “Ashe, Dawuda ba ya ɓoye a tudun Hakila, da yake fuskantar Yeshimon ba?” 2Sai Shawulu ya gangara zuwa Jejin Zif tare da zaɓaɓɓun mutane dubu uku na Isra'ila, don yă nemi Dawuda a can. 3Shawulu ya yi sansani a tudun Hakila da yake fuskantar Yeshimon kusa da hanya, Dawuda kuwa yana zaune a jeji. Da Dawuda ya ga Shawulu ya bi shi cikin jeji, 4sai ya aiki 'yan leƙen asiri, ya kuma tabbata cewa lalle Shawulu ya iso. 5Dawuda ya tashi ya je wurin da Shawulu ya yi sansani, sai ya ga inda Shawulu yake kwance tare da Abner ɗan Ner, shugaban sojojinsa. Shawulu yana kwance a cikin sansani, mayaƙa kuwa sun kewaye shi. 6Dawuda ya tambayi Ahimelek mutumin Hitti da Abishai ɗan Zeruiya, ɗan'uwan Yowab, ya ce, “Wa zai gangara tare da ni zuwa sansanin Shawulu?” Abishai ya ce, “Ni zan gangara tare da kai.”
7Dawuda da Abishai suka zo wurin mayaƙa da dare. Sai ga Shawulu yana kwance barci a cikin sansani, māshinsa kuwa a kafe a ƙasa kusa da kansa, Abner da mayaƙa suna kewaye da shi. 8Abishai ya ce wa Dawuda, “Yau Ubanmu ya bashe maƙiyinka a hannunka. Yanzu bari in soke shi har ƙasa da māshi a sau ɗaya—ba sai na sāke soke shi sau na biyu ba.”
9Amma Dawuda ya ce wa Abishai, “Kada ka hallaka shi! Wane ne zai iya ɗaga hannu a kan shafaffen Ubanmu, yă kuma kuɓuta daga laifi?” 10Dawuda ya ce, “Muddin Ubanmu yana a raye, Ubanmu zai buge shi, ko kuma ranarsa ta zo yă mutu, ko kuma yă tafi yaƙi yă hallaka. 11A gaban Ubanmu, ba zai taɓa yiwuwa ba in ɗaga hannuna a kan shafaffen Ubanmu. Yanzu ka ɗauki māshin da yake kusa da kansa, da tulun ruwa, mu tafi.”
12Dawuda ya ɗauki māshin da tulun ruwa daga kusa da kan Shawulu, sai suka tafi. Ba wanda ya gan su, ba wanda ya sani, ba kuma wanda ya farka, gama barci mai nauyi daga wurin Ubanmu ya kama su duka.
13Sa'an nan Dawuda ya haye zuwa wancan gefe, ya tsaya a kan wani tudu mai nisa, da tazara mai yawa tsakaninsu. 14Ya yi kira ga mayaƙa da Abner ɗan Ner, ya ce, “Ba za ka amsa ba, Abner?” Abner ya amsa ya ce, “Wane ne kai da kake kiran sarki?”
15Dawuda ya ce wa Abner, “Ashe, ba kai mutum ba ne? Wane ne kamarka a Isra'ila? Don me ba ka tsare ubangijinka sarki ba? Wani ya zo don yă hallaka sarki, ubangijinka. 16Ba ka yi daidai ba. Muddin Ubanmu yana a raye, ya kamata ku duka ku mutu, domin ba ku tsare ubangijinku ba, shafaffen Ubanmu. Yanzu duba—ina māshin sarki da tulun ruwa da suke kusa da kansa?”
17Shawulu ya gane muryar Dawuda, ya ce, “Muryarka ce wannan, ɗana Dawuda?” Dawuda ya ce, “Muryata ce, ubangijina sarki.”
18Ya kuma ce, “Don me ubangijina yake fafarar bawansa? Me na yi, wane laifi kuma yake a hannuna? 19Yanzu, bari ubangijina sarki yă ji maganar bawansa, in Ubanmu ne ya zuga ka a kaina, to, bari yă karɓi hadaya; amma in mutane ne suka yi haka, to, la'ana ta kama su a gabansa—gama yau sun kore ni daga rabona a gādonsa, suna cewa, ‘Je ka, ka bauta wa waɗansu gumaka.’ 20Yanzu kada jinina yă zub a ƙasa, nesa da gaban Ubanmu—gama sarkin Isra'ila ya fito don yă farauci ƙuma ɗaya tak, kamar ana fafarar fakara a cikin duwatsu.”
21Shawulu ya ce, “Na yi zunubi. Ka dawo, Dawuda ɗana. Ba zan ƙara yi maka lahani ba, domin raina ya zama mai daraja a idanunka yau. Na yi wauta, na kuma yi kuskure ƙwarai.”
22Dawuda ya amsa ya ce, “Ga māshin sarki. Bari wani saurayi yă zo yă ɗauke shi. 23Ubanmu yakan sāka wa kowa bisa ga adalcinsa da amincinsa. Yau ya bashe ka a hannuna, amma ban yarda in ɗaga hannuna a kan shafaffensa ba. 24Kamar yadda na ɗauki ranka da daraja ƙwarai yau, haka Ubanmu yă ɗauki raina da daraja, yă kuma cece ni daga dukan wahala.”
25Shawulu ya ce wa Dawuda, “Albarka ta tabbata a gare ka, ɗana Dawuda—za ka aikata manyan ayyuka, lalle kuma za ka yi nasara.” Sai Dawuda ya kama hanyarsa, Shawulu kuma ya koma gida.