Ranar Bikin Auren Sarki
Matar tana neman wanda take ƙauna cikin birni mai duhu, ta tambayi masu tsaro, sa'an nan ta same shi, ba za ta sake shi ba sai ta kai shi gidan mahaifiyarta. Sa'an nan wasu muryoyi suna kallon karusar Sulemanu mai tsaro tana zuwa, sarki da kambi a ranar aurensa.
3 1A kan gadona cikin dare na nemi wanda raina yake ƙauna; na neme shi, amma ban same shi ba. 2Yanzu zan tashi in zaga birnin, cikin tituna da danduna; zan nemi wanda raina yake ƙauna. Na neme shi, amma ban same shi ba. 3Masu gadi suka same ni sa'ad da suke zagaye cikin birnin. “Kun ga wanda raina yake ƙauna?” 4Da ƙyar na wuce su sai na sami wanda raina yake ƙauna. Na riƙe shi, ban kuwa bar shi yă tafi ba sai da na kawo shi gidan mahaifiyata, cikin ɗakin wadda ta ɗauki cikina. 5Ina rantsar da ku, ku 'ya'yan Urushalima, da bareyi da matan barewan jeji: kada ku tsokane ko ku tada ƙauna sai sa'ad da ta ga dama.
6Wane ne wannan mai hawowa daga jeji kamar ginshiƙan hayaƙi, mai ƙanshin mur da lubban, da dukan foda masu ƙanshi na ɗan kasuwa? 7Ga shi—keken Sulemanu ne, da jarumai sittin kewaye da shi, daga cikin jaruman Isra'ila, 8dukansu riƙe da takuba, horarru don yaƙi, kowa da takobinsa a gefensa, saboda razanar dare. 9Sarki Sulemanu ya yi wa kansa keke daga itacen Lebanon. 10Ya yi ginshiƙansa da azurfa, bayansa da zinariya, wurin zamansa da shunayya; cikinsa kuwa 'ya'yan Urushalima suka yi masa ado da ƙauna. 11Ku fito, ku 'ya'yan Sihiyona, ku dubi Sarki Sulemanu, sanye da rawanin da mahaifiyarsa ta sa masa a ranar bikin aurensa, a ranar da zuciyarsa ta yi farin ciki.