Tsarin Ubanmu domin Aure
Yesu ya kafa aure a kan yadda Ubanmu ya yi su tun farko, ya karɓi yara waɗanda almajirai suke korarwa, ya kuma ce wa wani saurayi mai kirki, mai arziki, ya sayar da kome. Ya tafi yana baƙin ciki. Abin da ya gagari mutane mai yiwuwa ne a wurin Ubanmu.
19 1Da Yesu ya gama waɗannan kalmomi, sai ya bar Galili ya tafi yankin Yahudiya, a hayin Urdun. 2Taro mai yawa ya bi shi, ya kuma warkar da su a can.
3Farisiyawa suka zo domin su gwada shi, suna tambaya, “Ya halatta mutum yă saki matarsa saboda kowane dalili?”
4Ya amsa ya ce, “Ba ku taɓa karanta cewa Ubanmu, wanda ya halicce su tun farko, ya yi su namiji da mace ba, 5ya kuma ce, ‘Saboda haka mutum zai bar mahaifinsa da mahaifiyarsa yă manne wa matarsa, su biyun kuwa su zama jiki ɗaya’? 6Saboda haka ba sa ƙara zama biyu, sai dai jiki ɗaya. Don haka, kada kowa yă raba abin da Ubanmu ya haɗa.”
7Suka ce masa, “To me ya sa Musa ya umarta cewa mutum yă ba da takardar saki yă kuma sallame ta?”
8Ya ce musu, “Musa ya ba ku dama ku saki matanku saboda taurin zuciyarku ne, amma ba haka yake ba tun farko. 9Ina gaya muku, duk wanda ya saki matarsa—sai dai saboda zina—ya kuma auri wata, yana zina.”
10Almajiran suka ce masa, “In haka yake tsakanin miji da mata, gara kada a yi aure.”
11Ya ce musu, “Ba dukan mutane ne za su iya karɓar wannan magana ba, sai waɗanda aka ba su. 12Akwai bābanni da aka haifa haka tun daga cikin mahaifiyarsu; akwai kuma bābanni da waɗansu suka mai da su haka; akwai kuma bābanni da suka mai da kansu haka saboda Mulkin Ubanmu. Wanda zai iya karɓar wannan, yă karɓa.”
Yesu ya Marabci Ƙananan Yara
13Sa'an nan aka kawo masa ƙananan yara domin yă ɗora musu hannuwansa yă yi addu'a, amma almajiran suka tsawata wa waɗanda suka kawo su.
14Amma Yesu ya ce, “Ku bar ƙananan yara su zo wurina, kada ku hana su, gama Mulkin Ubanmu na irin waɗannan ne.”
15Ya ɗora musu hannuwansa, sa'an nan ya tashi daga wurin.
Abu Ɗaya da Ya Rasa
16Sai wani mutum ya zo wurinsa ya tambaye shi, “Malam, wane abu nagari zan yi domin in sami rai madawwami?”
17Ya ce masa, “Me ya sa kake tambayata game da abin da yake nagari? Guda ɗaya ne kaɗai yake nagari. In kana so ka shiga rai, ka kiyaye dokoki.”
18Sai ya tambaya, “Waɗanne ne?” Yesu ya ce, “Kada ka yi kisankai, kada ka yi zina, kada ka yi sata, kada ka yi shaidar ƙarya, 19ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, ka kuma ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.”
20Saurayin ya ce masa, “Dukan waɗannan na kiyaye su. Me kuma nake rasa?”
21Yesu ya ce masa, “In kana so ka zama cikakke, je, ka sayar da dukiyarka ka ba wa matalauta—za ka kuwa sami dukiya a Sama—sa'an nan ka zo, ka bi ni.”
22Da saurayin ya ji haka, sai ya tafi yana baƙin ciki, domin yana da dukiya mai yawa.
23Yesu ya ce wa almajiransa, “Lalle hakika, ina gaya muku, da ƙyar mai arziki zai shiga Mulkin Ubanmu. 24Ina sāke gaya muku, ya fi sauƙi raƙumi yă shiga ta kafar allura, da mai arziki yă shiga Mulkin Ubanmu.”
25Da almajiran suka ji haka, sai suka yi mamaki ƙwarai, suka ce, “To wa zai iya samun ceto?”
26Yesu ya dube su ya ce, “Ga mutane wannan ba mai yiwuwa ba ne, amma ga Ubanmu kome mai yiwuwa ne.”
27Sa'an nan Bitrus ya ce masa, “Ga shi, mun bar kome mun kuma bi ka. To me za mu samu?”
28Yesu ya ce musu, “Lalle hakika, a lokacin sabuntawa, sa'ad da Ɗan Mutum ya zauna a kan kursiyinsa mai ɗaukaka, ku da kuka bi ni, ku ma za ku zauna a kan kursiyoyi goma sha biyu, kuna shari'ar kabilan Isra'ila goma sha biyu.
29Duk wanda ya bar gidaje ko 'yan'uwa maza ko 'yan'uwa mata ko mahaifi ko mahaifiya ko 'ya'ya ko gonaki saboda sunana, zai sami riɓi ɗari, yă kuma gāji rai madawwami. 30Amma da yawa da suke na farko za su zama na ƙarshe, da yawa kuma da suke na ƙarshe za su zama na farko.”