Yanzu a bugun takarda

Afisawa 4 FHB Father's Heart Bible™

UbaYesuRuhu
Rangwamen 15% a odarku ta farko →
Littafi

Ku Yi Tafiya da Ta Cancanci Kiranku

Haɗin kai ba kamanci ba ne — Ubangiji ɗaya da Uba ɗaya, amma baye-baye sun bambanta, kuma shugabanni suna nan ne domin su shirya kowa, ba domin su yi aikin a maimakonsu ba. Girma yana nufin daina kaɗuwa nan da can. Sa'an nan umarnai na yau da kullum: faɗi gaskiya, yi aiki, lura da bakinka.

Babi na 4.

Saboda haka ni, ɗan sarƙa saboda Ubangiji, ina roƙonku, ku yi tafiya da ta cancanci kiran da aka kira ku da shi, da dukan tawali'u da sanyin hali, da haƙuri, kuna jurewa juna cikin ƙauna, kuna marmarin kiyaye haɗin kai na Ruhu cikin ɗauri na salama. Jiki ɗaya ne, Ruhu kuma ɗaya, kamar yadda aka kira ku ga bege ɗaya da yake tare da kiranku. Ubangiji ɗaya, bangaskiya ɗaya, baftisma ɗaya, Uba ɗaya na kowa da kowa, wanda yake bisa kowa, da ta wurin kowa, da kuma cikin kowa.

Amma kowannenmu an ba shi alheri gwargwadon ma'aunin baiwar Almasihu. Saboda haka Nassi ya ce, “Da ya hau sama, ya kwaso bayi, ya kuma ba mutane kyautai.” a a v8 Bulus yana ambaton Zabura 68:18, zabura ta nasara da take yabon sarki mai cin nasara. Yana danganta ta ga hawan Almasihu zuwa sama bayan mutuwarsa da tashinsa daga matattu.

To, “ya hau”—mene ne wannan yake nufi, in ba cewa ya kuma sauka zuwa ƙananan sassa, wato ƙasa ba? Wannan da ya sauka, shi ne wanda ya hau can bisa dukan sammai, domin yă cika dukan abubuwa.

Shi ne kuma ya ba da manzanni, da annabawa, da masu bishara, da fastoci da malamai, domin su shirya tsarkaka saboda aikin hidima, domin gina jikin Almasihu, har sai dukanmu mu kai ga haɗin kai cikin bangaskiya da sanin Ɗan Ubanmu, mu zama cikakken balagagge, bisa ga cikakken ma'aunin tsayin daka da cikar Almasihu. Saboda haka ba za mu ƙara zama jarirai ba, waɗanda raƙuman ruwa suke ɗagawa, kowace iskar koyarwa kuma take kai-kawowa, ta wurin wayon mutane, da makircin dabaru na yaudara. Maimakon haka, ta wurin faɗar gaskiya cikin ƙauna, bari mu yi girma a kowace hanya zuwa gare shi wanda yake kai, wato Almasihu. Daga gare shi dukan jiki, haɗe kuma riƙe tare ta wurin kowace jijiya mai taimako, yana girma yayinda kowane sashe yake aiki yadda ya kamata, har jiki yă gina kansa cikin ƙauna.

Ku Yafa Sabon Hali

Saboda haka ina faɗar wannan, ina kuma ba da shaida cikin Ubangiji, kada ku ƙara rayuwa kamar al'ummai, cikin wofin tunaninsu. An duhunta musu fahimta, an kuma raba su da ran Ubanmu saboda jahilcin da yake cikinsu da taurin zukatansu. Da suka rasa dukan ji, sai suka ba da kansu ga biyan sha'awar jiki, suna aikata kowace ƙazanta da haɗama. Amma ba haka kuka koyi Almasihu ba, in dai kun ji labarinsa, aka kuma koyar da ku cikinsa, kamar yadda gaskiya take cikin Yesu, ku tuɓe tsohon halinku, wanda yake haɗe da tsohuwar rayuwarku, wanda kuma sha'awace-sha'awa na ruɗu suka ɓata, a kuma sabunta ku cikin ruhun tunaninku, ku kuma yafa sabon hali, wanda aka halitta kamar Ubanmu cikin adalci na gaskiya da tsarki.

Saboda haka ku kawar da ƙarya—kowannenku yă faɗi gaskiya da maƙwabcinsa, gama mu gaɓoɓin juna ne. Ku yi fushi, amma kada ku yi zunubi; kada rana tă faɗi kuna cikin fushinku, kada kuma ku ba Iblis zarafi. Dole ɓarawo yă daina sata; a maimako, yă yi aiki tuƙuru da hannuwansa, yana aikata abu mai kyau, domin yă sami abin da zai raba wa mabukata. Kada wata muguwar magana tă fito daga bakinku, sai dai abin da yake taimakon waɗansu su yi girma, wanda ya dace da lokaci, domin yă ba masu ji alheri. Kada ku ɓata wa Ruhu Mai Tsarki na Ubanmu rai, wanda ya hatimce ku saboda ranar fansa. Ku kawar da dukan ɗacin rai, da hasala, da fushi, da ihu, da ɓata suna, tare da dukan ƙeta. Ku yi wa juna alheri, masu tausayin zuciya, kuna gafarta wa juna, kamar yadda Ubanmu ya gafarta muku ta wurin Almasihu.