Ubanmu ya Amsa Hezekiya a cikin Baƙin Ciki
Hezekiya ya ɗauki wasiƙar barazanar zuwa gidan Ubanmu ya shimfiɗa ta a gabansa. Ishaya ya amsa cewa Mai Tsarki na Isra'ila ya ji ba'ar, kuma zai mayar da Sennakerib gida da ƙugiya da linzami. A daren nan aka bugi sansanin; Sennakerib ya mutu a gida.
19 1Da Sarki Hezekiya ya ji haka, sai ya yayyage tufafinsa, ya sa rigar makoki, ya shiga gidan Ubanmu. 2Ya aiki Eliyakim shugaban fada, da Shebna marubuci, da manyan firistoci, dukansu saye da tufafin makoki, zuwa wurin annabi Ishaya ɗan Amoz. 3Suka ce masa, “Hezekiya ya ce, Yau rana ce ta wahala, da tsawa, da kunya; yara sun kai lokacin haihuwa, amma babu ƙarfin a haife su. 4Wataƙila Ubanka zai ji dukan kalmomin shugaban sojoji, wanda maigidansa sarkin Assuriya ya aika domin yă zagi Uba mai rai, Ubanka kuma zai hukunta kalmomin da ya ji. Saboda haka ka yi addu'a domin raguwar da ta rage.”
5Da bayin Sarki Hezekiya suka zo wurin Ishaya,
6Ishaya ya ce musu, “Ku gaya wa maigidanku, Ubanmu ya ce, Kada ka ji tsoron kalmomin da ka ji, waɗanda bayin sarkin Assuriya suka zage ni da su. 7Ga shi, zan sa wani ruhu a cikinsa: zai ji wani labari, yă koma ƙasarsa, a can kuma zan sa a kashe shi da takobi.”
8Da shugaban sojoji ya ji sarkin Assuriya ya bar Lakish, sai ya janye, ya same shi yana yaƙi da Libna. 9Sarkin kuwa ya ji labarin Tirhaka sarkin Kush, cewa, “Ga shi, ya fito domin yă yaƙe ka.” Saboda haka ya sāke aika manzanni wurin Hezekiya, 10“Ku gaya wa Hezekiya sarkin Yahuda, Kada Allahnka wanda ka dogara gare shi yă ruɗe ka ta wurin yin alkawari cewa ba za a ba da Urushalima ga sarkin Assuriya ba. 11Ga shi, ka ji abin da sarakunan Assuriya suka yi wa kowace ƙasa, yadda suka hallaka su ƙaƙaf. Kai fa, za a cece ka? 12Allolin al'umman da kakannina suka hallaka sun cece su ne—Gozan, da Haran, da Rezef, da mutanen Eden da suke a Telassar? 13Ina sarkin Hamat, da sarkin Arfad, da sarkin birnin Sefarbayim, da na Hena, da na Iffa?”
Hezekiya ya Shimfiɗa Shi a Gaban Uba
14Hezekiya ya karɓi wasiƙar daga hannun manzannin, ya karanta ta. Sa'an nan ya haura zuwa gidan Ubanmu, ya shimfiɗa ta a gabansa. 15Hezekiya ya yi addu'a a gaban Ubanmu, ya ce, “Ya Allah na Isra'ila, wanda yake zaune bisa kerubobi, kai kaɗai ne Allah bisa dukan mulkokin duniya; kai ka yi sammai da ƙasa. 16Ka saurara, ya Ubanmu, ka kuma ji; ka buɗe idanunka ka gani. Ka ji kalmomin Sennakerib da ya aika domin yă zagi Uba mai rai. 17Hakika, ya Ubanmu, sarakunan Assuriya sun hallaka al'ummai da ƙasashensu, 18suka kuma jefa allolinsu cikin wuta; gama ba alloli ba ne, sai dai aikin hannun mutum, itace da dutse. Saboda haka suka hallaka su. 19Yanzu kuwa, ya Ubanmu, ka cece mu daga hannunsa, domin dukan mulkokin duniya su san kai kaɗai ne Allah.”
Ubanmu ya Ƙasƙantar da Girman Kan Sennakerib
20Ishaya ɗan Amoz ya aika wa Hezekiya cewa, “Ga abin da Ubanmu, Allah na Isra'ila, ya ce, Na ji addu'ar da ka yi mini game da Sennakerib sarkin Assuriya. 21Ga abin da Ubanmu ya ce game da shi, Budurwa Diyar Sihiyona ta rena ka, ta kuma yi maka ba'a; Diyar Urushalima ta kaɗa kai a bayanka. 22Wa ka yi wa ba'a, ka kuma saɓa wa? A kan wa ka ɗaga muryarka, ka kuma ɗaga idanunka da girman kai? A kan Mai Tsarki na Isra'ila ne! 23Ta wurin manzanninka ka yi wa Uba Maɗaukaki ba'a, ka kuma ce, Da yawan karusaina na hau kan tsaunukan dutse, can cikin zurfin Lebanon. Na sare manyan itatuwan al'ul nasa, zaɓaɓɓun itatuwan fir nasa. Na kai can tsayinsa mafi nisa, da kurminsa mafi kauri. 24Na haƙa rijiyoyi, na kuma sha ruwan baƙi; da tafin ƙafafuna na busar da dukan rafuffukan Masar. 25Ba ka ji ba? Tun da daɗewa na yi shi; tun zamanin dā na shirya shi. Yanzu kuwa na sa ya faru, domin ka mai da birane masu katanga tsibbai na kufai. 26Mazaunansu, waɗanda aka raba da ƙarfi, suka karaya suka kuma ji kunya. Sun zama kamar tsire-tsiren jeji, kamar ɗanyun toho kore, kamar ciyawar da ta tsiro a kan rufin bene, wadda ta ƙeƙashe kafin ta yi girma. 27Amma na san zamanka, da fitarka, da shigarka, da kuma fushinka a kaina. 28Saboda fushinka a kaina da kuma girman kanka wanda ya kai kunnuwana, zan sa ƙugiyata a hancinka da linzamina a leɓunanka, zan kuma mai da kai ta hanyar da ka zo.
29Wannan ita ce alamarka, Hezekiya, A wannan shekara za ka ci abin da ya tsiro da kansa, shekara mai zuwa kuma abin da ya tsiro daga gare shi; a shekara ta uku kuwa, ka yi shuka ka yi girbi, ka dasa gonakin inabi, ka kuma ci 'ya'yansu. 30Sauran gidan Yahuda da suka ragu za su sāke yin saiwa a ƙasa, su kuma ba da 'ya'ya a bisa. 31Gama daga Urushalima za a sami raguwa, daga kuma Dutsen Sihiyona rukunin waɗanda suka tsira. Kishin Uba na rundunonin sama zai aikata wannan.
32‘Saboda haka ga abin da Ubanmu ya ce game da sarkin Assuriya, Ba zai shiga wannan birni ba, ba kuwa zai harba kibiya a nan ba, ba zai fuskance shi da garkuwa ba, ba kuwa zai gina tudun yaƙi gāba da shi ba. 33Ta hanyar da ya zo, zai komo; ba zai shiga wannan birni ba, in ji Ubanmu. 34Zan kāre wannan birni in kuma cece shi, saboda kaina da kuma saboda bawana Dawuda.’”
35A daren nan sai mala'ikan Ubanmu ya fito, ya karkashe dubu ɗari da tamanin da biyar a sansanin Assuriyawa. Da gari ya waye, sa'ad da suka tashi—sai ga dukan gawawwaki a kwance. 36Saboda haka Sennakerib sarkin Assuriya ya tashi ya tafi. Ya koma Ninawa, ya zauna a can. 37Yana cikin sujada a haikalin allahnsa Nisrok, sai 'ya'yansa maza Adrammelek da Sharezer suka kashe shi da takobi, suka gudu zuwa Ararat. Ɗansa Esar-Haddon ya gāje shi.