Ataliya Ta Ƙwace Sarauta
Ataliya ta karkashe gidan sarauta, amma aka ɓoye jariri guda a gidan Ubanmu har shekara shida. Firist Yehoyada ya ba masu tsaro makamai, ya naɗa yaron sarki, ya kuma sa aka kashe sarauniyar a bayan wuri mai tsarki. Aka rushe haikalin Ba'al, ɗan shekara bakwai kuwa ya hau gadon sarauta.
11 1Da Ataliya, mahaifiyar Ahaziya, ta ga ɗanta ya mutu, sai ta kama hanya domin ta hallaka dukan iyalin sarauta. 2Amma Yehosheba, 'yar Sarki Yoram kuma 'yar'uwar Ahaziya, ta ɗauki Yowash ɗan Ahaziya, ta sace shi daga cikin 'ya'yan sarki waɗanda za a kashe. Ta ɓoye shi da uwar renonsa a ɗakin kwana, nesa da Ataliya, don kada a kashe shi. 3Ya kuwa kasance a ɓoye tare da ita a gidan Ubanmu shekara shida, Ataliya kuwa tana mulkin ƙasar.
Uba Ya Kiyaye Sarki Na Gaskiya
4A shekara ta bakwai Yehoyada ya aika a kira shugabannin ɗari-ɗari, na Kariyawa da na masu gadi, ya kawo su wurinsa a gidan Ubanmu. Ya yi alkawari da su, ya rantsar da su a gidan Ubanmu, ya kuma nuna musu ɗan sarki. 5Ya umarce su, “Ku yi haka, kashi ɗaya bisa uku naku da suke shigowa aiki ran Asabar za su yi gadin fadar sarki, 6kashi ɗaya kuma a Ƙofar Sur, kashi ɗaya kuma a ƙofar da take bayan masu gadi; ku yi ta sauya wa juna gadin fada. 7Sauran ɓangarorinku biyu da suke fita daga aiki ran Asabar dole su yi gadin gidan Ubanmu saboda sarki. 8Ku kewaye sarki a kowane gefe, kowane mutum da makamansa a hannunsa; duk wanda ya matso kusa da sahu, sai ku kashe shi. Ku kasance tare da sarki duk inda ya tafi.”
9Shugabannin ɗari-ɗari suka yi dukan abin da Yehoyada firist ya umarta. Kowanne ya ɗauki mutanensa—waɗanda suke shigowa aiki ran Asabar da waɗanda suke fita—suka zo wurin Yehoyada firist. 10Firist ɗin ya ba shugabannin ɗari-ɗari māsu da garkuwoyin Sarki Dawuda, waɗanda aka ajiye a gidan Ubanmu. 11Masu gadi suka tsaya kewaye da sarki, kowane mutum da makaminsa a hannunsa, daga gefen kudu na haikali har zuwa gefen arewa, kusa da bagaden da haikalin. 12Yehoyada ya fito da ɗan sarki, ya sa masa kambi, ya kuma ba shi shaidar. Suka naɗa shi sarki, suka shafe shi da mai, mutane kuwa suka tafa hannuwansu suka yi ihu suna cewa, “Ran sarki yă daɗe!”
13Da Ataliya ta ji ƙarar masu gadi da mutane, sai ta tafi wurin mutane a gidan Ubanmu. 14Ta duba—sai ga sarki tsaye kusa da ginshiƙi yadda al'ada ta bukata, shugabanni da masu busa ƙaho kuwa suna gefensa, dukan mutanen ƙasar suna farin ciki suna busa ƙaho. Ataliya ta yage tufafinta, tana ihu, “Cin amana! Cin amana!”
15Yehoyada firist ya umarci shugabannin ɗari-ɗari waɗanda suke bisa rundunar, “Ku fitar da ita ta tsakar sahu; duk wanda ya bi ta, sai ku kashe shi da takobi.” Domin firist ɗin ya riga ya ce kada a kashe ta a gidan Ubanmu. 16Sai suka kama ta, ta kuwa tafi ta mashigar dawakai zuwa fada, a can kuwa aka kashe ta.
17Sa'an nan Yehoyada ya yi alkawari tsakanin Ubanmu da sarki da mutane, cewa za su zama mutanen Ubanmu; ya kuma yi alkawari tsakanin sarki da mutane. 18Dukan mutanen ƙasar suka tafi haikalin Ba'al suka rushe shi. Suka farfashe bagadansa da gumakansa, suka kuma kashe Mattan, firist na Ba'al, a gaban bagadan. Sa'an nan firist ɗin ya sa masu gadi a gidan Ubanmu. 19Ya ɗauki shugabannin ɗari-ɗari, da Kariyawa, da masu gadi, da dukan mutanen ƙasar, suka gangarar da sarki daga gidan Ubanmu ta ƙofar masu gadi zuwa fadar sarki, a can kuwa ya zauna a kan kujerar sarautar sarakuna. 20Dukan mutanen ƙasar suka yi farin ciki, birnin kuwa ya natsu, da yake an kashe Ataliya da takobi a fadar sarki.
21Yowash yana da shekara bakwai sa'ad da ya zama sarki.