Yowash Ya Gyara Gidan Uba
Yowash ya umarta a gyara gidan Ubanmu, amma ba abin da ya faru har shekara ashirin da uku, don haka aka ajiye akwati mai rami a murfinsa kusa da bagade, kuɗin kuwa ya tafi kai tsaye ga ma'aikata, waɗanda suka zama masu gaskiya. Daga baya Yowash ya ba Hazayel toshiyar baki, shugabanninsa kuwa suka kashe shi.
12 1A shekara ta bakwai ta Yehu, Yehowash ya zama sarki; ya yi mulki shekara arba'in a Urushalima. Mahaifiyarsa ita ce Zibiya ta Beyer-sheba. 2Yehowash ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubanmu a dukan shekarun da Yehoyada firist ya koyar da shi. 3Duk da haka, wuraren sujada na kan tudu suka ci gaba da kasancewa; mutane suka ci gaba da yin hadaya da ƙona turare a can.
4Yehowash ya ce wa firistoci, “Dukan kuɗin kyautai masu tsarki da ake kawowa cikin gidan Ubanmu—kuɗin ƙidaya, da darajar da aka ƙididdige wa kowane mutum, da dukan kuɗin da zuciyar kowa ta motsa shi yă kawo cikin gidan Ubanmu, 5firistoci su karɓe shi, kowanne daga wurin ma'ajinsa, su kuma gyara duk wata barnar da aka samu a haikali.”
6Amma har zuwa shekara ta ashirin da uku ta Sarki Yehowash, firistoci ba su gyara barnar haikali ba tukuna. 7Sai Sarki Yehowash ya kirawo Yehoyada firist da sauran firistoci, ya ce, “Me ya sa ba kwa gyara barnar haikali? To, kada ku ƙara karɓar kuɗi daga wurin ma'ajanku—ku ba da shi domin gyare-gyare.”
8Firistoci suka yarda cewa ba za su ƙara karɓar kuɗi daga mutane ba, ba kuma za su gyara haikali da kansu ba. 9Sai Yehoyada firist ya ɗauki wani akwati, ya huda rami a murfinsa, ya kuma ajiye shi kusa da bagade, a hannun dama yayinda ake shiga gidan Ubanmu. A can firistoci masu tsaron bakin ƙofa suka riƙa sa dukan kuɗin da ake kawowa cikin gidan Ubanmu. 10Duk sa'ad da suka ga akwai kuɗi mai yawa a cikin akwatin, sai magatakardan sarki da babban firist su hau, su ƙidaya shi, su kuma sa kuɗin da aka samu a gidan Ubanmu cikin jakuna. 11Suka ba da kuɗin da aka auna ga ma'aikatan da suke kula da gidan Ubanmu, waɗanda suka biya masassaƙa da magina da suke aiki a gidan Ubanmu, 12da magina da masu sassaƙa duwatsu, don sayen katako da sassaƙaƙƙun duwatsu domin gyara barnar gidan Ubanmu, da duk abin da aka kashe a kan gyaransa. 13Ba a yi amfani da kuɗin da ake kawowa cikin gidan Ubanmu domin yin kwanonin azurfa, ko almakasan fitila, ko kwanonin yayyafawa, ko ƙahoni, ko wani abu na zinariya ko na azurfa ba; 14an ba da shi ne ga ma'aikata, waɗanda suka yi amfani da shi domin gyara gidan Ubanmu. 15Ba su nemi lissafi daga mutanen da aka ba su kuɗin domin su biya ma'aikata ba, gama sun yi aiki da aminci. 16Kuɗin da ya fito daga hadaya ta laifi da hadaya ta zunubi bai shiga gidan Ubanmu ba; na firistoci ne.
Fāɗuwar Yowash
17Sa'an nan Hazayel sarkin Aram ya kai wa Gat hari, ya kuma kame ta, sa'an nan ya kama hanya domin yă kai wa Urushalima hari. 18Amma Yehowash sarkin Yahuda ya ɗauki dukan kyautai masu tsarki da kakanninsa Yehoshafat, da Yehoram, da Ahaziya, sarakunan Yahuda, suka keɓe, tare da nasa, da dukan zinariyar da take cikin ɗakunan ajiya na gidan Ubanmu da na fadar sarki, ya kuma aika da su wurin Hazayel sarkin Aram. Saboda haka Hazayel ya janye daga Urushalima.
19Sauran ayyukan Yowash, da duk abin da ya yi—ba a rubuce suke a cikin Littafin Tarihin Sarakunan Yahuda ba? 20Fadawansa suka ƙulla maƙarƙashiya, suka kuma kashe Yowash a Bet-Millo, a kan hanyar da ta gangara zuwa Silla. 21Fadawansa Yozabad ɗan Shimeyat da Yehozabad ɗan Shomer suka buge shi suka kashe shi. Suka binne shi tare da kakanninsa a Birnin Dawuda, sai ɗansa Amaziya ya ci sarauta a maimakonsa.