Wani Mutum mai Igiyar Awo
Wani mai awo ya tashi don ya auna Urushalima, aka ce masa kada ya damu — birnin zai cika ya zarce kowane garu. Ubanmu da kansa zai zama garun wuta kewaye da ita da ɗaukaka a cikinta, al'ummai da yawa kuma za su haɗa kai da shi su zama 'ya'yansa.
2 1Sai na ɗaga kai, sai na ga wani mutum riƙe da igiyar awo a hannunsa. 2Na tambaya, “Ina za ka?” Ya ce mini, “Zan auna Urushalima, don in ga faɗinta da tsawonta.”
3Sai mala'ikan da yake magana da ni ya tafi, wani mala'ika kuma ya fito yă tarye shi, 4ya ce masa, “Yi gudu, ka gaya wa saurayin nan, ‘Urushalima za ta zauna kamar ƙauye mai faɗi, saboda yawan mutane da dabbobi a cikinta.’
5Ni kaina zan zama katangar wuta kewaye da ita, in ji Ubanmu, zan kuma zama ɗaukaka a cikinta.’”
6“Ku zo! Ku zo! Ku gudu daga ƙasar arewa, in ji Ubanmu, gama na watsar da ku kamar iskoki huɗu na sama, in ji Ubanmu. 7Ku zo, Sihiyona! Ku tsere, ku da kuke zama tare da 'yar Babila.
8Ga abin da Uban rundunonin sama ya ce — bayan ɗaukakarsa ta aiko ni gāba da al'umman da suka washe ku, duk wanda ya taɓa ku, ya taɓa ƙwayar idonsa ne.
9Gama ga shi, zan kaɗa hannuna a kansu, za su kuma zama ganima ga waɗanda suka bauta musu. Sa'an nan za ku san cewa Uban rundunonin sama ya aiko ni.
10Ki yi waƙa ki yi murna, 'yar Sihiyona! Gama ga shi, ina zuwa in zauna a cikinki, in ji Ubanmu.
11“Al'ummai da yawa za su haɗu da Ubanmu a ranar, su kuma zama 'ya'yana. Zan zauna a cikinku, za ku kuma san cewa Uban rundunonin sama ya aiko ni gare ku. 12Ubanmu kuma zai ɗauki Yahuda kamar rabonsa a ƙasa mai tsarki, yă kuma sāke zaɓen Urushalima.
13Ku yi shiru, dukan 'yan adam, a gaban Ubanmu, gama ya tashi daga mazauninsa mai tsarki.”