Ku Komo Wurina
Wahayoyin maidowa ga waɗanda suka dawo daga bauta, suna nuna gaba ga Sarki mai zuwa wanda zai shigo da tawali'u a kan jaki. Alkawuransa suna kewaye da maimaitaccen furucin alkawari ɗaya: za su zama mutanena, ni kuma Ubansu.
1 1A shekara ta biyu ta mulkin Dariyus, a wata na takwas, maganar Ubanmu ta zo wa Zakariya ɗan Berekiya, ɗan Iddo annabi, cewa: 2Ubanmu ya yi fushi ƙwarai da kakanninku.
3Saboda haka ka gaya musu, Ga abin da Uba na rundunonin sama yake cewa: Ku komo wurina, in ji Uba na rundunonin sama, ni kuwa zan komo wurinku. In ji Uba na rundunonin sama. 4Kada ku zama kamar kakanninku. Annabawan dā suka yi musu shela, cewa: Ga abin da Uba na rundunonin sama yake cewa: Ku juyo yanzu daga mugayen hanyoyinku da mugayen ayyukanku. Amma ba su saurara ba, ba su kuwa kula da ni ba, in ji Ubanmu.
5Kakanninku, ina suke yanzu? Annabawan kuma, suna raye har abada ne?
6Amma maganata da ƙa'idodina, waɗanda na umarci bayina annabawa, ashe, ba su cim ma kakanninku ba? Sai suka juyo suka ce, “Kamar yadda Uba na rundunonin sama ya shirya ya yi mana, gwargwadon hanyoyinmu da ayyukanmu, haka ya yi da mu.”
Uba Ya Aiki Mahayansa
7A rana ta ashirin da huɗu ga wata na goma sha ɗaya, wato watan Shebat, a shekara ta biyu ta mulkin Dariyus, maganar Ubanmu ta zo wa Zakariya ɗan Berekiya, ɗan Iddo annabi, cewa: 8Da dare na ga wahayi, sai ga wani mutum a gabana yana a kan jan doki, tsaye a cikin itatuwan margo da suke cikin wani kwari, a bayansa kuwa akwai dawakai jajaye, da ruwan ƙasa, da farare. 9Na tambaya, na ce, “Mene ne waɗannan, ranka ya daɗe?” Sai mala'ikan da yake magana da ni ya ce, “Zan nuna maka abin da suke.”
10Mutumin da yake cikin itatuwan margo ya amsa ya ce, “Waɗannan su ne waɗanda Ubanmu ya aika domin su zaga duniya.”
11Sai suka kawo rahoto ga mala'ikin Ubanmu da yake tsaye cikin itatuwan margo, suka ce, “Mun zaga duniya, ga shi dukan duniya tana zaune lafiya da salama.”
12Sai mala'ikin Ubanmu ya ce, “Ya Uba na rundunonin sama, har yaushe za ka hana wa Urushalima da biranen Yahuda jinƙai, kana fushi da su shekaru saba'in nan?”
13Sai Ubanmu ya yi magana da mala'ikan da yake magana da ni, da kalmomi masu daɗi masu ta'aziyya.
14Sai mala'ikan da yake magana da ni ya ce mini, “Ka yi shela cewa: Ga abin da Uba na rundunonin sama yake cewa: Ina matuƙar kishin Urushalima da Sihiyona,” 15amma ina fushi ƙwarai da al'umman da suke zaman natsuwa; na yi fushi kaɗan ne kawai, amma su kuwa suka ƙara kawo masifa. 16Saboda haka Ubanmu ya ce: Zan komo Urushalima da jinƙai; a can za a sāke gina gidana, in ji Uba na rundunonin sama, za a kuma miƙa igiyar aunawa a kan Urushalima.
17Ka ƙara yin shela cewa: In ji Uba na rundunonin sama: Biranena za su sāke yalwata da wadata; Ubanmu kuma zai sāke yi wa Sihiyona ta'aziyya, zai kuma sāke zaɓen Urushalima.
Ƙahoni da Maƙera
18Sa'an nan na ɗaga ido, sai ga ƙahoni huɗu a gabana. 19Sai na tambayi mala'ikan da yake magana da ni, na ce, “Mene ne waɗannan?” Ya ce, “Waɗannan su ne ƙahonin da suka watsar da Yahuda, da Isra'ila, da Urushalima.”
20Sa'an nan Ubanmu ya nuna mini maƙera huɗu. 21Na tambaya, na ce, “Me waɗannan suke zuwa su yi?” Ya ce, “Waɗannan ƙahoni ne suka watsar da Yahuda har ba wanda ya iya ɗaga kansa; amma waɗannan maƙera sun zo domin su firgita su, su kuma kā da ƙahonin da al'ummai suka ɗaga gāba da ƙasar Yahuda domin su watsar da ita.”