Ɗan Rago da Mutum Dubu Ɗari da Arba'in da Huɗu
Ɗan Rago yana tsaye a kan Sihiyona tare da mutum 144,000 da aka yi wa alama da sunan Ubansa, waɗanda suka san waƙar da ba wani kuma da zai iya koyo. Mala'iku uku suna tashi a sama: labari mai daɗi ga kowace al'umma, faɗuwar Babila, gargaɗi ga masu yi wa dabbar sujada. Sa'an nan aka girbe duniya aka kuma tattake inabin.
14 1Na ga Ɗan Rago, Yesu, tsaye a kan Dutsen Sihiyona, tare da mutum dubu ɗari da arba'in da huɗu waɗanda suke da sunansa da sunan Ubansa a rubuce a goshinsu. 2Na ji wata murya daga Sama kamar rurin ruwaye masu yawa da kuma kamar tsawa mai ƙarfi, muryar da na ji kuwa tana kama da masu garaya suna kaɗa garayunsu. 3Suka rera sabuwar waƙa a gaban kursiyin, da halittu huɗu masu rai, da dattawa; sai mutum dubu ɗari da arba'in da huɗu kaɗai, waɗanda aka fanshe daga duniya, suka iya koyonta. 4Waɗannan su ne waɗanda ba su ƙazantu da mata ba, gama budurwai ne. Suna bin Yesu, Ɗan Rago, duk inda ya tafi; an saye su daga cikin 'yan adam, su ne nunan fari ga Ubanmu da kuma Ɗan Rago, 5ba a kuwa sami ƙarya a bakunansu ba; marasa aibu ne su.
Bisharar Madawwami Ta Fita
6Na ga wani mala'ika yana tashi sama a tsakiyar sararin sama, yana riƙe da bisharar madawwami domin yă yi shelarta ga mazaunan duniya—ga kowace al'umma, da kabila, da harshe, da mutane. 7Ya ɗaga murya da ƙarfi yana cewa, “Ku ji tsoron Ubanmu, ku kuma ɗaukaka shi, gama sa'ar hukuncinsa ta zo. Ku yi wa Mahaliccin Sama, da ƙasa, da teku, da maɓulɓulan ruwa sujada.”
8Mala'ika na biyu ya biyo baya yana cewa, “Ta fāɗi, ta fāɗi, Babila mai girma, wadda ta sa dukan al'ummai suka sha ruwan inabin sha'awar fasikancinta.”
9Mala'ika na uku kuma ya biyo baya, yana ihu da ƙarfi yana cewa, “Duk wanda ya yi wa dabbar nan da siffarta sujada, ya kuma karɓi alama a goshinsa ko a hannunsa, 10shi ma zai sha ruwan inabin fushin Ubanmu, wanda aka zuba shi babu garwaya a cikin kwaf na hasalarsa, za a kuma ba shi azaba da wuta da farar wuta a gaban mala'iku masu tsarki da kuma a gaban Ɗan Rago. 11Hayaƙin azabarsu yana hawa sama har abada abadin; babu hutu dare da rana ga waɗanda suke yi wa dabbar da siffarta sujada, ko kuwa suke karɓar alamar sunanta.”
12A nan ne haƙurin tsarkaka yake: waɗanda suke kiyaye umarnan Ubanmu suke kuma riƙe da bangaskiyarsu ga Yesu.
13Na ji wata murya daga Sama tana cewa, “Ka rubuta, Masu albarka ne matattu waɗanda suke mutuwa cikin Ubangiji daga yanzu.” “I,” in ji Ruhu Mai Tsarki, “za su huta daga aikinsu, gama ayyukansu suna binsu.”
Wani Mai Kama da Ɗan Mutum
14Na duba, sai ga wani farin girgije, a kansa kuwa ga wani zaune mai kama da ɗan mutum—Yesu—da rawanin zinariya a kansa, da kuma lauje mai kaifi a hannunsa. 15Sai wani mala'ika ya fito daga haikali, yana kira da ƙarfi ga wanda yake zaune a kan girgijen yana cewa, “Ka sa laujenka ka yi girbi; gama sa'ar girbi ta zo, girbin duniya ya nuna sarai.” 16Sai wanda yake a kan girgijen ya kaɗa laujensa a bisa duniya, aka kuwa girbe duniya.
17Sa'an nan wani mala'ika ya fito daga haikalin da yake Sama, shi ma yana da lauje mai kaifi. 18Wani mala'ika kuma, mai iko a kan wuta, ya zo daga bagaden yana kira da ƙarfi ga wanda yake riƙe da lauje mai kaifin nan yana cewa, “Ka sa laujenka mai kaifi ka tara nonon inabi daga kuringar inabin duniya, gama inabinta ya nuna.” 19Mala'ikan ya kakkaɓa laujensa a cikin duniya, ya girbe kuringar inabin duniya, ya kuma jefa shi cikin babban wurin matsar inabi na fushin Ubanmu. 20Aka tattake wurin matsar inabin a bayan birni, jini kuwa ya gudu daga wurin matsar inabin har ya kai bakin linzamin doki, misalin tafiyar mil ɗari da tamanin.