Uba Ya Yi Gargaɗi: Ku Gudu daga Urushalima
Irmiya yana kallon kewayen yaƙi yana matsowa, yana kuma jin shugabanni suna alkawarta salama a kan raunin da ba su yi masa magani ba. Ubanmu ya ba da hanya ɗaya ta tsira: ku tsaya a mararraba, ku tambayi tsohuwar hanya, ku bi ta. Jama'a suka amsa cewa ba za su bi ba. Ya kira su azurfar da aka ƙi.
6 1“Ku gudu don ceton rai, ku 'ya'yan Benyamin, ku fita daga Urushalima! Ku busa ƙaho a Tekowa, ku kuma ɗaga tuta a bisa Bet-hakkerem, gama masifa tana gabatowa daga arewa, babbar hallaka. 2Diyar Sihiyona mai kyau da laushi—zan hallaka ta. 3Makiyaya da garkunansu za su zo su yaƙe ta; za su kafa tentunansu kewaye da ita, kowa yana kiwo a rabonsa.”
4Ku shirya yaƙi da ita! Ku zo, mu kai hari da tsakar rana! Amma kaitonmu, gama rana tana faɗuwa inuwowin yamma kuma suna ƙaruwa da tsawo. 5Ku zo, mu kai hari da dare mu rushe kagarorinta!
6Gama Uban rundunonin Sama ya ce, Ku sare itatuwanta ku kuma gina tudu don ƙawanyar Urushalima. Dole a hukunta birnin nan; babu kome a cikinta sai danniya. 7“Kamar yadda rijiya take kiyaye ruwanta sabo, haka take kiyaye muguntarta sabuwa. Ana jin ƙarar rikici da hallaka a cikinta; cuta da raunuka kullum suna a gabana. 8Ki yi gargaɗi, ya Urushalima, in ba haka ba zan juya baya gare ki da ƙyama in mai da ke kango, ƙasar da ba mai zama a cikinta.”
9Uban rundunonin Sama ya ce, Za su kala raguwar Isra'ila sarai kamar kurangar inabi wadda ake kala. Ka sāke zura hannunka a kan rassan, kamar mai tattara 'ya'yan inabi.
10“Wa zan yi masa magana in gargaɗe shi, da zai saurara? Kunnuwansu a rufe suke, saboda haka ba sa iya ji. Maganar Ubanmu abar ƙyama ce a gare su; ba su jin daɗinta.
11Amma na cika da fushin Ubanmu; na gaji da riƙe shi a ciki. A zuba shi a kan yara a kan tituna, da a kan samari da suka taru; za a kama mai gida da matarsa duka, da tsoho da wanda ya tsufa ƙwarai.” 12Za a mai da gidajensu ga waɗansu, gonakinsu da matansu tare, gama zan miƙa hannuna gāba da mazaunan ƙasar, in ji Ubanmu. 13Gama daga mafi ƙanƙanta har zuwa mafi girma, duk suna kwaɗayin ribar zalunci; daga annabi har zuwa firist, duk suna aikata ha'inci. 14Suna yi wa raunin mutanena magani kamar ba shi da tsanani. Suna cewa, ‘Salama, salama,’ alhali kuwa babu salama. 15Suka ji kunyar aikinsu na banƙyama? A'a, ba su ji kunya ko kaɗan ba; ba su ma san yadda za su ji kunya ba. Saboda haka za su fāɗi tare da waɗanda suka fāɗi; za a kakkaɓe su sa'ad da na hukunta su, in ji Ubanmu.
16Ga abin da Ubanmu ya ce, Ku tsaya a mararraba ku duba; ku nemi hanyoyin dā, inda hanya mai kyau take, ku bi ta, za ku kuwa sami hutawa ga rayukanku. Amma suka ce, ‘Ba za mu bi ta ba.’ 17Na naɗa muku masu gadi na ce, ‘Ku saurari ƙarar ƙaho!’ Amma suka ce, ‘Ba za mu saurara ba.’ 18“Saboda haka ku ji, ya ku al'ummai; ku lura, ya ku shaidu, da abin da zai same su. 19Ki saurara, ya ke duniya: ina kawo masifa a kan mutanen nan, 'ya'yan dabarunsu, domin ba su saurari maganata ba kuma sun ƙi koyarwata. 20Ina ruwana da turaren Sheba ko kayan ƙanshi mai zaƙi daga ƙasa mai nisa? Hadayunku na ƙonawa ba abin karɓa ba ne; hadayunku ba sa faranta mini rai.”
21Saboda haka ga abin da Ubanmu ya ce, Zan sa abubuwan tuntuɓe a gaban mutanen nan. Iyaye da 'ya'ya duka za su yi tuntuɓe a kansu; maƙwabta da abokai za su hallaka.
22Ga abin da Ubanmu ya ce, Duba, ga rundunar soja tana zuwa daga ƙasar arewa; babbar al'umma tana tashi daga iyakar duniya. 23Sun riƙe baka da māshi; su mugaye ne ba sa nuna jinƙai. Ƙararsu tana ruri kamar teku yayinda suke hawan dawakai, a shirye cikin tsarin yaƙi gāba da ke, ya Diyar Sihiyona.
24Mun ji labari a kansu, hannuwanmu kuwa suka yi laushi. Baƙin ciki ya kama mu, zafi kamar na mace mai naƙuda. 25Kada ku fita zuwa gonaki ko ku yi tafiya a kan hanyoyi, gama abokin gāba yana da takobi, razana kuma tana ko'ina. 26Ya Diyar mutanena, ki sa tufafin makoki ki birkiɗa a cikin toka; ki yi makoki da kuka mai zafi kamar don makaɗaicin ɗa, gama farat ɗaya mai hallakarwa zai auko mana.
27“Na mai da kai mai gwajin ƙarafa a cikin mutanena, domin ka lura ka kuma gwada hanyoyinsu. 28Dukansu 'yan tawaye ne masu taurin kai, suna yawo suna baza ƙarairayi. Tagulla ne da baƙin ƙarfe; dukansu suna aikata ɓarna. 29Zugazugi suna hura wuta da ƙarfi don su ƙone darma da wuta, amma tacewar banza ce; ba a cire mugaye ba. 30Ana ce da su azurfa wadda aka ƙi, domin Ubanmu ya ƙi su.”