Ishaku Ya Sāke Albarkata Yaƙub
Da aka sallame shi don ya nemo mata, Yakubu ya kwana a fili da dutse a matsayin matashin kai, ya kuma yi mafarkin matakala cike da mala'iku. Ubanmu ya maimaita alkawarin Ibrahim ga mai gudun hijira, ya kuma yi alkawari zai komo da shi gida. Yakubu ya farka a tsorace, ya yi ciniki.
28 1Sai Ishaku ya kira Yaƙub, ya sa masa albarka, ya kuma umarce shi, “Kada ka auri wata daga cikin 'yan matan Kan'ana. 2Ka tashi ka tafi Faddan-aram, zuwa gidan Betuwel mahaifin mahaifiyarka, ka auro wa kanka mata a can daga cikin 'yan matan Laban ɗan'uwan mahaifiyarka. 3Bari El Shaddai, Ubanka Maɗaukaki, yă sa maka albarka, yă ba ka 'ya'ya masu yawa, yă riɓaɓɓanya ka, har ka zama taron al'ummai. 4Bari yă ba ka albarkar Ibrahim, kai da zuriyarka tare da kai, domin ka gāji ƙasar da kake zaune a cikinta baƙo, wadda Ubanmu ya ba wa Ibrahim.”
5Sai Ishaku ya sallami Yaƙub, ya kuwa tafi Faddan-aram, wurin Laban ɗan Betuwel mutumin Aram, ɗan'uwan Rifkatu mahaifiyar Yaƙub da Isuwa.
6Isuwa ya ji cewa Ishaku ya sa wa Yaƙub albarka ya kuma aike shi Faddan-aram domin yă auro mata daga can, da kuma yadda ya umarce shi sa'ad da yake sa masa albarka cewa, “Kada ka auri mace daga cikin matan Kan'ana,” 7da kuma yadda Yaƙub ya yi biyayya ga mahaifinsa da mahaifiyarsa, ya tafi Faddan-aram. 8Saboda haka Isuwa ya gane cewa 'yan matan Kan'ana ba su gamshi mahaifinsa Ishaku ba. 9Sai Isuwa ya tafi wurin Isma'ila, ya auri Mahalat 'yar Isma'ila ɗan Ibrahim, 'yar'uwar Nebayiwot, ban da sauran matansa.
Hanya Zuwa Haran
10Yaƙub ya bar Biyer-sheba, ya kama hanya zuwa Haran. 11Da ya kai wani wuri, sai ya kwana a can, gama rana ta faɗi. Ya ɗauki ɗaya daga cikin duwatsun wurin, ya sanya shi a ƙarƙashin kansa, ya kwanta a wurin nan yă yi barci. 12Ya yi mafarki, sai ga wata matakala tsaye a ƙasa, kanta ya kai Sama, mala'ikun Ubanmu kuwa suna hawa suna sauka a kanta. a a v12 Yesu ya shaida kansa a matsayin wannan matakala — haɗin da yake tsakanin ƙasa da Sama, shi ne wanda ta wurinsa muke zuwa wurin Ubanmu (Yohanna 1:51).
13Ga kuma Ubanmu tsaye a bisanta, ya ce, “Ni ne Ubanka, Allah na Ibrahim mahaifinka, da kuma na Ishaku. Zan ba ka kai da zuriyarka ƙasar da kake kwance a kanta. 14Zuriyarka za tă zama kamar ƙurar ƙasa; za ka bazu zuwa yamma da gabas da arewa da kudu. Ta wurinka da kuma zuriyarka, dukan iyalan duniya za su sami albarka. 15Ka sani, ina tare da kai. Zan tsare ka duk inda ka tafi, in kuma komo da kai zuwa wannan ƙasa. Ba zan rabu da kai ba sai na cika abin da na yi maka alkawari.”
16Sai Yaƙub ya farka daga barcinsa, ya ce, “Hakika Ubanmu yana a wannan wuri, ni kuwa ban sani ba!” 17Tsoro ya kama shi, sai ya ce, “Wannan wuri mai bantsoro ne ƙwarai! Wannan ba kome ba ne illa gidan Ubanmu, wannan kuwa ƙofar Sama ce.”
18Yaƙub ya tashi da sassafe, ya ɗauki dutsen da ya sa a ƙarƙashin kansa, ya kafa shi a matsayin al'amudi, ya kuma zuba mai a kansa. 19Ya sa wa wurin nan suna Betel, ko da yake dā sunan birnin Luz ne. b b v19 Betel yana nufin “gidan Allah”; dā ana kiran garin Luz. 20Yaƙub ya yi alkawari, ya ce, “In Allah yana tare da ni, ya kuma tsare ni a wannan tafiya da nake yi, ya ba ni abinci in ci da tufafi in sa, 21in kuma dawo lafiya zuwa gidan mahaifina, to, Ubanmu zai zama Ubana, 22wannan dutsen kuma da na kafa a matsayin al'amudi zai zama gidan Ubanmu, kuma daga cikin dukan abin da ka ba ni, hakika zan ba ka kashi ɗaya bisa goma.”