Gidanmu Madawwami Tare da Uba
Bulus ya bayyana dalilin da ya sa yake ci gaba da ba da jikinsa. Za a kwance alfarwar, gida daga Ubanmu kuma yana jira. Ƙaunar Almasihu tana iza shi, kujerar shari'ar Almasihu kuma tana jira. Ubanmu ya sulhunta duniya da kansa, Bulus kuwa yana ɗauke da wannan roƙo a matsayin jakada.
5 1Mun sani, in an rushe alfarwarmu ta duniya, muna da gini daga wurin Ubanmu, gida wanda ba a gina da hannaye ba, madawwami cikin sammai. 2Gama a cikin wannan alfarwa muna nishi, muna marmarin a suturta mu da mazauninmu na sama, 3in dai, sa'ad da muka sa shi, ba za a same mu tsirara ba. 4Yayinda muke cikin wannan alfarwa muna nishi, cikin nauyi—ba ma son a tuɓe mu ba ne, sai dai a ƙara suturta mu, domin rai yă haɗiye abin da yake na mutuwa. 5To, wanda ya shirya mu saboda wannan abu, Ubanmu ne, wanda ya ba mu Ruhu Mai Tsarki a matsayin lamuni.
6Saboda haka kullum muna da gabagaɗi, muna sane cewa muddin muna zaune a jiki, muna nesa da Ubangiji, 7gama muna tafiya ta wurin bangaskiya ne, ba ta wurin gani ba. 8Muna da gabagaɗi, mun kuma gwammace mu rabu da jiki, mu zauna tare da Ubangiji. 9Saboda haka, ko muna zaune a nan ko muna nesa, manufarmu ita ce mu gamshe shi. 10Gama dole dukanmu mu bayyana a gaban kujerar shari'ar Almasihu, domin kowa yă karɓi sakamakon abin da ya aikata a cikin jiki, ko nagari ne ko mugu.
An Sulhunta Mu, An Aiko da Mu a Matsayin Wakilai
11Saboda haka, da yake mun san tsoron Ubangiji, muna rinjayar mutane; a bayyane muke a gaban Ubanmu, ina kuma fatan a bayyane muke ga lamirinku. 12Ba sāke yabon kanmu muke yi muku ba, sai dai muna ba ku dalilin yin taƙama da mu, domin ku sami amsa ga waɗanda suke taƙama da bayyanar waje, ba ta zuciya ba. 13Ko mun rasa hankalinmu, to saboda Ubanmu ne; ko muna cikin hankalinmu, to saboda ku ne. 14Gama ƙaunar Almasihu tana matsa mana, tun da mun tabbata cewa, mutum ɗaya ya mutu saboda kowa, saboda haka duka sun mutu. 15Ya mutu saboda kowa, domin masu rai kada su ƙara rayuwa saboda kansu, sai dai saboda wanda ya mutu dominsu, aka kuma tashe shi.
16Saboda haka, daga yanzu, ba za mu san kowa bisa ga ma'aunin mutane ba. Dā mun taɓa sanin Almasihu haka, amma yanzu ba haka ba ne. 17Saboda haka, in wani yana cikin Almasihu, sabuwar halitta ce! Tsohon ya shuɗe; ga shi, sabon ya zo! 18Dukan wannan daga wurin Ubanmu ne, wanda ya sulhunta mu da kansa ta wurin Almasihu, ya kuma ba mu hidimar sulhu: a a v18 Sulhu yana farawa ne daga zuciyar Ubanmu kansa—shi ne wanda yake miƙa hannu domin yă dawo da mu gida, Yesu kuwa shi ne hanyar da yake bi. 19Wato, cikin Almasihu Ubanmu yana sulhunta duniya da kansa, ba ya lissafta zunubansu a kansu ba, ya kuma danƙa mana saƙon sulhu.
20Saboda haka mu wakilan Almasihu ne, kamar dai Ubanmu yana yin roƙo ta wurinmu. Muna roƙo a madadin Almasihu, ku sulhuntu da Ubanmu. 21Saboda mu, ya sa shi wanda bai san zunubi ba yă zama zunubi, domin cikinsa mu zama adalcin Ubanmu.