Yanzu a bugun takarda

1 Sama'ila 19 FHB Father's Heart Bible™

UbaYesuRuhu
Rangwamen 15% a odarku ta farko →
Littafi

Shawulu ya Yi Niyyar Kashe Dawuda

Yonatan ya lallashi mahaifinsa sau ɗaya, ya kuwa riƙe har zuwa mashi na gaba. Mikal ta saukar da Dawuda ta taga, ta sa gunki a gadonsa don ta sami lokaci. Manzannin Shawulu suka riƙa cika da Ruhun Ubanmu suna annabci maimakon su kama shi, sa'an nan Shawulu ma haka.

Babi na 19.

Shawulu ya yi magana da ɗansa Yonatan da dukan fadawansa game da kashe Dawuda. Amma Yonatan ɗan Shawulu yana jin daɗin Dawuda ƙwarai. Yonatan ya gaya wa Dawuda, “Shawulu mahaifina yana so yă kashe ka, saboda haka ka yi hankali da safe—ka ɓuya, kada a gan ka. Zan fita in tsaya kusa da mahaifina a cikin jeji inda kake, in yi magana da mahaifina game da kai—sa'an nan in gaya maka duk abin da na gano.”

Yonatan ya yi magana mai kyau game da Dawuda ga mahaifinsa Shawulu, ya ce masa, “Kada sarki yă yi wa bawansa Dawuda zunubi, gama bai yi maka zunubi ba. A maimakon haka, ayyukansa sun yi maka kyau ƙwarai. Ya sa ransa cikin hatsari domin yă kashe Bafilistin, Ubanmu kuwa ya ba da babban nasara ga dukan Isra'ila. Ka gan shi ka kuma yi farin ciki. Me ya sa za ka yi zunubi ga jinin marar laifi, ta wurin kashe Dawuda ba dalili ba?”

Shawulu ya saurari Yonatan, ya rantse, “Muddin Ubanmu yana raye, ba za a kashe Dawuda ba.”

Yonatan ya kira Dawuda ya gaya masa dukan wannan, sa'an nan ya kawo shi wurin Shawulu, Dawuda kuwa ya yi masa hidima kamar dā.

Yaƙi ya sāke ɓarkewa. Dawuda ya fita ya yaƙi Filistiyawa, ya karkashe su da bugu mai girma, suka kuwa gudu daga gabansa.

Amma wani mugun ruhu daga wurin Ubanmu ya auko wa Shawulu yayinda yake zaune a gidansa, da māshi a hannunsa, Dawuda kuwa yana kaɗa molo. Shawulu ya yi ƙoƙari yă kafe Dawuda a bango da māshinsa, amma Dawuda ya kauce, māshin kuwa ya kafu a bango. Dawuda ya gudu ya tsira a wannan dare. Shawulu ya aiki mutane su yi gadin gidan Dawuda, su kashe shi da gari ya waye. Mikal matar Dawuda ta gargaɗe shi, “In ba ka gudu yau da dare ba, za a kashe ka da safe.” Saboda haka Mikal ta saukar da Dawuda ta taga, ya kuwa gudu ya tsira. Sa'an nan Mikal ta ɗauki gunkin gida, ta kwantar da shi a kan gado, ta sa bargon gashin akuya a kansa, ta kuma rufe shi da zane. Sa'ad da Shawulu ya aiki manzanni su kama Dawuda, Mikal ta ce, “Ba shi da lafiya.”

Saboda haka Shawulu ya sāke aikin manzannin su ga Dawuda, yana cewa, “Ku kawo mini shi tare da gadon, domin in kashe shi.” Sa'ad da manzannin suka shigo, sai ga gunkin gida a kan gado, da bargon gashin akuya a kansa.

Shawulu ya ce wa Mikal, “Me ya sa kika yaudare ni haka, kika bar abokin gābana ya tsira?” Mikal ta ce wa Shawulu, “Ya ce mini, ‘Ki bar ni in tafi, don me zan kashe ki?’”

Dawuda ya gudu ya tsira, ya zo wurin Sama'ila a Rama, ya gaya masa dukan abin da Shawulu ya yi masa. Sa'an nan shi da Sama'ila suka tafi suka zauna a Nayiyot. Aka gaya wa Shawulu, “Dawuda yana Nayiyot a Rama.” Shawulu ya aiki manzanni su kama Dawuda. Amma da suka ga ƙungiyar annabawa suna annabci, Sama'ila kuma tsaye a matsayin shugabansu, sai Ruhun Ubanmu ya auko wa manzannin Shawulu, su ma suka yi annabci. Aka gaya wa Shawulu, sai ya aiki waɗansu manzanni, su ma suka yi annabci. Shawulu ya sāke aikin manzanni, sau na uku, su ma suka yi annabci. A ƙarshe Shawulu kansa ya tafi Rama, ya kai babbar rijiyar da take Seku. Ya yi tambaya, “Ina Sama'ila da Dawuda suke?” Sai wani ya ce, “A Nayiyot a Rama.”

Ya tafi Nayiyot a Rama, amma Ruhun Ubanmu ya auko masa shi ma, yana tafiya yana annabci, har ya isa Nayiyot a Rama. Shi ma ya tuɓe tufafinsa, ya yi annabci a gaban Sama'ila, ya kwanta tsirara dukan ranar nan da dare. Shi ya sa mutane kan ce, “Ko Shawulu ma yana cikin annabawa ne?”