Maganar Uba a kan Yerobowam
Yerobowam ya aiki matarsa a ɓoye don ta tambaya game da ɗansu da yake ciwo; Ahiya makaho, wanda Ubanmu ya riga ya faɗakar, ya kira sunanta a bakin ƙofa ya kuma amsa cewa yaron zai mutu da zarar ta kai gida, gidan kuma ya hallaka. A Yahuda, Shishak ya kwashe zinariyar haikali daga hannun Rehobowam.
14 1A lokacin nan Abiya ɗan Yerobowam ya yi rashin lafiya. 2Yerobowam ya ce wa matarsa, “Ki tashi, ki ɓad da kamanninki domin kada kowa ya gane ke matar Yerobowam ce, ki tafi Shilo. Annabi Ahiya yana can, wanda ya gaya mini cewa zan zama sarki a kan mutanen nan. 3Ki ɗauki dunƙulen burodi goma, da waɗansu wainu, da tulun zuma, ki tafi wurinsa. Zai gaya miki abin da zai faru da yaron.”
4Matar Yerobowam ta yi haka. Ta tafi Shilo, zuwa gidan Ahiya. Ahiya ba ya iya gani kuma; idanunsa sun dushe saboda tsufa.
5Amma Ubanmu ya riga ya gaya wa Ahiya, “Matar Yerobowam tana zuwa ta tambaye ka game da ɗanta mara lafiya. Ka gaya mata haka; sa'ad da ta zo, za ta ɓad da kamanninta kamar wata mace dabam.”
6Da Ahiya ya ji ƙarar sawunta a bakin ƙofa, sai ya ce, “Shigo, matar Yerobowam. Me ya sa kike riya kamar ke wata ce? An aiko ni gare ki da mugun labari.
7Ki tafi, ki gaya wa Yerobowam, ‘Ga abin da Ubanmu, Allah na Isra'ila, yake cewa, “Na ɗaga ka daga cikin mutane, na mai da kai shugaba a kan mutanena Isra'ila. 8Na yage mulki daga gidan Dawuda na ba ka shi. Duk da haka ba ka zama kamar bawana Dawuda ba, wanda ya kiyaye umarnaina ya kuma bi ni da dukan zuciyarsa, yana yin abin da yake daidai a idanuna kaɗai. 9Ka yi mugunta fiye da duk waɗanda suka riga ka. Ka tafi ka yi waɗansu alloli da gumaka na zubi, kana tsokanata har in yi fushi, ka kuma jefa ni a bayanka. 10Saboda haka ina kawo masifa a kan gidan Yerobowam. Zan datse wa Yerobowam kowane namiji a cikin Isra'ila, bawa da 'yantacce, zan kuma ƙone gidan Yerobowam kamar yadda akan ƙone taki har sai ya ƙare. 11Duk wanda yake na Yerobowam da ya mutu a cikin birni, karnuka za su cinye shi, waɗanda kuma suka mutu a jeji tsuntsayen sama za su cinye su. Gama Ubanmu ya yi magana.”’
12Ki tashi, ki tafi gida. Sa'ad da ƙafafunki suka shiga birni, yaron zai mutu. 13Dukan Isra'ila za su yi makokinsa su kuma binne shi. Shi kaɗai daga gidan Yerobowam zai kai ga kabari, domin a cikinsa ne Ubanmu, Allah na Isra'ila, ya sami wani abu mai kyau a gidan Yerobowam. 14Ban da haka, Ubanmu zai tā da wa kansa wani sarki a kan Isra'ila wanda zai datse gidan Yerobowam a wannan rana—har ma yanzu. 15Ubanmu zai bugi Isra'ila har ta yi ta rawa kamar iwa a cikin ruwa, zai tumɓuke su daga wannan ƙasa mai kyau da ya ba kakanninsu, zai kuma warwatsa su har gaba da Kogin Yufiretis, domin sun yi gumakan Ashera da suka tsokane shi ya yi fushi. 16Zai ba da Isra'ila saboda zunuban da Yerobowam ya yi, ya kuma sa Isra'ila suka yi.”
17Matar Yerobowam ta tashi, ta tafi, ta kuma isa Tirza. Da ta kai bakin ƙofar gida, sai yaron ya mutu. 18Dukan Isra'ila suka binne shi suka yi makokinsa, yadda Ubanmu ya faɗa ta bakin bawansa annabi Ahiya.
19Sauran ayyukan Yerobowam, yadda ya yi yaƙe-yaƙe ya kuma yi mulki, a rubuce suke a cikin Littafin Tarihin Sarakunan Isra'ila. 20Yerobowam ya yi sarauta shekara ashirin da biyu, sa'an nan ya huta tare da kakanninsa, ɗansa Nadab kuwa ya yi sarauta a maimakonsa.
Rehobowam Ya Yi Sarauta a Yahuda
21Rehobowam ɗan Sulemanu ya yi sarauta a Yahuda. Yana da shekara arba'in da ɗaya sa'ad da ya zama sarki, ya kuma yi sarauta shekara goma sha bakwai a Urushalima, birnin da Ubanmu ya zaɓa daga dukan kabilan Isra'ila domin ya sa sunansa a can. Sunan mahaifiyarsa Na'ama ce, Baamoniya. 22Yahuda suka yi mugunta a gaban Ubanmu, suka tsokane shi har ya yi kishi ta wurin zunuban da suka yi—fiye da duk abin da kakanninsu suka yi. 23Su ma suka gina wa kansu masujadan kan tudu, da keɓaɓɓun al'amudai, da gumakan Ashera a kan kowane tudu mai tsayi da kuma ƙarƙashin kowane koren itace. 24Har ma akwai karuwan maza na masujada a ƙasar. Mutanen suka yi dukan abubuwan ƙyama na al'umman da Ubanmu ya kori daga gaban Isra'ila.
25A shekara ta biyar ta Sarki Rehobowam, Shishak sarkin Masar ya hauro ya yaƙi Urushalima. 26Ya kwashe dukiyar gidan Ubanmu da ta fadar sarki—kome, har da dukan garkuwoyin zinariya da Sulemanu ya yi. 27Saboda haka Sarki Rehobowam ya yi garkuwoyin tagulla don maimakonsu, ya kuma miƙa su ga shugabannin masu gadi da suke tsaron ƙofar fadar sarki. 28A duk sa'ad da sarki ya shiga gidan Ubanmu, masu gadi sukan ɗauki garkuwoyin, sa'an nan su mayar da su cikin ɗakin gadi.
29Sauran ayyukan Rehobowam, da dukan abin da ya yi—ba a rubuce suke a cikin Littafin Tarihin Sarakunan Yahuda ba? 30Akwai yaƙi kullum tsakanin Rehobowam da Yerobowam. 31Rehobowam ya huta tare da kakanninsa, aka binne shi tare da su a Birnin Dawuda. Sunan mahaifiyarsa Na'ama ce, Baamoniya. Ɗansa Abiyam kuwa ya yi sarauta a maimakonsa.