Alkawarin Ubanmu da Dawuda
Dawuda yana so ya gina wa Ubanmu gida, Natan kuma ya amince kafin ya ji daga gare shi. Amsar ta juya shi: Ubanka zai gina maka gida, ɗanka kuma zai gina nawa. Dawuda ya tafi ya zauna, yana cike da mamaki cewa duk wannan ya shafe shi.
17 1Bayan Dawuda ya zauna a gidansa, sai ya ce wa annabi Natan, “Dubi, ina zama a gidan itacen al'ul, amma akwatin alkawarin Ubanmu yana ƙarƙashin labulen tenti.”
2Natan ya amsa wa Dawuda ya ce, “Ka yi duk abin da yake a zuciyarka, gama Ubanmu yana tare da kai.”
3Amma a daren nan maganar Ubanmu ta zo wa Natan, ta ce:
4Ka tafi ka gaya wa bawana Dawuda, “Ga abin da Ubanka ya ce: Ba kai ne za ka gina mini gida in zauna a ciki ba.” 5Ban taɓa zama a gida ba tun ranar da na fitar da Isra'ila har yă zuwa yanzu—na yi ta yawo daga tenti zuwa tenti, daga mazauni zuwa mazauni.
6Duk inda na yi zirga-zirga tare da dukan Isra'ila, shin na taɓa yin magana da wani daga cikin alƙalan Isra'ila, waɗanda na umarce su su yi kiwon mutanena, na ce, “Don me ba ku gina mini gidan itacen al'ul ba?”
7Saboda haka ka gaya wa bawana Dawuda, “Ga abin da Uban rundunonin Sama ya ce: Na ɗauke ka daga wurin kiwo, daga bin garke, ka zama mai mulki a kan mutanena Isra'ila. 8Na kasance tare da kai duk inda ka tafi, na kuma karkashe dukan maƙiyanka a gabanka. Yanzu zan sa sunanka kamar sunan manyan mutanen duniya. 9Zan tanada wa mutanena Isra'ila wuri, in dasa su a can, su zauna a gidansu, ba kuma za a ƙara damun su ba. Mugaye ba za su ƙara danne su ba yadda suka yi dā, 10tun lokacin da na naɗa alƙalai a kan mutanena Isra'ila. Zan rinjayi dukan maƙiyanka. Ina gaya maka, Ubanka zai gina maka gida. 11Sa'ad da kwanakinka suka cika, ka tafi ka kasance tare da kakanninka, zan tā da zuriyarka a bayanka, ɗaya daga cikin 'ya'yanka, zan kuma kafa mulkinsa. 12Shi ne zai gina mini gida, zan kuma kafa gadon sarautarsa har abada. 13Zan zama Ubansa, shi kuma zai zama ɗana. Ba zan ƙwace madawwamiyar ƙaunata daga gare shi ba yadda na ƙwace ta daga wanda ya riga ka. 14Zan naɗa shi a kan gidana da mulkina har abada, gadon sarautarsa kuma zai tsaya daram har abada.”
15Natan ya faɗa wa Dawuda dukan waɗannan maganganu da kuma wannan wahayi duka.
Dawuda ya Zauna a Gaban Ubanmu da Mamaki
16Sai Sarki Dawuda ya shiga, ya zauna a gaban Ubanmu, ya ce, “Wane ne ni, ya Ubana, kuma mene ne gidana, da ka kawo ni har wannan? 17Kamar dai wannan ƙaramin abu ne a idanunka, ya Ubana—ka yi magana game da gidan bawanka har zuwa nan gaba mai nisa, ka kuma dube ni kamar babban mutum a cikin mutane, ya Ubana. 18Me kuma Dawuda zai iya ce maka saboda girmama bawanka? Gama ka san bawanka. 19Ya Ubana, saboda bawanka kuma bisa ga nufin zuciyarka, ka yi dukan waɗannan manyan ayyuka, ka bayyana dukan waɗannan manyan alkawura. 20Ya Ubana, babu wani kamar ka, babu wani Uba sai kai, yadda muka ji da kunnuwanmu. 21Wane ne kamar mutanenka Isra'ila, al'umma guda a duniya da Ubanmu ya tafi ya fanshe su su zama jama'a gare shi, kana yi wa kanka suna ta wurin manya da ayyuka masu ban tsoro, kana korar al'ummai a gaban mutanenka, waɗanda ka fanshe daga Masar? 22Ka mai da mutanenka Isra'ila naka na har abada, kai kuma, ya Ubana, ka zama Ubansu. 23Yanzu, ya Ubana, bari maganar da ka faɗa game da bawanka da gidansa tă tabbata har abada, ka yi yadda ka faɗa. 24Bari tă tabbata, sunanka kuma yă ƙara girma har abada, don a ce, ‘Uban rundunonin Sama shi ne Ubanmu a kan Isra'ila.’ Bari a kafa gidan bawanka Dawuda a gabanka. 25Gama kai, ya Ubana, ka bayyana wa bawanka cewa za ka gina masa gida—saboda haka bawanka ya sami ƙarfin hali ya yi addu'a a gabanka. 26Yanzu, ya Ubana, kai ne Ubanmu, ka yi wa bawanka alkawarin wannan abu mai kyau. 27Yanzu ka zaɓa ka albarkaci gidan bawanka, domin yă ci gaba a gabanka har abada, gama kai, ya Ubana, ka albarkace shi, shi kuwa albarkatacce ne har abada.”