Ubanmu Ya Yi Gargaɗi ta Wurin Irmiya
Sojojin Masar sun janye Babilawa, Urushalima kuwa ta sa zuciya; Irmiya ya kawo maganar Ubanmu cewa za su dawo su ƙone birnin. Yana barin birni domin al'amarin iyalinsa, sai aka kama shi a matsayin mai gudu zuwa wajen abokan gaba, aka yi masa duka, aka sa shi a kurkuku. Zedekiya ya tambaye shi a ɓoye ko akwai magana, ya sami mai tsanani, ya kuma ba shi abinci.
37 1Zedekiya ɗan Yosiya ya yi sarauta a maimakon Koniya ɗan Yehoyakim, wanda Nebukadnezzar sarkin Babila ya naɗa sarki a ƙasar Yahuda. 2Amma ko shi, ko fadawansa, ko mutanen ƙasar, ba su kula da maganar Ubanmu da aka faɗa ta wurin annabi Irmiya ba.
3Sarki Zedekiya ya aiki Yehukal ɗan Shelemiya da Zefaniya ɗan Ma'aseiya firist wurin annabi Irmiya su ce, “Muna roƙonka, ka yi mana addu'a ga Ubanmu.”
4A lokacin Irmiya yana ta kai da kawowa cikin mutane, gama ba a riga an sa shi a kurkuku ba. 5Mayaƙan Fir'auna kuwa suka fito daga Masar. Da Babiloniyawa da suke kewaye da Urushalima suka ji labari, sai suka janye daga Urushalima.
6Sai maganar Ubanmu ta zo wurin annabi Irmiya cewa,
7Ga abin da Ubanmu na Isra'ila yake cewa, Ka faɗa wa sarkin Yahuda wanda ya aike ka wurina ka tambaye ni cewa, Mayaƙan Fir'auna da suka fito domin su taimake ka, suna komawa gida ƙasarsu ta Masar. 8Sa'an nan Babiloniyawa za su dawo su yaƙi wannan birni, su ƙwace shi, su kuma ƙone shi da wuta.
9Ga abin da Ubanmu yake cewa, Kada ku ruɗi kanku, kuna cewa, “Lalle Babiloniyawa za su rabu da mu.” Ba za su rabu ba. 10Ko da kun hallaka dukan mayaƙan Babila da suke yaƙe ku, har waɗanda suka ji rauni kaɗai suka ragu cikin tentunansu, za su tashi su ƙone wannan birni da wuta.
An Kama Irmiya Aka Sa shi a Kurkuku
11To, sa'ad da mayaƙan Babila suka janye daga Urushalima saboda mayaƙan Fir'auna, 12sai Irmiya ya fita daga Urushalima zuwa ƙasar Benyamin domin ya karɓi rabonsa a can cikin mutane. 13Da ya kai Ƙofar Benyamin, sai shugaban masu gadi mai suna Iriya ɗan Shelemiya ɗan Hananiya ya kama annabi Irmiya ya ce, “Kana gudu zuwa wurin Babiloniyawa ne!”
14Irmiya ya ce, “Ƙarya ce! Ba na gudu zuwa wurin Babiloniyawa.” Amma Iriya bai kula da shi ba, sai ya kama Irmiya ya kai shi wurin shugabanni.
15Shugabannin kuwa suka yi fushi da Irmiya, suka yi masa dūka, suka sa shi a kurkuku a gidan Yonatan marubuci, wanda aka mai da shi kurkuku.
16Haka Irmiya ya shiga ɗakunan ƙarƙashin ƙasa na kurkukun, a can kuma ya kwana kwanaki masu yawa. 17Sa'an nan Sarki Zedekiya ya aika aka fito da shi. Sarki ya tambaye shi a ɓoye a cikin fada ya ce, “Akwai wata magana daga wurin Ubanmu?” Irmiya ya ce, “Akwai. Za a bashe ka ga sarkin Babila.”
18Irmiya ya tambayi Sarki Zedekiya ya ce, “Yaya na yi maka zunubi, ko ga fadawanka, ko ga wannan jama'a, da ka sa ni a kurkuku? 19Ina annabawanku yanzu, waɗanda suka yi annabci cewa, ‘Sarkin Babila ba zai zo yaƙe ku ko wannan ƙasa ba’? 20Yanzu ina roƙonka, ka saurare ni, ya ranka yă daɗe sarki. Bari roƙona yă kai gare ka, kada ka mai da ni gidan Yonatan marubuci, don kada in mutu a can.”
21Sai Sarki Zedekiya ya ba da umarni, suka sa Irmiya a filin masu gadi, suna ba shi gurasa guda kowace rana daga titin masu tuya, har sai da gurasar birnin ta ƙare. Haka Irmiya ya zauna a filin masu gadi.