Naɗaɗɗen Littafi Mai Zaƙi kamar Zuma
Ya ci takardar, ɗanɗanonta kuma ya yi zaƙi kamar zuma, sa'an nan aka ɗauke shi zuwa wurin waɗanda suke zaman bauta a Tel-abib, inda ya zauna cikinsu a ruɗe kwana bakwai. Ubanmu ya mai da shi mai tsaro, wanda zai ba da lissafin yin gargaɗi, sa'an nan ya ɗaure harshensa don ya yi magana sai lokacin da aka ba shi kalmomi kaɗai.
3 1Ya ce mini, “Ɗan mutum, ka ci abin da ka samu. Ka ci wannan naɗaɗɗen littafi, sa'an nan ka tafi ka yi magana da gidan Isra'ila.”
2Sai na buɗe bakina, ya kuwa ba ni wannan naɗaɗɗen littafi in ci.
3Ya ce mini, “Ɗan mutum, ka ciyar da cikinka, ka cika cikinka da wannan naɗaɗɗen littafin da nake ba ka.” Sai na cinye shi, a bakina kuwa ya yi zaƙi kamar zuma.
4Sa'an nan ya ce mini, “Ɗan mutum, ka tafi wurin gidan Isra'ila ka faɗa musu maganata.
5“Gama ba a aike ka wurin mutane masu baƙar magana da wuyar harshe ba, sai dai wurin gidan Isra'ila, 6ba wurin mutane masu yawa masu baƙar magana da wuyar harshe da ba za ka iya gane maganarsu ba. Lalle, da na aike ka wurinsu, da sun saurare ka. 7Amma gidan Isra'ila ba za su yarda su saurare ka ba, domin ba sa so su saurare ni; gama dukan gidan Isra'ila masu taurin kai ne da taurin zuciya. 8Ga shi, na mai da fuskarka da tauri kamar fuskokinsu, goshinka kuma da tauri kamar goshinsu. 9Na mai da goshinka kamar dutse mai tauri ƙwarai, wanda ya fi dutsen wuta tauri. Kada ka ji tsoronsu ko ka firgita saboda kallonsu, gama su gidan 'yan tawaye ne.”
10Ya ce mini, “Ɗan mutum, ka ɗauki dukan kalmomin da nake faɗa maka a cikin zuciyarka, ka kuma saurare su da kunnuwanka. 11Ka tafi wurin waɗanda aka kai zaman bauta, wato mutanenka, ka yi musu magana. Ka ce musu, ‘Ga abin da Uba Mai Iko Duka yake cewa,’ ko sun saurara ko sun ƙi saurara.”
12Sai Ruhun Ubanmu ya ɗaga ni, na kuma ji wata babbar ƙara mai motsi a bayana, “Albarka ta tabbata ga ɗaukakar Ubanmu daga mazauninsa!” 13ƙarar fikafikan halittu masu rai suna shafa juna, da ƙarar ƙafafun da suke gefensu, wata babbar ƙara mai motsi. 14Ruhu ya ɗaga ni ya tafi da ni, na kuwa tafi cikin ɗaci, ruhuna yana ƙuna a cikina, hannun Ubanmu kuwa yana da ƙarfi a kaina. 15Na iso wurin waɗanda aka kai zaman bauta a Tel-abib kusa da Kogin Kebar, na kuwa zauna a cikinsu a can, cike da mamaki, kwana bakwai.
Uba Ya Naɗa Mai Tsaro
16Bayan kwana bakwai, sai maganar Ubanmu ta zo mini,
17“Ɗan mutum, na mai da kai mai tsaro domin gidan Isra'ila. Duk sa'ad da ka ji magana daga bakina, sai ka gargaɗe su a madadina. 18Idan na ce wa mugu, ‘Lalle za ka mutu,’ kai kuwa ba ka gargaɗe shi ba, ba ka kuma yi magana don ka gargaɗi mugun yă bar muguwar hanyarsa domin ya ceci ransa ba, mugun nan zai mutu cikin zunubinsa, amma zan nemi alhakin jininsa daga hannunka.
19“Amma in ka gargaɗi mugun, bai kuwa juya daga muguntarsa ko muguwar hanyarsa ba, zai mutu cikin zunubinsa, amma kai ka ceci ranka.
20“Haka kuma, sa'ad da mai adalci ya juya daga adalcinsa ya yi laifi, na kuma sa dutsen tuntuɓe a gabansa, zai mutu. Tun da ba ka gargaɗe shi ba, zai mutu cikin zunubinsa, ba za a kuma tuna da ayyukansa na adalci ba, zan kuwa nemi alhakin jininsa daga hannunka. 21Amma in ka gargaɗi mai adalci kada ya yi zunubi, bai kuwa yi ba, zai rayu domin ya kula da gargaɗin, kai kuwa ka ceci ranka.”
22Hannun Ubanmu yana a kaina a can, sai ya ce mini, “Ka tashi, ka fita zuwa kwari, a can kuwa zan yi magana da kai.”
23Sai na tashi na tafi kwarin, a can kuwa ɗaukakar Ubanmu ta tsaya, kamar ɗaukakar da na gani kusa da Kogin Kebar, sai na fāɗi rubda ciki.
24Ruhu ya shiga cikina, ya tsai da ni a ƙafafuna, ya yi magana da ni, ya ce, “Ka tafi, ka kulle kanka a cikin gidanka. 25Kai kuma, ɗan mutum, za su ɗaura maka igiyoyi su daure ka da su, don kada ka iya fita cikin mutane.
26Zan sa harshenka yă manne a rufin bakinka; za ka zama bebe, ba za ka iya tsauta musu ba, gama su gidan 'yan tawaye ne. 27Amma sa'ad da na yi magana da kai, zan buɗe bakinka, za ka kuma ce musu, ‘Ga abin da Uba Mai Iko Duka yake cewa.’ Duk wanda yake so yă saurara, sai yă saurara; duk wanda kuma zai ƙi, sai yă ƙi—gama su gidan 'yan tawaye ne.”