Mafaka ta Dukan Rayuwa
Addu'ar tsoho. Ya dogara ga Ubansa tun haihuwarsa, yanzu kuma yana tsoron a yar da shi yayin da ƙarfinsa yake raguwa, abokan gāba kuma suna cewa an yashe shi. Abin da yake roƙo shi ne lokaci — domin ya ci gaba da faɗa wa tsara mai zuwa abin da ya sani.
71 1A gare ka, ya Ubana, na nemi mafaka; kada a taɓa kunyata ni. 2Cikin adalcinka ka ceto ni, ka kuɓutar da ni; ka saurare ni, ka cece ni. 3Ka zama dutsena na mafaka, wanda kullum zan iya zuwa gare shi; ka ba da umarni domin a ceto ni, gama kai ne dutsena da kagarata. 4Ya Ubana, ka kuɓutar da ni daga hannun mugaye, daga damƙar marasa adalci da masu zalunci.
5Gama kai ne begena, ya Uba Mai Iko Duka, abin dogarata tun ƙuruciyata. 6Na dogara gare ka tun haihuwata; kai ne ka ɗauke ni daga cikin mahaifiyata. Kullum ina yabonka. 7Na zama abin mamaki ga mutane masu yawa, amma kai ne mafakata mai ƙarfi. 8Bakina yana cike da yabonka, da ɗaukakarka dukan yini.
9Kada ka watsar da ni a lokacin tsufata; sa'ad da ƙarfina ya raunana, kada ka yashe ni. 10Gama maƙiyana suna maganar gāba da ni; waɗanda suke lura domin su ƙwace raina suna haɗa baki tare. 11Suna cewa, “Allah ya yashe shi; ku bi shi, ku kama shi, gama babu wanda zai kuɓutar da shi.”
12Ya Ubana, kada ka yi nesa da ni; ya Ubana, ka yi hanzari ka taimake ni! 13Bari masu zargina su sha kunya su kuma hallaka; bari waɗanda suke neman cutata a lulluɓe su da reni da kunya.
14Amma zan yi bege kullum, zan kuma ƙara yabonka da yawa. 15Bakina zai faɗi adalcinka, da cetonka dukan yini, ko da yake ban san yawansa ba. 16Zan zo ina shelar manyan ayyukan Uba Mai Iko Duka; zan yi shelar adalcinka, naka kaɗai.
17Ya Ubana, ka koya mini tun ƙuruciyata, kuma har yau ina shelar ayyukanka masu ban mamaki. 18Saboda haka ko sa'ad da na tsufa na kuma yi furfura, ya Ubana, kada ka yashe ni, sai na yi shelar ikonka ga wani tsara, da ƙarfinka ga dukan waɗanda za su zo.
19Adalcinka, ya Ubana, ya kai can sammai masu tsawo. Kai da ka yi manyan abubuwa, ya Ubana, wa yake kamanka? 20Kai da ka nuna mini wahaloli da masifu masu yawa za ka sāke rayar da ni; daga zurfin ƙasa za ka sāke fito da ni. 21Za ka ƙara mini girma ka kuma sāke ta'azantar da ni.
22Zan kuma yabe ka da molo saboda amincinka, ya Ubana; zan rera maka yabo da garaya, ya Mai Tsarki na Isra'ila—Ubana. 23Leɓunana za su yi sowa ta murna sa'ad da nake rera maka yabo, da raina kuma, wanda ka fanshe. 24Harshena kuma zai faɗi adalcinka dukan yini, gama waɗanda suka nemi cutata sun sha kunya suka kuma wulaƙantu.