Ubanmu Yake Kafa Takawar Mutum
Zuciya tana shiryawa, Ubanmu kuma yana bi da matakai. Wannan ja-in-ja tana ratsa dukan babin har zuwa kuri'ar da ake jefawa a cinya. Yawancinsa game da sarakuna ne da yanayinsu. Girmankai yana gaban faɗuwa, mallakar ranka kuma ta fi cin birni.
16 1Shirye-shiryen zuciya na mutum ne, amma amsar harshe daga Ubanmu take. 2Dukan hanyoyin mutum tsabtatattu ne a idonsa, amma Ubanmu yakan auna niyyar zuciya. 3Ka danƙa ayyukanka ga Ubanmu, shirye-shiryenka kuma za su tabbata. 4Ubanmu ya yi kome domin manufarsa, har da mugaye domin ranar masifa. 5Duk mai girman kai abin ƙyama ne ga Ubanmu; ka tabbata, ba zai tafi babu hukunci ba. 6Ƙauna da aminci suna kaffara zunubi, tsoron Ubanmu kuma yakan juyar da mutum daga mugunta. 7Sa'ad da hanyoyin mutum suka gamshi Ubanmu, sai Ubanmu ya sa har abokan gāban mutumin su yi zaman lafiya da shi. 8Gara kaɗan tare da adalci da riba mai yawa tare da rashin gaskiya. 9Zuciyar mutum takan shirya hanyarsa, amma Ubanmu yake kafa takawarsa. 10Hukuncin Allah yana bisa leɓunan sarki; bakinsa ba ya ci amanar adalci. 11Sikeli da ma'auni masu gaskiya na Ubanmu ne; dukan ma'aunin nauyi da ke cikin jaka aikinsa ne. 12Abin ƙyama ne ga sarakuna su aikata mugunta, gama ta wurin adalci ake kafa gadon sarauta. 13Leɓunan adalci farin cikin sarakuna ne, suna kuma ƙaunar mai faɗar gaskiya. 14Fushin sarki ɗan aika na mutuwa ne, amma mai hikima zai kwantar da shi. 15Cikin haske na fuskar sarki akwai rai, tagomashinsa kuma kamar girgijen ruwan bazara ne. 16Ya fi kyau ƙwarai a sami hikima fiye da zinariya! Samun fahimi ya fi azurfa daraja. 17Babbar hanyar masu adalci takan juya daga mugunta; duk mai tsaron hanyarsa yana kāre ransa. 18Girman kai yakan riga halaka, ruhun fahariya kuma yakan riga fāɗuwa. 19Gara ka zama mai tawali'u a cikin matalauta da ka raba ganima tare da masu girman kai. 20Duk wanda yake kula da magana zai sami alheri, mai albarka kuma shi ne wanda ya dogara ga Ubanmu. 21Akan kira mai hikima a zuci mai basira, magana mai daɗi kuma takan ƙara rarrashi. 22Fahimi maɓuɓɓugar rai ne ga wanda yake da shi, amma wauta ce take horon wawaye. 23Zuciyar mai hikima takan sa maganarsa ta zama ta hikima, takan kuma ƙara rarrashi a leɓunansa. 24Kalmomi masu daɗi gumbar zuma ne, mai zaƙi ga rai, da warkarwa ga ƙasusuwa. 25Akwai hanyar da take kama da daidai ga mutum, amma ƙarshenta hanyar mutuwa ce. 26Marmarin mai aiki yana aiki dominsa; yunwarsa takan tura shi gaba. 27Mutumin banza yakan tona mugunta, a leɓunansa kuma akwai wuta mai ƙuna. 28Mutum mai karkata yakan baza faɗa, mai gulma kuma yakan rarraba abokai na kusa. 29Mutum mai rikici yakan ruɗi maƙwabcinsa yă kuma bi da shi a hanyar lahani. 30Mai ƙyaftawa da idanunsa yana ƙulla mugunta; mai matse leɓunansa ya kuduri aniyar mugunta. 31Furfura rawanin ɗaukaka ne; akan same shi ta wurin tafiya a hanyar adalci. 32Gara mai haƙuri da mai ƙarfi, mai mallakar ransa kuma ya fi mai ƙwace birni. 33Akan jefa ƙuri'a a cinya, amma kowane hukuncinta daga Ubanmu yake.