Amsa Mai Laushi Takan Kawar da Hasala
Wannan game da yanayin magana ne. Amsa mai taushi tana kawar da fushi, kalma mai zafi kuma tana tayar da shi, kalmar da ta zo a lokacin da ya dace kuma abin farin ciki ce. Yana maimaita cewa idanun Ubanmu suna ko'ina, ya kuma fifita ganye tare da ƙauna fiye da sa mai ƙiba tare da ƙiyayya.
15 1Amsa mai laushi takan kawar da hasala, amma magana mai zafi takan tā da fushi. 2Harshen masu hikima yakan yabi sani, amma bakunan wawaye sukan zubo wauta. 3Idanun Ubanmu suna ko'ina, suna kallon mugaye da masu kirki. 4Harshe mai laushi itaciyar rai ne, amma harshe mai lalaci yakan karya ruhu. 5Wawa yakan rena horon ubansa, amma duk wanda yake kula da gyara mai hankali ne. 6A gidan mai adalci akwai dukiya mai yawa, amma ribar mugu takan kawo wahala. 7Leɓunan masu hikima sukan baza sani, amma zukatan wawaye ba haka suke ba. 8Hadayar mugaye abin ƙyama ce ga Ubanmu, amma addu'ar masu adalci tana faranta masa rai. 9Hanyar mugu abin ƙyama ce ga Ubanmu, amma yana ƙaunar wanda yake neman adalci. 10Akwai horo mai tsanani ga wanda ya bar hanya, duk wanda kuma ya ƙi gyara zai mutu. 11Lahira da Hallaka a buɗe suke a gaban Ubanmu; balle fa zukatan dukan mutane! 12Mai ba'a ba ya son a gyara shi; ba zai je wurin masu hikima ba. 13Zuciya mai farin ciki takan sa fuska ta yi fara'a, amma zuciya mai baƙin ciki takan karya ruhu. 14Zuciya mai basira takan nemi sani, amma bakunan wawaye sukan ci wauta. 15Dukan kwanakin mai shan wahala masu wuya ne, amma zuciya mai farin ciki kullum tana biki. 16Gara kaɗan tare da tsoron Ubanmu da dukiya mai yawa tare da wahala. 17Gara abincin ganye inda akwai ƙauna da sa mai ƙiba tare da ƙiyayya. 18Mai saurin fushi yakan tā da faɗa, amma mai jinkirin fushi yakan kwantar da husuma. 19Hanyar rago kamar shingen ƙaya take, amma hanyar masu adalci babbar hanya ce mai santsi. 20Ɗa mai hikima yakan faranta wa mahaifinsa rai, amma wawa yakan rena mahaifiyarsa. 21Wauta abin farin ciki ce ga marar hankali, amma mai fahimi yakan bi miƙaƙƙiyar hanya. 22Shirye-shirye sukan lalace in babu shawara, amma da mashawarta masu yawa sukan yi nasara. 23Mutum yakan ji farin ciki sa'ad da ya ba da amsa daidai, ina kuma misalin kyan magana da ta zo a kan kari! 24Hanyar rai takan kai mai hankali sama, tana juyar da shi daga Lahira can ƙasa. 25Ubanmu yakan rushe gidan masu girman kai, amma yakan kiyaye iyakar gwauruwa. 26Tunanin mugaye abin ƙyama ne ga Ubanmu, amma kalmomi masu alheri tsarkaka ne. 27Duk wanda yake haɗamar ribar zalunci yakan kawo wa iyalinsa wahala, amma wanda yake ƙin cin hanci zai rayu. 28Zuciyar mai adalci takan auna yadda za ta ba da amsa, amma bakin mugu yakan zubo mugunta. 29Ubanmu yana nesa da mugaye, amma yakan ji addu'ar masu adalci. 30Hasken ido yakan faranta wa zuciya rai, labari mai daɗi kuma yakan ƙarfafa ƙasusuwa. 31Kunnen da yake sauraron gyara mai ba da rai zai zauna cikin masu hikima. 32Duk wanda ya ƙyale horo yana rena kansa, amma wanda yake sauraron gyara yakan sami fahimi. 33Tsoron Ubanmu horon hikima ne, tawali'u kuma yana zuwa kafin ɗaukaka.