Uba Ya Hukunta Ƙiyayyar Dā ta Edom
Edom, a Dutsen Seyir, ta riƙe ƙiyayya ta dā ta kuma ba da Isra'ila ga takobi a ranar masifa, sa'an nan ta ce ƙasashen biyu da aka wofintar nata ne. Ubanmu ya amsa cewa Edom ce za ta zama wofi, har abada.
35 1Maganar Ubanmu ta zo mini cewa,
2Ɗan mutum, ka kafa fuskarka gāba da Dutsen Seyir, ka yi annabci a kansa. 3Ka ce masa, Ga abin da Uba Mai Iko Dukka yake cewa, “Ga shi, ina gāba da kai, Dutsen Seyir. Zan miƙa hannuna gāba da kai, in mai da kai kufai da kango. 4Zan mai da garuruwanka kufai, za ka kuma zama kufai. Sa'an nan za ka san cewa ni ne Uba.
5Domin ka riƙe ƙiyayya ta dā, ka kuma ba da mutanen Isra'ila ga takobi a lokacin masifarsu, a lokacin da hukuncinsu na ƙarshe ya zo,” 6saboda haka, muddin ina raye, in ji Uba Mai Iko Dukka, zan ba da kai ga zub da jini, zub da jini kuma zai bi ka. Tun da yake ba ka ƙi zub da jini ba, zub da jini zai bi ka. 7“Zan mai da Dutsen Seyir kufai da kango, in kuma datse daga gare shi duk mai zuwa da komowa. 8Zan cika duwatsunsa da waɗanda aka kashe; a kan tuddanka, da kwaruruka, da dukan rafukanka, waɗanda aka kashe da takobi za su fāɗi. 9Zan mai da kai kufai har abada; ba za a sāke zama a garuruwanka ba. Sa'an nan za ka san cewa ni ne Uba.
10Saboda ka ce, ‘Waɗannan al'ummai biyu, waɗannan ƙasashe biyu za su zama nawa; za mu mallake su’—ko da yake Ubanmu yana nan,” 11saboda haka, muddin ina raye, in ji Uba Mai Iko Dukka, zan yi maka gwargwadon fushi da kishin da ka nuna cikin ƙiyayyarka ga Isra'ila, zan kuma sanar da kaina a cikin mutanen Isra'ila sa'ad da na hukunta ka.
12Sa'an nan za ka san ni ne Uba. Na ji dukan renin da ka yi wa duwatsun Isra'ila, kana cewa, “An mai da su kufai, an ba mu su mu cinye.” 13Ka yi fahariya a kaina da bakinka, ka kuma tara maganganunka a kaina; na ji su. 14Ga abin da Uba Mai Iko Dukka yake cewa, Yayin da dukan duniya take murna, zan mai da kai kufai. 15Kamar yadda ka yi murna domin gādon gidan Isra'ila ya zama kufai, haka ma zan yi maka. Za ka zama kufai, Dutsen Seyir, da dukan Edom, dukanta. Sa'an nan za su san cewa ni ne Uba.