Annoba Guda Ɗaya Kuma
Annoba ɗaya ta rage. Da tsakar dare kowane ɗan fari a Masar zai mutu, daga kan gadon sarauta har zuwa wurin niƙa, kuma kuka zai tashi irin wanda ba a taɓa ji ba. Duk da haka ko kare ba zai yi wa Isra'ila haushi ba — Ubanmu ya bayyana bambancin sarai. Musa ya fita daga gaban Fir'auna da zafin fushi.
11 1Ubanmu ya ce wa Musa, “Sauran annoba guda ɗaya zan kawo a kan Fir'auna da kuma Masar. Bayan haka zai bar ku ku fita daga nan; sa'ad da ya yi haka, zai kore ku gaba ɗaya. 2Ka gaya wa mutane, kowane mutum yă roƙi maƙwabcinsa, kowace mace kuma maƙwabciyarta, kayan azurfa da na zinariya.”
3Ubanmu kuwa ya sa mutanen suka sami tagomashi a wurin Masarawa. Ban da haka, Musa da kansa ya zama mai girma ƙwarai a ƙasar Masar, a idanun bayin Fir'auna da kuma na mutanen.
4Musa ya ce, “Ga abin da Ubanmu ya ce: Wajen tsakar dare zan ratsa Masar,
5kowane ɗan fari kuma a ƙasar Masar zai mutu, daga ɗan farin Fir'auna wanda yake zaune a kan gadon sarautarsa har zuwa ɗan farin baiwar da take bayan dutsen niƙa, da kuma kowane ɗan farin dabba. 6Babban kuka zai cika dukan ƙasar Masar, wanda ba a taɓa yin irinsa ba, ba kuwa za a ƙara yin irinsa ba. 7Amma ko kare ba zai yi gurnani ga wani daga cikin mutanen Isra'ila ba, ko mutum ko dabba, domin ku san cewa Ubanmu yana bambanta Masar da Isra'ila. 8Dukan waɗannan bayinka za su sauko wurina, su rusuna a gabana, su ce, ‘Ka tafi, kai da dukan mutanen da suke binka.’ Bayan haka zan fita.” Sa'an nan Musa ya bar Fir'auna cikin fushi mai tsanani.
9Ubanmu ya ce wa Musa, “Fir'auna ba zai saurare ka ba, domin al'ajibaina su yawaita a ƙasar Masar.”
10Musa da Haruna suka yi dukan waɗannan al'ajibai a gaban Fir'auna, amma Ubanmu ya taurare zuciyar Fir'auna, bai kuwa yarda yă bar Isra'ilawa su fita daga ƙasarsa ba.