Ubanmu Ya Ceci Isra'ila ta Hannun Shawulu
Nahash ya yi wa Yabesh-gileyad tayin salama a kan farashin kowane idon dama. Shawulu, yana noma sa'ad da labarin ya iso, Ruhu ya sauko masa, ya yanyanka shanunsa don ya kira Isra'ila, ya kuma fatattaki Ammonawa kafin safiya. Ya ƙi ya kashe masu sukarsa: yau Ubanmu ya kawo ceto.
11 1Sai Nahash mutumin Ammon ya hauro ya kafa sansani ya kewaye Yabesh-gileyad. Dukan mutanen Yabesh suka ce wa Nahash, “Ka yi alkawari da mu, mu kuwa bauta maka.”
2Nahash mutumin Ammon ya amsa ya ce, “Zan yi wannan alkawari da ku ne bisa sharaɗin in ƙwaƙule idon dama na kowannenku, in kuma kawo wa dukan Isra'ila kunya.”
3Dattawan Yabesh suka ce masa, “Ka ba mu kwana bakwai mu aiki manzanni ko'ina a yankin Isra'ila. In babu wanda zai cece mu, sai mu miƙa kanmu gare ka.” 4Manzannin suka iso Gibeya ta Shawulu, suka faɗa wa mutane abin da ya faru, sai dukansu suka tā da murya suka yi kuka.
5A daidai wannan lokaci sai ga Shawulu yana dawowa daga gona, yana bin bayan shanunsa. Ya yi tambaya ya ce, “Me ya sami mutane? Me ya sa suke kuka?” Sai suka faɗa masa labarin mutanen Yabesh. 6Da Shawulu ya ji waɗannan kalmomi, sai Ruhun Ubanmu ya sauko masa da ƙarfi, fushinsa kuwa ya ƙuna ƙwarai. 7Ya ɗauki shanu biyu, ya yayyanka su gunduwa-gunduwa, ya aika da su ko'ina a yankin Isra'ila ta hannun manzanni, yana cewa, “Haka za a yi wa shanun duk wanda bai fito ya bi Shawulu da Sama'ila ba.” Sai tsoron Ubanmu ya kama mutane, suka fito kamar mutum ɗaya. 8Ya ƙidaya su a Bezek, suka kai Isra'ilawa dubu ɗari uku, mutanen Yahuda kuwa dubu talatin. 9Suka ce wa manzannin da suka zo, “Ku ce wa mutanen Yabesh-gileyad, ‘Gobe, in rana ta yi zafi, za a cece ku.’” Manzannin suka tafi suka faɗa wa mutanen Yabesh, suka kuwa yi murna. 10Mutanen Yabesh suka ce, “Gobe za mu miƙa kanmu gare ka, ka yi mana duk abin da ka ga dama.” 11Kashegari sai Shawulu ya raba mutane kashi uku. Da sintiri na asuba suka shiga sansani suka karkashe mutanen Ammon har zafin rana ya yi, waɗanda suka tsira kuwa suka watse har ba a bar su biyu tare ba.
An Sabunta Mulki a Gaban Ubanmu
12Mutane suka ce wa Sama'ila, “Su wane ne suka ce, ‘Shawulu zai yi mulki a kanmu?’ Ka ba da waɗannan mutane, mu kashe su.”
13Amma Shawulu ya ce, “Ba za a kashe kowa yau ba, gama yau Ubanmu ya kawo wa Isra'ila ceto.”
14Sama'ila ya ce wa mutane, “Ku zo, mu tafi Gilgal mu sabunta mulki a can.” 15Dukan mutane suka tafi Gilgal suka naɗa Shawulu sarki a can a gaban Ubanmu. A can kuwa suka miƙa hadayun salama a gaban Ubanmu, Shawulu da dukan mutanen Isra'ila kuwa suka yi farin ciki ƙwarai.